25

2K 142 0
                                    

KALLON KITSE PRT (25)

Yaushe ka fara kula da rashina a gidan nan, hala yau ne ka fara..... ."
ya katseta cikin tsawa yace, "ke! Kar ki gayamin maganar banza, inba hakaba zaki gane kurenki, ina tambayarki kina so ki maidani dan iska." nan da nan hankalinta ya tashi, fuskarsa ta koma kamar yadda ta fara ganinsa rana ta farko da suka hadu a shopping mall, sam ba annuri a fuskar sa, yaci gaba da cewa kada ki sake kaimin wannan lokacin baki gida, inba hakaba zaki gane kurenki, inba iskanci ba, yanzu karfe goma saura zaki dawomin gida, har kinada gots din ki rika gaya min magana? Toh kiyi hankali nafada miki."
waje ya nufa, fita yayi ya bar gidan baki daya, ita kuwa baki sake, haka ta tsaya tana kallonsa,
yau meke faruwa ne? Dole ta nemi shanshani, ya za ayi haka ta faru, ta kuma sake tunani, o.k ai dama malam hussaini ya fada mata, mijinta zai kasance mai bala'in kishi, tayi dariya ta karasa daki, nikam nasan bai isa ba, toh amma ai bai taba nuna mata wannan fushinba, ta gani a kwayar idonsa, dam babu wasa.
Tayi tsaki "mts.... Zai gane kurenshi ne, zai dawo ya sameni."
jafar bai dawo ba sai wuraren karfe daya da rabi na dare. Tana zaune a falo, duk hankalinta a tashe yake, ya shigo duk yanayinsa ya canja. Ta tsaya tana harararsa, baima san tanayi ba, ya wuce zai shiga daki, saita shiga gabansa, tayi tsaye, "kai ina zaka haka? Ta fada cike da isa. Ya kalleta daga samanta har kasanta, baice mata komaiba, mamaki ne ta bashi? Oho! Sai kuma ta yatsine fuskarta, tana kallonsa ido cikin ido tace, "warin me nakeji? Kaddai giya ka shawo?." kallonta kawai yakeyi. Can ta dan matso gunsa, tana sunsunarshi, warin giyarce da gaske, harara ta kuma wurga masa, mai cike da tsiwa, "kai bakajin abinda nace ne, ko kai kur...ma..ne."tureta yayi ya shige daki abinsa, ya rufe kofar da karfi, ta nan inda ta fadi, yanzu kam hankalinta ya soma tashi, wai meke faruwa ne? Ta tambayi kanta, karda aikine ya fara lalacewa, toh meya kawo haka? Ta kara tambayar kanta.
Inko hakane, ta shiga uku! Taje ta murda kofar dakin, gam take, yasa key ya rufe, falo ta kwana ranar, dan bataso jamila tasan abunda ke faruwa.
Washe gari bata farka ba sai wajajen goma saura, abun mamaki jafar ya fice daga gidan shida baya barin gida indai bata ce, ya fita ba. Ta iske jamila a kicin, "a'a yadai naganki a falone 'yar uwa?."

wannan shafin ya samu matsala

Ammi ki taimakeni, am in big trouble dan bazan iya rabuwa da jafar ba, har karshen rayuwata!."
magajiya ta riko hanunta, "toh ki kara komawa gun su shanshani mana, kila kuskure aka samu ta wurinsu."
"ammi bazan kara zuwa ba, saboda komai ya lalace, inaso dai ki kaini wani wurin inda za ayi min aiki cikin gaggawa." ajiyar zuciya tayi tace, "wuri biyu na sani, zan kuma kaiki, ki kwantar da hankalinki, za ayi nasara."
"toh jamila fa, ya za ayi da ita?
Sai munje gun malaman su zasu san abunda yafi." ko kalaci batayi ba suka fita.
Boka na farko da suka samu yace musu, jafar kam bazata sameshi yadda ta kesoba, dan yana neman tsari sosai ajikinsa, amma kuma bayada niyar rabuwa da ita, "saidai dolene zakiyi hakurin zama dashi, dan yanzu bayada damuwa daya wuce ta mahaifiyarsa, daya bari kila inya ganta zai iya sauka, amma da duk kika nemi hanashi ganinta, toh ba karamin tashin hankali zaki gani ba, shawarar da zan baki, shine kije gun master na shanshani shi zai iya taimaka miki, kila kiyi nasara.
Na biyun kuwa tayar mata da hankali yayi yace. Jafar bazai kara sauraranta ba, tsanane zai shiga tsakaninsu. Hankalin marliya ya tashi sosai ta rasa inane zata sa kanta. A rayuwarta bata taba tsammanin zata shiga cikin kuncin rayuwa irin wannan lokacin ba, mamaki take yadda da namiji yake nema ya gagareta cukin kankanin lokaci, ta tuna saidai ta tarwatsawa namiji lissafi badai shi yayi da itaba, haka zata juyasu son ranta, tasha wulakanta namiji, ta daburce akan rabuwa da ita, amma gashi yau namiji na neman ya daburce mata. Oh! Ita Allah dama bata hadu da jafar ba.
Ta sami kwana biyu bata cikin nutsuwa sosai, magajiya kuma tana cikin lallashinta a kullum, saita nuna mata ta cire wa ranta son jafar yayi yawa shiyasa take wahala, tasha tunasar da ita cewa, tun farkon haduwarta da jafar take cikin tashin hankali, mezai sa bazata manta dashiba, taci gaba da rayuwarta yadda ta saba a da, tun daga lokacin duk taji ta tsani mahaifiyar tata, dan dai itace silar lalacewar rayuwarta, sannan kuma itace ta koya mata wannan tarbiya ta rashi ganin girman na sama da ita, duk wani abu data ke lallashinta a yanzu ba burgeta yake yiba, don dai ta riga ta bata mata rayuwa.
Ita kanta magajiya ta lura da yanda 'yarta keyi mata wani irin kallo wanda ke fassara mata 'yar na tsananta, dan hakane ta janye.
A ran kwana na uku tana kwance tana tunanin yadda zata shawo kan jafar, sai Allah yasa ta tuna yadda jafar keda biyayya, dan yanada displine ta mike da sauri ta sami magajiya a falo, tareda wani mutum, dama a kullum aikin kenan, daga wannan namiji ya fita

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now