5

3.1K 199 0
                                    

KALLON KITSE PRT>>>>> (5)

bata daina dukan yaran mutane ba, harda cizo takeyi. Mal. Mamman yayi dariya, inna zata daina, yarinta ke damunta, amma kam Aisha akwai ta da fada, shiyasa nake sonta, saboda tsiwanta, ga iya lafazi kamar wata babba, koda yake tana tare da manya dole ta iya, yaci gaba, dama inna wata magana ce ta kawoni, mai muhimmanci, don Allah inna dama.....dama indo ce nake so, amma sam taki amince min, yanzu haka satina uku kenan ban sata a ido ba, nayi da ita ta fadamin dalilinta, amma taki shine nace bara na biyo ta wurinki, kila ta amince. Inna ta gyara zama sosai, ta kara gyarawa uwani kwanciya, dan tuni tayi barci, akafan innar, toh mal. Mamman gaskiya ne, kuma haka yayi kyau, in Allah ya yarda zanyi mata magana, kuma zan nemeka. Allah yasa Alheri a wannan batu, Allah kuma yasa damu za'ayi ameen.
Bayan tafiyarsa inna har daki tabi indo, indo tace ita bawai auren ne bata soba, ita bata so ta bar gidan, inna tace, wannan mai sauki ne, saiku zauna a boys quater, tunda ba kowa anan. Ahaka inna ta kwantar wa da indo hankali, har ta amince da maganan auren mal. Mamman.
Washe gari ta nemi mal. Mamman ta fada masa yadda sukayi, yaji dadi sosai dan dama gida haya yake zama, yanzu ya huta da biya, yayi godiya yace, saita taimaka ta tambayeta yadda takeso ayi, dan gaskiya inaso a daura kafin azumi. Inna tace hakane, yau fa saura kwana goma sha bakwai a fara, dan hka ninasa ranar nanda sati biyu, mal. Mamman ya washe baki yana godiya, inna ta kara da cewa kaje ka duba dakunan, ga makulli, Allah yasa an dace. Ya amsa yana godiya.
Abu anyi shi a saukake, dan haka komai yayi sha'awa, indo ta tare a dakinta, harma inna ta bata kyautan set din kujeru da gado, komai yayi acan-acan.
Jafar ana saura kwana biyu a zumi ya dawo gida, ba wacce ya sawa ido irin uwani, saboda acewarsa ta cika shagwaba, komai tayi, sai ya kusheta, tun da tazo gidan yau watanta kusan bakwai, amma bata daina kazanta ba, makaranta kuwa tana dai nata kokarin amma ba sosai ba, shiyasa yake yawan tsawata mata.
Ita kuwa data lura da hakan, indai tasan yana gida saita gudu can sashen indo, tayi zamanta.
Azumi na saura kwana daya ya kare jibi sallah, salaha da 'ya'yanta suka dira sokoto, dama tuni mal. Mamman yaje ya tarbesu, ana sallar azahar suna shigowa, inna tasa indo ta shirya abinci kala biyu, ga fura kuma da sinasir, don haka yaran sunji dadi kwarai don suna son irin hurar inna. Salaha tace gaskiya inna kinyi dacen yarinya, ta maidake uwa.
Inna tace kinsan dama tun can 'yar shagwaba ce shiyasa, hafsat da uwani da yake suna sa'annan juna, nan da nan suka shaku da junan su, suna wasa.
Washe gari zainab ma ta ison gidan tare da 'ya'yanta baki dayan su, da yake shima mijn ya gina gida musamman saboda insun zo su zauna, shiyasa basu barin kowa. Alokancin ne suka hadu su uku ina nfin uwani, hafsat, da kuma fa'iza, duk da duk sun girmeta amma tafisu baki, ga tsiwa, amma ba karfi. Inda uwani ke sa'an cinzali shine, saboda tsiwarta, dolene ako da yaushe sai su rinka fada da hafsat dan itama ba kyalle bace, har gwara fa'iza dako tsokananta kayi ba ruwanta.
Ranar sallah bayan andawo idi, jafar ya shigo gidan, nan da nan yara sukaje gunsa suna fadin uncle barka da sallah. Saida ya bawa kowa, amma banda uwani, idonta yayi rau-rau zatayi kuka, ya daka mata tsawa, in kikayi min kuka saina gurje bakin nan naki. Salaha tace "haba jafaru ya zaka bawa kowa nasa banda ita, kuma kace kar tayi kuka? Inna tace 'eh ai gara kitayani fadi, in gaya miki auta sam baison diyar nan tawa, zo uwani ki karba, ya shiga ya zauna tare, da fadin salaha don Allah dubi yarinyar nan kazamiyace wallahi, ki duba kiga hafsat da fa'iza anyi musu kitso, sannan kayan jikinsu komai tsab, ita fa? Dubeta kanta babu kitson kwarai sannan ta cire zaninta ta yar, dubi fuskarta ki gani, duk majina ina zan bata barka da sallah?
Inna tace babu ruwanka da ita, haka kawai yarinya karama batada ikon sakewa itada gidansu, kaidai sonkai kake nunawa, toh ta Allah ba takaba, ni wallahi na matsu ka koma makaranta mu huta, tunda kadawo ka ishemu da masifa, ko an gayama bana lura da yadda duk ka takura mata?
Salaha tace. Kaiko jafar ka bawa kanka lafiya, kaima kasan sai a hankali uwani zata daina behaving haka.
"kinsan Allah salaha, wannan yarinyar bazata dainaba, ai kazanta halittace..."
"bari kaga irin yaran nan sunfi kowa kwalliya insuka girma, yarinta ne ke damunta.
Ya mike tsaye yana fadin  toh haka dai kukace , ai muna nan zamu gani.
Lokacin zainab ta shigo, uwani ta ruga aguje tanayi mata oyoyo aunty. Aiko saita fadi kasa, jafar da karfi yace Allah ya kara. Inna da sauri ta mike tunkan salaha takai harta dauko ta, da yake inna jikinta mai iri kyan nan ne, bazaka taba yarda takai hamsin da biyar ba, don kyan jikinta, batada kiba dai-dai take. Wurga wa jafar harara, batace komaiba, amma ta rungume uwani ta lallashi, shikuwa jafar mikewa yayi dan yasan ya batawa inna rai, ya fito waje yaci karo dasu bashir...........

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now