27

1.9K 150 0
                                    

KALLON KITSE PRT (27)

Bakin cikine ya taso mata kamar ta bude baki tayi ihu, amma saita hakura dayin hakan.
Tanan inda take har ya fito, wanka yayi, sai a lokacin taga yadda yayi kiba, yayi mata kyau a ido, ta kasa dauke idonta akansa. Shi kuwa yi yayi kamar bai san da mutum a dakin ba, ya saka jallabiyarsa, ya shimfida darduma, ya soma sallah.
Daya idar ma baice da ita komaiba, ya hau gado zai kwanta saitayi saurin isa gunsa zata rikeshi, yayi saurin kaucewa, "kada kira yimin haka, saboda ni ba sa anki bane!
"dan Allah ka fadamin abunda nayi maka doctor, kasan na cancanci insan abunda nayi maka, kasan ni mai baka hakuri ce, doctor inka nayiwa Allah ka fadamin abunda nayi maka, ni matarka ce dole in damu da irin zaman da mukeyi? Yana kwance kan gado ya zuba mata ido, a ransa tunani yake yadda akayi ya auri tsohuwar mace, ko a ido ka kalleta kasan ta kwana biyu, sam babu alamun sassauci a fuskarsa yace, kin gama? Tasa gwiwarta akasa tana wani irin abu na masu ban tausayi, shikam ko kallo bata isheshi ba, itama ta lura da irin tsana da kyamar da yake nuna mata, "kitashi ki fita inaso in huta, bana son yawan surutu. Ya runtse idonsa, marliya jikinta ya gama sanyi, tasan jafar yayi nisa da tsanarta, toh meya kawo wannan sauyi cikin lokaci kankani abu kamar almara? Haka ta fita ta bar dakin gwiwa a sanyi.
Jafaru kam duk lamarinsa ya canja, abinda baya zato shi zaiyi shi a rayuwa, yanzu shi yakeyi saboda, shan barasa, da harkar 'yan mata abun ba a cewa komai, anan mashayarsa yana zaune yana shan abinsa cikin hankali da nishadi, ji yayi ankira sunansa da karfin gaske, "JAFAR!!!." ya dago ido ya kalli inda yaji ankira sunansa, abun mamaki bashir ya gani, cike da zagwadi suka rungume junansu, suna dariya na farin cikin ganin junansu, "aboki" inji bashir, "inkon Allah ashe rai kanga rai a inda baya tsammani? Me kakeyi nan jafar?."
"kai meya kawoka nan garin? Suka kara rungume juna, sannan suka zauna. Jafar ya kira waiter yace a kawo musu kwalbar barasa uku, bashir ya dakatar dashi yace, a'a bana shan barasa, amma za a iya kawomin maltina."
"kaddai ace kabar sha bashir?
"eh na bari, Allah ya taimakeni jafar, kai ya akayi ka fada shanta jafar?
Ajiyar zuciya yayi, "it's long story bashir bazan iya fadamaka yanzu ba, me zai hana gobe mu hadu nan in fada maka?
"a'a nikam daka ganni nan na shigone dan akwai wani oga na daya sauka a cikin motel din yace, nayi magana akai musu barasar can confercuce acan muke meeting, amma da baka ganni nan ba, saidai mu hadu acan inda na sauka hamdala hotel, sai muyi lunch tare da karfe biyu, koya ka gani? Suka tafa "toh Allah ya kaimu." har mota ya raka bashir, bayan ya kaiwa Ogan nasa sako.
Aranar jafar saida ya sha tayi masa yawa, don har saida aka tukashi gida. Marliya ta karasa dashi daki.
Suna isa ya zuba mata amai ajikinta, bayi tayi tana wanke jikinta, ta shiga uku haka rayuwarta zata zama kuma, dama ace farko haka rayuwar ta kasance inyaso daga baya taji dadi.
Washe gari kuwa harda dukanta yayi, wai wane dalili zaisa ta kwana masa daki, baya gargadeta da shigar masa dakiba? Haka tabar dakin tana kuka, tare da magiya, "sakayyar da zakayi min kenan?."
tureta yayi da karfi, har saida ta buge kanta a bango, kwal kake ji, yace, "da yake ba kece sanadin maidani haka ba?." nan da nan kanta ya kumbura, ita kuwa jamila inbanda dariya ba abunda takeyi, da sauri ta isa gun jafar tana lallashinsa, "yi hakuri Oga, zo muje ka karya, don Allah kyaleta."
suka wuce zuwa kitchen, kuka mai karfin gaske marliya ta sake, "lallai ashe haka duniya take? Wata rana in kaine gobe ba kai bane, dubi yadda ake wulakantani," ta fada cikin ranta, cike da takaici, don mene zata tsaya ana wulakanta ta? Ta kara tambayar kanta, dole ta nuna musu tafi karfin wulakanci, koda shiga kitchen kissing ta cimma sunayi, cike da muradin junansu, ai nan wani irin kishi ya taso mata, ta nufesu cike da masifa, abun mamaki, saita kasa ce musu komai, ihu ta rinkayi sai kace mahaukaciya, tuni jamila taji tsoro, amma shi gogan ko kallo ba isheshi ba, saima kara jawo jamila ajiki yake tayi, yana lasarta. Ita kuwa tana zukewa dan munafunci. Marliya ta dauko muciya ta nufosu dashi, jamila ta kwalawa akanta, sai kuwa jini ya barke, zata kara mata sai jafar ya rike hannunta ya fisge mucciyar, ya yar, ya fara galla mata mari, kamar guda hudu, sannan ya tureta ta fadi kasa, kara mikewa tayi, ta nufi jamila ta rike mata wuya, tareda cizonta a kumatunta, jamila sai ihu ta keyi, shikuwa jafaru, yanata kokarin yaga ya raba fada. Da kyar ya kwaci jamila, kanta da kumatunta jini kawai ke zuba, kamar fanfo, marliya dariya takeyi, wai ita a ganinta ta rama wulakancin da kuma takaici da jamila tasa ta aciki, shikuwa jafar police ya kira, cikin minti goma sha biyar da yake basuda nisa suka shigo, suka wuce da ita.
Washe gari inda sukayi alkawari da bashir, nan suka hadu. Saida suka gama cin abinci, sannan jafar yace, "yau kaga yadda na zama bashir, ba komai ya kaini wannan rayuwar ba sai mata dana aura,

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now