49

2K 164 1
                                    

KALLON KITSE

Uwani taci gaba da cewa, na rasa ya zanyi da matsalar, kullum idanuna na zubar da hawaye." lawisa ta zura mata idanu tana saurarenta, sam bata taba kawowa uwani tanada wani matsala ba.
Kin san Allah lawisa ina cikin damuwa matsananciya...." lawisa ta tsinkata, ki fadamin mana." uwani tace, yau wata takwas kenan da auren uncle akaina! Lawisa ta zare idonta sosai, saidai bata ce komaiba, taci gaba da sauraren uwani, ajiyar zuciya tayi, sannan ta kwashe labari ta fada mata, "dan hakane inkin tuna na fada miki irin matar da yake aure, kuma inaso ki sani yana tare da ita, ai gara ke yusuf ba a gama dashi ba, ina nufin na rabashi da 'yan uwansa, shifa uncle shekararsa hudu baizo gida ba, babu abunda yafi bani tsoro irin abunda akayiwa inna, ita kanta anyi mata asiri, da saura kadan ta haukace.
Lawisa inba dan Allah ya hanaba da sai dai a rasa su duka, sukarta fa taso ta haukata lawisa, toh nifa da aka kira kishiyar ta me zatayi min? Lawisa kam inbanda girgiza kai ba abunda takeyi, tama rasa abunda zata ce mata, sai ajiyar zuciya ta keyi, "babu abunda zatayi miki uwani, tunda Allah ya fito da zaluncinta a fili, na tabbata Allah bazai kyalesu ba, muci gaba da addu'a.
Hakane inji uwani, dan tun lokacin kam daga inna har su Baba ba wanda ya zauna, rokon Allah muka sa agaba, sannan kullum sai ankawo mana rubutu daga sokoto, daga inda ma yafi sokoto nisa ana kawowa, inna kuwa bata sha tare muke sha, nasan inna badan anfi karfinta ba da ba ayi hakan ba.
Sannan ni nasan inna mai kaunata ce, inna bata hadani da kowa ba!
Inda ace uncle na nan a yadda yake da da bazan damuba, amma irin wahalar data sha shike bata tsoro, da har take tausaya min duk da ba fadamin tayi ba, amma nasan abunda ke damunta kenan.
Lawisa nasan iyayen mu baza su taba zaluntar muba, sannan ki tuna Allah ya basu dama su zaba mana miji a auren fari, saboda haka nake baki shawara kije ki basu goyon baya, Allah yana ji kuma baya bacci, yasan biyayyace kika yiwa iyayenka, kuma shi zai saka mik, shine kuma zai kareki.
Ki sani a rayuwar mutum baki dayanta, tuni Allah ya riga daya shirya maka rayuwarka, abunda nake so dake shine kirika addu'a dan nikam nayi imani addu'a jagora ce a rayuwar dan Adam,
inada littafin addu'o'i da mukeyi da inna cikin dare, in mun tashi yin nafilfili, saboda hakane ma kije kiyi, insha Allahu zakiji komai yayi sauki. Sannan inaso mu rike junanmu amana, lawisa nasan na fiki zurfin ciki, toh amma bawai dan ban yarda dake bane, a'a kinsan hamza wankine, ni kuma shi nake so, dan haka nema nake neman hanyar da zanbi uncle ya sauwake min, sannan in fada muku abunda ke faruwa, dan inna ta bani tabbacin in Allah ya yarda zata san yadda zatayi ta raba auren tunda bana so, ita ma bata so." haka dai abokan suka tashi cike da nazarin hirar da sukayi.
Ranar littini rana ce da uwani ta tashi da wani irin ciwon kai, ga zazzabi mai zafi data ke fama dashi, har karfe takwas na safe bata fito ba, inna ta leka dakin data ji tana ta zuba amai.
Nan da nan ta rame, saika ce wadda tayi sati ba lafiya, ga kuma wani irin fari datayi, hankalin inna ya tashi sosai, bata jira wani abu ba ta saka hijabi suka wuce asibiti, har a cikin mota ma ta rinka yunkurin amai, sai dai ba komai acikinta.
Suna isa asibiti inna ta wuce kai tsaye ofishin likita, da yake asibitin take zuwa an saba da ita, matar da ke cikin office din zata fito, ita kuma ta shiga, "doctor! Doctor!
Emergency ne, jikata tana mota aje a taimaka mata. Da saurin gaske likitar ta fito aka shiga da uwani dakin duba marasa lafiya.
Inna meke damunta?
Zazzabi ne tun shekaran jiya nake lura da yanayinta, nasan bata da lafiya, amma yarinyar nan tace, min ita lafiyarta lau, sam bata son zuwa asibiti, balle kuma in za a mata zancen allura." da sauri aka danneta akayi mata allura, duk da bata da lafiya sai da aka danneta, sannan akasa mata ruwa.
Daki aka basu, doctor hadiza tace, idan ta tashi za a debi jininta da fitsarinta. Inna tace toh.
A lokacin hankalin inna ya kwanta, saida tasha ruwa biyu sannan ta samu kanta, ankuma debi jininta da fitsari an ce sai gobe za a kawo result, a wannan rana kadai da ciwon ya kwantar da ita harta zabge, tayi rama. Sai dai da sauki, dan har da dan abinci ta dan ci, duk da ba wani yawa ne dashi ba.
Washe gari kam da sauki sosai, dan tayi karin safe ba laif.
Wajajen goma da rabi doctor hadiza ta shigo, suna hada ido da uwani ta rika dariya, mai tsoro allura an tashi?
Inna tace haka kuwa take, tun fil azal tsoron allura, doctor hadiza ta samu wuri ta zauna suna gaisawa da inna. Bayan nan doctor tace, inna dama tanada aure ne?
Gaban uwani ya buga kamar zai fito, eh tanada aure kam, saidai bata tare da, mijin ma baya nan." ajiyar zuciya tayi, toh sakamakon gwajin fitsari da akayi ya nuna tanada shigar ciki wata daya da 'yan kwanaki." inna ta zare ido, ita kuwa uwani kuka ta saki.

Inna kuwa mamaki ne da tunani duk suka kamata a lokaci daya, ta dubi inda uwanin take, sannan tace ciki...ciki...toh ya akayi? Doctor Hadiza tace, inna aiba abun mamaki bane tunda tana da miji."
da sauri inna tace, hakane, babu mamaki tunda akwai aure."
toh ke mekike wa kuka bacin kiyi farin ciki? Doctor hadiza ta fada cike da zolaya, ko duk kukan farin ciki ne? Tunda kin samu sauki na sallameki, sai dai za a kawo magani da zaki rinka sha." inna tayi godiya domin uwani kuka takeyi sosai, har a cikin mota bata daina ba, dole inna ta sauka daga fushinta ta fara lallashi dan sam bata son kukan uwanin.
Suna isa cikin falo uwani ta fara fadin inna kiyi hakuri, wallahi ba laifi na bane, uncle ne yayi min dole a ranar da zaku dawo daga umrah ki tambayi Baba kiji."
inna ta rungumeta, "ai bance komaiba uwani, fushin da kika ga inayi dan baki fadamin ba, amma ai ba komai." uwani najin ta fadi haka, sai tace, inna kin hakura?
Eh na hakura, kiyi shiru haka nan, kinga ba dadin jikinki kike jiba.
Saita sassauta kukan nata, "toh inna acire cikin mana, tunda kince raba auren zakiyi." tunda ta fara maganar inna ta tsura mata ido, tana kallonta, aranta kuma mamaki ne ya kamata, lallai jikan data ke ta mafarkin samu shine za a zubar tun ba yau ba take so taga jinin jafaru, Allah bai kawo ba shine zata cire wanda ta samu yanzu?
Bazai yuwu ba. Saita tsinci kanta da cema uwani, "karki damu badai har yanzu baki sonsa ba? Da sauri tace " eh inna bana sonsa."
toh ki bari in Allah ya saukeki lafiya, sai yayi sakin." nan da nan uwani ta saki fuskarta, tare da rungume inna tana godiya, tana nuna jin dadinta.
Inna kuwa aranta dadi ne ya kamata mara misaltuwa, batama san inda zata sa kanta ba, "oh Allah na gode maka, ya Allah ka sauketa lafiya, Amin." ta kara tsurawa uwani ido, yarinta ke damun yarinyar nan. A dai-dai nan indo tayi sallama, "hum 'yar shagwaba abun ne ya tashi ko? Tayi tambayar cikin zolaya.
Uwani ta mike zuwa daki, tare da buga kafarta a kasa, irin na shagwaba. Indo ta kalli inna jiki dai da sauki? Ajiyar zuciya tayi kafin tace, "hakane, da sauki, amma indo baki kyauta minba, ashe dan nan naki abunda ya aikata kenan, gashi har ciki ya tabbata..." guda indo ta saki, tana fadin Allah mun gode maka, ashe abun alheri ne ya faru? Kinsan Allah inna wannan auren Alheri ne, Allah ya sauketa lafiya." da sauri inna ta amsa, Amin, amma to baki fadamin rashin lafiyar da uwanin takeyi ba kenan da muka dawo? Haba inna toh ba gashi abun ya nuna ba da kansa, gaskiya jafaru namijin duniya ne, Allah yasa albarka."

***** ***** *******

jafaru kuwa dai har ya samu wata biyar cur a sudan, sannan suka fara shirin dawowa sai da ya samu sati a abuja, sannan ya shigo kaduna. Washe gari tunda safe ya kama hanyar kebbi, karfe sha daya saura ya isa kebbi, da sabuwar motarsa honda accourt V6 2008, baka ce, gashi tayi masa kyau sosai. Yana sanye da wandon kaki, sai 'yar t. Shirt dinsa a jiki, fara sol. Ya dan rame, amma baiyi duhu ba.
Inna na zaune akan kafet din falonta, tana gyran caset din disc dinta, saita ji sallamar jafar, ya shigo cike da nishadi, itama cike da fara'a tace oyoyo auta saukar yaushe? Ya zauna daf da ita, yana cewa, "yau satinmu daya da kwanaki."
aini ban zaci da wuri zaku dawo ba." haka muma, Allah ne ya sauwake abun shiyasa muka dawo tunma watan daya shigene muka so dawowa, America ce ta rikemu, harta na so ta zabe wasu daga cikinmu muje muyi course a war sch. Na can, toh sai dai ni ban samuba, inna ya kwana biyu?
"lafiya lau auta, bari ingani me zan samo maka ne?
Ta tashi ta shiga kicin ta hado masa abinci, anyi sa'a kuwa indo ta gama." sai da yaci yasha, a wannan karon ya tabbatar inna ta sauka sosai, dan ya lura ta fara sakin jik dashi.
Ita kuwa uwani yin jarabawa kawai takeyi, amma ba wani dadin jiknta take jiba, gashi yanzu ma suka fara neco, lawisa ke ce mata, "uwani dakin hakura da rubuta jarabawar nan, har sai kin sami sauki."
a'a gaskiya bazan iyaba, saboda bana so sai wani shekara indawo, nafi so in na tafi na tafi kenan.
Toh Allah ya kara sauki." daya ke sun fito bakin gate ne suna jira azo daukarsu, dayake uwani yanzu motarsu lawisa take bi, da yake mal. Mamman ya tafi ganin gida.
Jafaru ya koshi sosai yaushe rabonsa daya samu irin haka? Ya dawo inna ta kula dashi, har yama manta. Yadan kwanta suna dan hira, "auta inna ta kirashi.
Na'am ya fada tare da kallonta, watakan dan nace ka fita hanyar uwani shne kaki, har kaje kayi mata ciki akan dole ko? Gabansa yayi mummunan faduwa, dan yadda inna ta hade girar sama data kasa.
Sai dai inyi abunda zanyi, amma maganata banza ce agareka ko? Taci gaba da magana ranta duk abace. Da sauri ya dawo kusa da ita, Haba inna ya kamata ki hakura hakanan, wallahi ina son Aisha da zuciya daya, inna zan riketa amana." banyarda ba jafaru, yaudaran mu kake y, ni kuma ban zan yarda ba, dan haka har yanzu ban hakura, inta haihu dole a raba aure nan kaji na fada maka? Tana gama fadan haka ta tashi ta wuce dakinta.

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now