54

2.2K 151 0
                                    

Kallon kitse

a'a da sake gara ayi saurin daukar mataki...." fa'iza ta katse su, ni dai bana so ku fadawa wani, amana ce tsakani na daku, kudai bani shawara yadda zanyi, ina son hamza, so mai yawa, ina sonsa tsakani da Allah, bana son abunda zai bata masa rai.
Lallai kuwa shiyasa kike tare da wahala, tabbas so shike sa mutum ya makance, har ya fada cikin wani yanayin na rashin sanin abunda ya dace dashi, inaso ki sani, nima ina bala'in son uncle, amma idan yayi abunda ba dai-dai ba, nakan nuna masa kuskurensa, kuma dolene yace min, he is sorry, saboda nima ai inyi masa laifi baiyi appologising ba, bazaiji dadi ba, dukkan mu mutane ne, dukkan mu Allah ne ya hallicce mu, kuma shi yasan akwai hakkin mace akan mijinta, akwai kuma hakkin namiji akan matarsa.....kai ko dan da ka haifama yanada nasa hakkin akan iyayensa, abun nufi anan shine yanada kyau idan kina da abunda kike so hamza ya sani game da zamanku, ya kamata kisan yadda zakiyi, ki zauna dashi ku fahimci juna, kin taba gwada hakan?
Ajiyar zuciya tayi a'a ban taba ba."
toh dole ki zama comfuse, dole in kun samu mis-understanding tsakanin ku kufadawa junan ku dalilin da wannan abun ya faru, har kuka yi fada.
Hafsat tace, nayarda da zancenki 'yar uwa, haka muke da isma'il, indai muka samu mis-understanding, bayan mun sauko mukan zauna muyi zancen cikin natsuwa, sai kiga kuma andawo ana hira, tuni mun manta da wannan.
Kingani kuskure ne ace kayi ma mutum laifi ba kace dashi sorry ba, babu dadi kosu mazan da Allah ya daukaka su akanmu, ai sun san in sunyi laifi, ko Allah da mukayi laifi yace, kune mi gafarata zan yafe muku, ko Allah yana son mu nemi tubansa, balle mu mutane da zuciyoyinmu in banda butulci me muka adana.
Jikin fa'iza yayi sanyi, wannan magana haka take, gaskiya kuka fadamun, dan gaskiya ina fama da girman kai, sam! Bana iya bada hakuri, har ma gara shi inya gama fadan yakancemin inyi hakuri idan ya batamini.
Kingani laifinki ne, toh dan Allah ki kula. Haka sukai ta hira har goma da rabi na dare, a can falo suka ji anayiwa jafar tsiya nan da nan uwani tasha jinin jikinta, "shikuma wannan uncle din naku akwai shi da nacin tsiya, jiya da kyar ya bari na kwana gun inna, gashi ko aiki ba a gama ba, ya fara nacin nasa.
Ah munji yana nacin an zautashi me zai hana shi nacin bayan kin gama dashi, don Allah meye sirrin?
Wane sirri kuma?
Jafar yasa baki, su duka suka kalleshi "uncle ina wuni?
Lafiya lau daughters kuna lafiya? Dama kuka rikemin baby ko?
A'a ba ruwan mu, gata nan ku tafi. Ya sami wuri ya zauna, suka ci gaba da hira, "ya akayi banji ance akwai mai karamin ciki acikinku ba?
Haba angaya ma mu irin matarka ce? "uhm haka kika gani daughter, amma kema in fada miki kin kamu, su duka suka zura mata ido, dan Allah uncle da gaske kake?
Ina wasa daku ne? Maza kije ki duba kanki. Hafsat tasa hannu ta rufe fuskarta wai taji kunya.
Ya mike tsaye, "baby taso mu tafi.
Kai uncle dan Allah ka bari har anjima." kinga ni ba ruwana da wayonki, haka kikayi min jiya na kwanta da kewarki, ni gaskiya bazan iyaba, kowa na zaune falo, sai inzo in wuce tare da kai.
Zan kuwa daukeki mu tafi.
Kai uncle." inji fa'iza, zaka iya?
Me zai hana daughter, itace rayuwata fa. Baki daya sukayi dariya, "tashi mu tafi." yanayi fuskarsa ya sauya alamun ba wasa yake yi ba, "toh uncle ka fara tafiya zamu rakota, kaga ta cika jin kunyar su mami na shiyasa."
toh shikenan na bari, amma kuka wuce nan da minti goma zan zo in daukeki ne, yana gama fadar haka ya fita,
yana zaune falonsa ya samu kusan minti ashirin, amma babu alamunsu, ya fito zuwa sashen inna, sai ya tarar dasu suna fitowa. Ajiyar zuciya yayi, "kunyi sa'a  da yau saidai kunyar taki ta wahalar dake. Sukayi dariya suna fadin saida safe uncle. Ita kuwa uwani in banda takaici babu abunda ke damunta, shikuwa ko ajikinshi, jafaru kenan!
Washe garin sallah, tun da safe kuwa uwani ta tashi da ciwon mara, sai dai bata fadawa kowa ba, saima aiki data sa kanta, duk da haka saida inna ta ganota, amma itama bata ce da ita uffan ba, haka ta rika fama duk da bawai ciwon yayi nisa bane, tayi kwalliyarta ta sallah kafin su jafar su dawo daga sallar idi, yana shigowa ya ganta kwance kan kafet, tana rike da mararta, da sauri ya isa gunta, Aisha haihuwar ce? Hawaye kadai ya gani suna fita daga idonta, "anya lokaci yayi kuwa danayi scaning dinki last time ya nuna bayan sallah da sati biyu."
muryar inna yaji daga bayansa, aiko lokaci baiyi ba dole tayi fama da hakan, tunda baka raga mata ba, haba jafar ya kamata ka kyaleta ta haihu, ka cika nacin tsiya, duba min ita ko haihuwarce, in baza ka iya ba inkira baban salma (family doctor dinsu)
zan iya inna, da sauri ya dubata, haka dinne ba haihuwar bace, dan haka ya dauketa zuwa asibiti, dan ayi mata scanning. Doctor sani ya samu da yake sun san juna, tare suka dubata, anyi sa'a ciwon ya sauka, sannan kuma baby lafiya lau, acikin mota in banda ajiyar zuciya babu abunda yakeyi.

suna isa bakin gate sai ga su inna suma zasuje asibitin, ai suna ganinsu inna tayi hamdala ga Allah (S.W.A).
Tun daga ranar uwani ta koma gun inna, ido sosai tasawa jafar, shi din ma ya lura da hakan. Suna zaune a daki shida babyn tasa, ya ke cemata "baby gani nazo inaso ki fadamun duk abinda kike so, saboda zan hada kayan lefe." da sauri ta rufe idonta a ranta kuwa kunya ce ta shigeta, lefe kuma?
Ta tambayi kanta, "kinsan dole ayi lefen baby, gana haihuwa shima dole ne ayi."
nidai duk abunda kayi yayi." murmushi yayi, ya cire hannayenta daga fuskarta, ya tallbo habbarta, "baby i luv u! Tasa idonta kasa, "me too." da sauri ya rungumeta ya soma kissing dinta.
Sallamar inna ya hanashi cigaba, dole ya mike yana sosa kansa, "inna ga paper nan da biro na bawa Aisha ta rubuta abunda take bukata, dan lefe zan hadamata."
toh madallah auta, aiba saita rubuta ba, ka iya kawo abunda kake da niyyar bayarwa, sai muje kano mu sayo mata, tunda su mami na nan."
yauwa haka yayi kuwa, amma inna dakin bari su su tafi, in kin tafi wazai kula da ita?
Hakane basai naje ba suma sun isa." toh kinsan in na koma da sati daya zan wuce kaduna, don haka nake so in wuce gobe idan Allah ya kaimu." toh Allah ya kaimu lafiya, Allah yayi albarka ya kare min kai auta." irin addu'o'in inna kenan a ko da yaushe, bashi kadai ba hatta jikokinta haka take dasu.
Ai kuwa driver jafaru ya turoma su zainab suka wuce kano, ita kuwa inna sai shirye-shiryen tarbar haihuwa takeyi, hatta sabulun salon mai jego ta tanadar dashi, sabulun hadi tayi ga abunda ta hada dashi, sabulun salo takarda biyu, sabulai na wanka kamar dudu osun, dettol, tura, zest, sai na jajirai sabulun pears, saita samu zuma, kwai aloevera, lemun tsami, olive oil, zaitun, saida ta tatse aloevera, lemun tsami, kwai kuma bata saka yolk dinba, sai white na kwain, sannan ta kankare sabulun baki daya, ta cire na jaririn ta saka sabulun pears.
Kwana biyu su salaha sukayi a kano suka dawo, lefe kkam yayi armashi, set din akwati biyu suka saya, sannan set daya na jariri, da inna tayi magana cewa sukai duk abunda ta gani, wallahi jafaru yace ayi, dan musamman akwai wadanda ya turo daga kaduna, "toh Allah ya tabbatar da Alheri, komai an shirya sai haihuwa ake jira. Haka kuma raba kayan akayi kashi biyar, dan jafar yace akaisu duka baki dayan su kar abar ko daya, haka akayi kuwa kowa anbashi kashi daya ya tafi dashi, harda su hafsat dasu fa'iza measurement kawai suka karba.
Uwani kam ta rasa abunda keyi mata dadi, tunani ne, ya fado mata, inda batayi sa'ar uwa irin inna ba, ya zatayi? Kuka ta rinkayi tana yiwa Allah (S.W.A) godiya.
Ita tasan a rayuwa batasan wahala ba, babu abunda zatayi sai  dai addu'a da zatayi, tayi wa su inna.
Bayan sallah da sati biyu uwani ta haifi tsaleliyar yarinya, babu inda tabar jafar, hatta yatsun kafarta da hannunta bata bari ba.
Uwani tayi haihuwa cikin sauki, dan nakuda da haihuwar kwata-kwata bata fi awa daya ba, tsab! Inna ta wankesu an gyara ko ina, sai kamshi ke tashi, aminai da 'yan uwa sai tururuwa suke ana yin barka, tare da gano ma idonsu irin lefe da kayan jariri da aka tanadarwa mai jego, gaskiya abun sai wanda ya gani.
Bayan kwana biyu da haihuwar jafar ya shigo murna daya nunawa uwani har diamond na zobe ya bata. Ranar suna aka sawa baby sunan inna (fatima) zasu kirata zarah, yadda aka tsara sunan kamar aure, domin 'yan decorata aka dauko musamman suka gyara tsakar gidan, wannan aikin aunty salaha ne, tsab! Ta shirya mai jego cikin lace baki da orange (kalar lemun zaki) da yake orange baida yawa akan lace, saita sa ma ta gwaggwaro kalar orange, zoka ga uwani kamar ba haihuwa tayi ba, kace ranar ake bikinta, gashi an cika sosai, shima jafar saida yazo aka dauki hotuna, gaskiya bikin suna yayi kyau, dan bakasan ma haihuwar bace kace bikin aure ne.
Taron dina ya tashi lafiya, kowa yana Allah raya zahra, mai jego taci gaba da wanka, inna tana kula dasu yadda ya kamata. Jafar ya koma kaduna cike da kewar uwani, da kuma 'yar babynsa zahra.
Satinshi uku yazo kebbi, saboda kewar uwani da babynsa, yana tsananin son yarinya. Itako uwani in tana shayar da ita kara sonta take yi, sabo da tsananin kama datake mata da uncle, saida ya shigo gidan uwani tana wanka, domin yanzu da kanta takewa kanta, don inna ta gasa ta yadda ya kamata, zama yayi a inda inna keyiwa baby zahra wanka, bayan sun gaisa tace autana ya hanya?
Yace Alhamdulilah.
Ta nadeta cikin tawul ta miko mishi, ya amsa tare da cewa ina mamanta ne? Inna tace tana wanka." kafin yace wani abu saiga uwani ta fito.
Ya bita da kallo tayi shar abinta, ta kara haske da cika, yasan uwani daban take da sauran matan bariki da ada yake ma kallon kitse, komai na uwani daban ne, ta dubeshi da murmushi uncle sannu da zuwa." yace kema sannu da gida. Sha'awar matarshi ta tsarga mishi jiki, ya dubi inna wadda ta miko hannu tace, bani ita insa mata kaya." ya mikata tare da fadin, "inna sunyi arba'in?
Ta dubeshi da sauri, menene?
Ya shafi fuskarshi, "dama wai saboda mu koma ne, don.....inna

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now