35

1.9K 152 0
                                    

KALLON KITSE

Toh Allah ya bada sa'a, saiki shiga kicin a samo abunda za aci ko? Cikin jakarta ta zaro atamfa tana nunawa inna, inna ya kika ga wannan zanin?."
"iye! Waya baki?
"inna wazai bani? Anko nefa na kawo miki, sai kimin."
"nawaye, wacece zatayi aure?
Balaraba ce, a islamiyarmu take, inna kinsanta tare muka sauke da ita." hala ta wuce ku a boko ne?
A'a ajinta ma uku, makarantarmu daya da ita ai."
"ikon Allah haka zataci gaba ko shikenan?
"nima ban saniba, ko zataci gaba, amma a makarantarmu akwai masu aure."
"Toh Allah nuna mana lokacin, nawa ne?
"dubu daya ne inna ba yawa."
"uhm hakane Allah yaba da ikon biya."
wannan hutun bataje ko nan da can ba, tana tare da inna, sun koma makaranta abun ba a cewa komai, domin a kullum inna burinta ta gyara uwaninta, ita kuwa gimbiyar sai kara kyau take,
ta kara cika sosai, dai ta cika budurwa, dan gashi har suna neman su koma term na karshe, wato promotional exams, kwanakin baya a wannan hutun ne salaha ta aiko musu da kudin jirgi, ita da inna, acan sukayi sati biyu, sannan sukaje gusau da mota, nan abu yafi ma uwani dadi, dan sun hadu da hafsat tace,
"nifa har yanzu kinsan uncle mamaki yake bani, yace wai ke yake so! Uhm ke abun yaba mamaki koni, ni ina zanje da wannan gogaggen dan duniyan. Wallahi ko a kafa aka daura minshi bana so."
kai uwani kinsan fa ya hadu, kowace mace zata so ace mijinta ne, toh ko matan ma bani ba wallahi, bana son shi, ko kadan. Ku kyau kuke hange ba hali ba? Wato shiyasa muke da matsala a wurin fidda gwani."
"hakane wallahi da yawan mu, abunda ke cutar mu kenan, koma ba haka ba wallahi kinga uncle son 'yan mata, in kin shiga dakinsa, in banda wasiku da hotunan 'yan mata babu komai, musamman wata durowa gareshi, na wadannan tarkacen, Allah kiyaye in so namiji irin wannan."
"kai uwani anya ba sharri kike son yiwa uncle ba? Wallahi gaskiya na fadamiki, sau nawa yana sani gyaran dakinsa, ai ba haka kawai zan shirya magana ba, ban fadawa kowa ba kuma saike, dan haka nima nayi mursisi naki ba yadda za ace in cuci kaina, dan inna ma ba so takeyi ba, itama tasan halinsa ne shiyasa."
"uhm kinsan ba wanda zai yadda da wannan labarin akan uncle, dan haka abarta haka karta wuce dakin nan."
nima nasan haka idan ka ganshi kamar bazaiyi ba, Allah dai ya shiryemu baki dayan mu,(ameen)
a yau su uwani sun koma makaranta cike da jindadi, dan sun shiga S.S 3, abun kamar a mafarki suke gani, kowa na yaba yadda uwani tayi kyau, fatar jikinta kamar tarwada, akan tambayeta, wane irin mai take shafawa?
"baseline, amsarta bata wuce hakan, ba komai bane kuwa, illa girma ne ya shigeta gadan-gadan.
Hamza kuwa yanata shirin tafiya service, soyayyar su sai karuwa yakeyi.
Sun sami kamar wata daya da rabi da komawa makaranta, jafar ya shigo gari. Uwani ta shigo gidan, ta iske wata dankareriyar wata mota a tsakar gida, batayi mamaki ba, dan dama ana irin wadannan bakin, da taso taki shiga dan ta gane jafar ne, taji gabanta yana faduwa da sauri, da sauri, tayi ta maza ta shiga falon.
Yana zaune suna hira da inna, tadan dubi inda yake zaune tace, "uncle ina wuni, sannu da zuwa."
ya amsa yana kallonta ta kara girma, dan watannin da ya tafine har ta kara kyau haka. Lallai kuwa dole ne kuwa yasan yanda zaiyi ya auri yarinyar nan, dan gaskiya dashi ta dace.
Nan da nan yaji hirarsa da inna ta fita kansa, zumbur ya mike.
"inna ina zuwa, bari inje in gaida baba yunusa."
toh saika dawo." ta fada itama tana mikewa. Inna ta karasa daki tana yiwa uwani sannu da zuwa, "inna sannu da gida. Ta amsa cike da fara'a
"inna yaushe uncle ya dawo?
Acewarsa yau satinsa uku da dawowa, saida sukayi summiting report. Sannan aka basu iznin tafiya."
gaskiya inna yadan fada, lallai aikin soja sai mai hakuri, ai shi yaji zai iya dan haka yai ta fama."
jafar kuwa ya isa dakinsa yayi wanka, yayi shiri tsab, har ya fito sai ga muzamil kanin jafar ne, amma shikam yayi aure, harda 'ya'yansa biyu, suna ganin juna sukayi musabaha cike da farin ciki ganin juna, dan dama suna dan taba shiri tsakanin su.
"a'a saukar yaushe captain?
Yau din nan officer." suka kwashe da dariya baki dayansu, "sunan daka lakabamin kenan?
"eh, to nima ai captain ka kirani dashi, wuri suka samu suka zauna, suna hira. A lokacin uwani ta fito cike da yanga, dama akwai shi, tayi kyau sosai a idon jafar, ya rasa dalili, bai taba jin abunda yake jiba in har yaga uwani, hakan sai ya manta abunda yakeyi
duk hankalinsa sai ya dawo kanta why? Ta dan rissina tana gaida muzamil, ya amsa yanayi mata saita dawo, ta wuce. Tana tafiya a nutse, sam jafar yama mance akwai mutum a kusa dashi, sai da ya tabashi yace, "dan uwa kana tare dani kuwa? Yayi ajiyar zuciya yace, "kasan mene muzamil? Wallahi yarinyar nan nakeso, amma sam inna taki amince min, wai bata yadda dani ba."
muzamil yana girgiza kansa yace, naji komai jafaru, tun wacan zuwan da kayi baba ya fadamin,

(hahaha su jafar an fada tarko lolz)

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now