15

2K 146 1
                                    

>>>>>>KALLON KITSE PRT (15)

saida ya gansuma ya gano ba 'yan ainihin maiduguri bane, 'yan sadakayalla ne, tunda a maiduguri a kwaisu ai kuwa hashimu yace,  "muyi masa addu'a ba abunda zai sameshi in Allah ya yarda,
yayi ajiyar zuciya anya zamu fadawa fatima wannan labarin?
"a'a karmu fada mata, mu nuna mata komai yayi dai-dai, in muka fada mata tana iya hanawa.
"toh amma in muka boye mata kanmu muka cuta hashimu saboda bamu kyauta mataba, bamu kuma kyautawa jafar din ba.......jafar ne yayi sallama ya nemi wuri ya ajiye musu abincin karin daya siyo musu, ya sami wuri ya zauna, sannan ya gaidasu, kawu yace, "jafaru anya wannan aure da kake nema zaiyi tasiri a rayuwarka?.
Gaban jafar ya fadi, ya dago kansa, yace, baba meka gani ne?
"gani nayi wannan gidan ba gidan mutunci bane, kobaka lura bane?
Baba yunusa yayi saurin amsar maganan, kar kaje son zuciya ya saka cikin halaka, dan nan idan fatima taji bazata yarda ayi wannan auren ba.
Ai kuwa jafar kuka ya saka musu wiwi, saikace karamin yaro.
Nan da nan kuma hankalinsu ya tashi, ya rinka fadin don Allah baba kar ku fadamata, inason marliya, wallahi aka fasayi da ita, toh bazanyi aure ba, har in mutu.
Sunajin haka sukace bazamu fadaba jafaru, tunda ai kai zaka zauna da abarka, ba damuba, zamu baka hadin kai, yi hakuri kabar kukan hakanan. Jafar ya share kwallah yana godiya.
Da yake jirgi suka shiga nan da nan suka isa kebbi, sun kaiwa haj. Fatima labarin komai, amma banda lala cewar wurin, tayi farin ciki sosai, don ko ba komai ta matsu dan nata yayi aure, hatta kudin sadaki basu fada mata ainihin abinda aka biya, dubu dari sukace, amma duk da haka saida ta jinjina wannan kudin.
Bayan jafar ya bar airport gun lawal ya wuce, yana fada masa ansa ranar bikinsu da marliya, lawal akoda yaushe abun na daure masa kai, ya danyi ajiyar zuciya dama jafar kana nan kan bakanka, saika auri yarinyar nan, bayan nabaka labarinsu da ita da 'yan uwanta? Why? Meyasa zaka auri tsohuwa a tsofaffin ma kucaka? Don Allah ka......"
"indai haka zaka rinka yimin, duk in an zomaka da maganar marliya, toh wallahi zan daina zuwa, kuma wallahi zan iya rabuwa da duk wanda yace zai rabamu.
Lawal yace, meya dameni? Allah ya baka hakuri, ni inta nine ka hada guda dari irin su meya dameni? Nidai na fadamaka gaskiya ne, tsakanina dakai na abokan juna, amma tunda baka ganeba its o.k. Ai bani zan zauna da itaba, she is all yours, Allah ya ganar dakai.
Idanun jafar sukai jajir yama rasa me zai cewa lawal, amma ba yadda zaiyi, dole ya hakura da duk wulakancin dazaiyi masa, saboda anan kam shi kadai ne abokin shawararsa dan bai yadda da kowa ba, kamar yadda ya yadda da lawal, dan haka sai ya maida abun wasa yace, "dama ni zan zauna da abita, dan haka kai dan kallo ne, ba ruwanka, inaso muje dakai gun marliya a matsayin babban aboki, dan ashirya komai, ka gane ko? Amma bance kaje kata yaba maganaba, kamar ranar farko da nayi introducing dinka, don ranar kaban haushi.
"nasani ai , well its your life, dan haka zanyi abunda ya kamata.
"thank you my friend zamuje gobe da daddare zan zo in daukeka.
Kudi yaba marliya ta fara sayayyan kayan aure, shi kuwa wani yaronsa emmer yaba kudi yaje kano ya siyo masa atamfofi, shima din ya shiga shaguna duk abunda ya burgeshi saiya saya, akalla saida suka sai kaya set dari, banda gyale da under wears, abun nayi ne, dan dai jafar ya kashe kudi ba kadan ba, inka ganshi ya zama abun tausayi, duk ya rame, yayi fari dan dama shi fari ne, troly ce manya-manya guda biyar, duk an cikasu da kaya, sai masu binsu guda hudu, sai kanana guda uku da kit. A dakinsa ya ajiye akwatinan, ana saura sati daya daurin aure, zainab da salaha, da matan Alh. Yunusa su biyu da wasu kannan mahaifinsa goggoninsa su uku, ta wurin inna kuwa su shida suka hadu, saura sai ana saura kwana biyu daurin aure zasuje da mota, amma wadannan da jirgi zasuje.
Da karfe dayan rana suka isa, mota biyu suka shiga shida lawal daya jeep ce ta daukesu, kai tsaye gidan jafar suka nufa, da yake gidan ba laifi yanada girma, four bed room ne da makeken falo, anacin abinci ya shigo suka kara gaisawa, ya kira emmer yace yaje ya dauko akwatina su duba, in akwai abunda za a kara, sai a kara.
Da emmer ya soma fito da akwatina kallon juna suka farayi, dan abun ya basu tsoro, abu kamar hauka, akwati goma sha hudu. Inji zainab ta fadawa salaha a kunne.
Salaha kuwa sai girgiza kai take, tama kasa magana, sai ajiyar zuciya, da kyar emmer ke daukosu, duk da yadda yake jin karfi. Daya gama salaha da goggo mairo suka soma budewa, ya mike yace ina zuwa, bari inje in dawo kafin ku gama."
"toh kai ba anan bane za a kawo amarya munzo mun tare?
"a'a ai insha Allahu next month zan gama course dina, in koma kaduna, dan haka sukace gara abar jere sai an koma kaduna, sai ayi.
Tace "toh aina zata zauna yanzu?.
Ya nuna dakinsa, a wancan dakin zata zauna, akwai gidan abokina daya aramin da yake shima iyalansa na kaduna, acan zansa sauran baki.
Toh Allah yasa ayi lafiya.
Tunda suka bude kaya suke mamaki,

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now