10

2.3K 152 0
                                    

>>>>KALLON KITSE PRT (10)

Toh na amince Allah yasa ayi a sa'a.
"Amin, su duka suka amsa, sai a lokancin jafar ya saki fuskarsa don yaga inna sai hira takeyi dasu.
Anan sukai isha'i, dan har saida sukaci abincin dare, sannan baba yunusa yace, jafar yakai shi gida, tare suka fita da Alh. Hashimu, da yake dama ya daba sauka can gidan baba yunusa. Sai wajajen goma da minti sha biyar ya shigo gidan, ya isketa har daki, ya sami wuri ya zauna, inna na gode.
Ya fada kansa a kasa, ta wurga masa harara, "da akayi me? Ya saki murmushinsa na zolaya, "da amincewarki inna,
"toh bari in fada maka, da duk yarinyar nan ta shigo bata kwantar min da hankali ba, dole ka sake aure.
Yace "eh na yarda inna, yarinya ce 'yar babban gida, zakiyi mamaki inna, bazata bayar daniba. Ta zumburu baki nidai na fada maka, da duk takini nima zan nemi mai kaunata.
Dariya yayi sosai, "inna zan baki mamaki.
"toh Allah yasa.
Amin. Ya amsa. Nan fa suka ci gaba da hirar da tunda ya shigo garin a wannan lokaci nai samuba.
Ranar lahadi ya koma warri, a ranar ya wuce gurin marliya, yana isa ya danna mata kira, baifi minti biyu ba sai gata, sai fara'a takeyi, ta shiga cikin mota data dauki sanyi, ga sauti yana fita a hankali gwanin dadi, ya dube ta sosai yace "i miss you baby". Ta sunkuyar da kanta kasa, tace ina wuni? Yadan yar da hanunsa yace nifa kunyar nan taki tayi yawa my marliya, inaso ki sake dani, dan naje nayi magana aje nema min aurenki, kinga kuwa na kusa zama "yours" koba hakaba?
Farin ciki ya bayyana a fuskarta, tana yiwa Allah godiya, cikin ranta ta karasa kanta a kasa, "haba my love ki nunamin farin cikin ki mana.
"you are very special to me". Ta nemi rufe fuskarta, ya rike hanunta da sauri, "a'ah don Allah kar kyi min haka, inaso inga beutiful face dinki.
Ta fisge hanunta tana kokarin fita daga motar, yayi saurin bada hakuri, "don Allah kiyi hakuri na daina.
Ta dube shi, tace nasha gaya maka bana son hakanan, ance fa duk inda mace da namiji suka kasance su biyu toh na ukun su shaidanne,
don haka nakeso ka rinka hakuri da irin wannan abun.
Ya kara jin dadi a zuciyarsa, dan dai yasan yayi sa'ar mata kamila, yasan zai dace da matar kwarai, wanda take kare mutuncinta, dan haka yasan in sunyi aure zata kare masa mutuncinsa, Allah ya nuna masa. (Amin). Ya fada a fili. Ta dube shi tace, da mene?
"sirrina ne marliya".
"toh ai sirrinka nima nawa ne"
"hakane, in lokaci yayi zaki sani.
Haka sukai hira na masoya, masu ji da junansu, da kuma son junansu.
**** **** **** ****
MARLIYA YA'U
'yar asalin maiduguri ce karkida, don haka talaici ne ya dawo dasu zama a portcourt, anan warri mahifinsu ya rasu, tuni ba yanzu ba, suna zaune ne da mahaifiyarsu magajiya aka fi saninta anan warri, ba wanda baisan halinta ba, gogagiyar 'yar duniya ce, hakama 'ya'yanta ta koya musu, da yake Allah ya azurtasu da kyau, sunyi kyan dan maciji, don ba abunda sukasa ma ransu in banda son duniya. Marliya itace ta hudu gun mahaifiyarta, itace kuma ta gadota sak! Halinsu daya da mahaifiyarta, malamai da bokaye ba inda bata lekawa, tunda mahaifiyarta ce ta koya mata, tunda tasan tafita iya duniyancin.
Ta soma ganin jafar ne ranar daya biya wani babban shoping mall. Suna daga cikin motar wata abokiyarta, shikuma ya fito daga cikin tasa motar, duk da haduwar motarsa (jeep), ita kam mai motar yafi burgeta, dan dama su mota itace take ganar dasu wane irin mutum ne kai, a rayuwarta bata taba son da namiji ba sai yau, tun da take arayuwarta bata taba zaton zatayi aure ba, ballantana tayi soyayyar gaskiya. Tasha jan ra'ayin maza batama san iyakarsu ba, akan zata aure su, saita gama yagar rabonta, saita yadda dasu, amma nayau ba haka bane, da sauri ta fita daga motar taje ta duba number motar ta rubuta a wayarta, tayi saving.
Jamila abokiyarta tace, "wai ya naji kinyi shiru na marly? (yadda suke kiranta kenan), mu wuce ne? Tace, a'ah jamila dan Allah kiyi hakuri akwai wanda ya shiga wurin nan inaso in dan kara kallonsa.
"kinga bachelor din kuwa ya hadu da yawa.
Jamila tace, ya akayi kika san bachalor ne?
"haka kawai naji ajikina baida aure".
Ko yanada aure jamila zan nemeshi, in aure shi kota halin kaka ne.
Jamila ta zaro ido waje, "aure marly baby?
Haba dai kin manta da "oath" din mune akan bazamu taba aure ba a rayuwar mu?.
Marliya ta dubi jamila na kusan minti uku, "anya bazan karya wannan rantsuwa ba jamila? I thing am in love".
Jamila mamaki ya kamata sosai itama sai taji tana so taga wannan bawan Allah, da yayi saurin tafiya da zuciyar marliya, dan ita tasan ba tun yau ba sun sha garzayawa da maza masu kyau ga kudi ba juyin da basuyi haka bai taba faruwa ba, sai yau.
Adai-dai lokacin......

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now