18

1.9K 139 0
                                    

KALLON KITSE PRT (18)

Tana tsakiyar gado night gount ce ajikinta, duk ilahirin jikinta awaje, dataji shigowarsa saita mike zaune, tana murmushi. Shima murmushin yakeyi, ya isa gunta, ya zauna, "amarya kinsha kamshi, ya ya hidima? Ta wangale baki tana murmushi. Wani dadi yaji ya buge hancinsa, baisan komeye bane, bai kuma ya isa ya tamaya ba, dan yana tsoro kada a hanashi abunda yayi niyya. Ya shafa gefen fuskarta, "zo muje muyi alwala, muyi sallah, ko kinyi isha?
Kwanciya tayi tana shagwaba. Shikam ya mike ya shiga toilet yayi wanka tareda alwalla yazo yayi sallah, sannan yafita ya dauko leda, kaji ne aciki da madara mai sanyi, ya dauko plate ya juye. Ai tana ganin kaza ta mike zaune, ta dawo kasa, yace dama bakiyi barci ba?. Ta rangada ido, tace ina naga barci wannan yunwa da nakeji? suka ci, suka sha, sai da sukayi dam, sun hau gado, a yau yayi mamakin marliya yanda ta kauda kunya baki daya ta rinka nuna masa soyayya, abunda yafi bashi mamaki shine, yadda zata juya da namiji wurin kwanciya, indai dadi ne yaji kam, dan ya sami abunda yake nema, amma bashine da namiji na farko daya kasance da ita ba, har aka kira sallar asuba idonsa biyu, abun ya daure masa kai ya rasa abunda yakeyi masa dadi, yanzu dama marliya ba virging bace taketa nuke-nuke sai kace ta kirki?
Dayaje masallaci ya dawo ya isketa sai bacci takeyi, ya tunama jiya bata bari sukayi nafila ba suka kwanta, yadan janye zanin data rufa da shi, ta dube shi cike da takaici tace, "nifa ba a tadani daga barci, sai in ni na tashi da kaina!.
Abunda ya bashi mamaki kenan, baice mata komaiba, sai ya tsinci kansa dace mata Allah baki hakuri, dama na cene kitashi kiyi sallah.
Tace haba jafar bayan wahalar dani dakayi jiya? Takaici ne ya kara kamashi, ya bata wahala kodai ta bashi wahala? A fuskar sa sam bai nuna mata ranshi ya baciba, saima ya sami wuri ya zauna yace "haba dan Allah kiyi hakuri, ki tashi kiyi sallah mana, bakisan wasa da sallah ba kyau ba? Ta ware ido sosai tace, bazan iyayi yanzu ba, sai anjima.
Tashi yayi yana murmushi, "Allah yabawa gimbiya hakuri asha bacci lafiya.
Yasa kai ya fita kitchen ya shiga, ya hada tea mai kauri yana sha.
Daya gama sai ya dawo ya kwanta, abun mamaki ta shiga yi mishi susar kadangare, can ta shiga tube kaya, me zaiyi? Shima saiya fara maida martani. Wajajen karfe biyu saura, suka tashi shima kofa sukaji ana kwankwasa musu, da sauri ya mike ya shiga bandaki yayi wanka ya saka wata blue sky shadda, yayi kyau a idonta, ta rinka sumbatarsa, shikam abun yana bashi mamaki, ya akayi marliya ta iya irin wannan soyayyar? Ya fita ya bude kofar, su uwani ce da hafsat, ya hararesu, "ku haka akeyi, kuyi ta buga ma mutane kofa da karfi, zaku karya kofar ne?
Hafsat tace, "dama inna ce tace mu kawo abinci, yanzu zuwanmu na uku kenan, munzo tun safe baku bude ba.
Ya dubi uwani ke bakisan halina bane? Da ai saiki gaya mata, ba a buga kofa, ku aje abincin ku tafi, ba shikenan ba?
Daga can bayansu suka tsinkayi muryar marliya tana cewa, " toh ai saika bari su shigo ciki ko?.
Ya basu hanya suka shiga, idon marliya akan uwani ta tsaya tace, "wannan kanwarka ce ko?.
Yadan dubeta kasa-kasa, "eh hakane ya akayi kika san haka?
"kuna kama."
"wace kama?.
"yanayi da juna kukeyi." yayi murmushi, "wancan itace hafsat 'yata ce, ita ce 'yar yaya zainab, ta biyun kin gane yaya zainab?
O.k na ganeta, nikam dan Allah dauko plate ka dibar mana abinci, dama yunwa nakeji." da sauri ya shiga kitchen ya hada musu abinci, dankali da miya ne da kwai sai kayan tea.
Sun sami kamar sati biyu a kebbi shima suka takure don ta nuna masa ita bata son zaman wannan garin, yace da ita aiba nan zasu zaunaba, hutunsa kawai yake jira, tunda dama kaduna zai koma da zama. Da kyar sukayi sati uku, kamar ance gobe zasu wuce warri, da daddare sukaje yiwa inna bankwana, tunda sukaje yau ta fito, wai ita rana takeji, garin ya cika rana.
Ita kuma inna bata fasa sa abinci akai ba, koba komai tasan jafar na bukata.
Suna zaune bamai cewa komai, sai shi jafar din da yake ta shagwabarsa, ita kuwa gimbiyar ta juya musu baya, tana taunar cingam, tana kallon t.v, duk ta tsargu, har dai yadda ta gani a idon inna sam bata ra ayinta, a ranta tace, "nafiki iko da shi dai, kuma wannan zai zama na karshe keda ganin danki. Tayi murmushin mugunta.
Uwani ta kawo mata ruwa, tun kafin ta ajiye tace, "nifa bazan sha ruwa ba, ke maida.
Hatta jafar saida abin ya masa zafi, shidai baya ganin laifinta.
Daya lura zaman ba dadi, sai yace inna, zasu wuce.
Zumbur ta mike tana gun-guni, dama ta matsu su tafi, sai yayi kamar baiji ba, suka kama hanya suka fita.
Inna ajiyar zuciya tayi tace, "Allah wadarn naka ya lalace." uwani ta shigo tace, "inna ke kadai kike magana?".
"uhm ni kadai kuwa, waccan 'yar barikin na kewa addu'a, Allah ya shiryeta." uwani tace metayi makine?
"bazaki ganeba uwani, ke yarinya ce, Allah ya shiryeta, ya shiryamin ku baki dayanku amin",
yau watansu uku da komawa kaduna, har an kara masa girma, ya kai matsayin captain, duk yadda kaga jafar naji da kansa,

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now