9

2.3K 159 1
                                    

KALLON KITSE PRT  (9)

saboda zafi ga tsoro ya kara tureta, maza barmin dakina,.
Ta fice a guje tana kuka, sai dakin inna, ta fada jikinta, "inna ni bazan sake kaiwa yaya jafar abinci ba, kullum naje saiya dakeni, yau ma rankwashina yayi, bakiji ba kamar kaina zai cire, yanzu haka kaina ciwo yake min.
"yi hakuri zai zo ya sameni ai".
A'a inna don Allah ki kyale shi, wallahi zai karamin wanda yafi wannan, nidai bazan sake kai masa abinci ba.
"toh shikenan je kidauki maganin ciwon kai kisha.
"a'a inna ai naji sauki.
Dama nasani bazaki shaba.
"yauwa dan Allah inna kibari naje gusau mana, kinsan fa kinyi alkawari. Inna ta zuba mata ido. Anya uwani zan iya bari kitafi ki bari dai auren mansura sai muje, tunda lokacin kina hutu
toh shikenan Allah ya nuna mana.
A lokacin jafar ya shigo tsab uwani ta mike ta wuce dakinsu, ya dubi inna wacce ta hada girar sama data kasa, ba alamun wasa a fuskarta, daga sama yaji tana fadin, me uwani tayi ma ka doketa?.
"ni inna? Ta banka mishi harara wanda ke nuna wai wasa nakeyi dakai? Sai yasha jinin jikinsa kansa akasa yace inna ayi hakuri, ai ita taja.
"kar kasake dukanta akai, kanaji nako? Haka kawai cin zali, kasan inka sake saina rama mata wallahi,
kansa akasa dai yace inna ayi hakuri, baza a sakeba.
Tace ni nafada maka ban amince da neman auren nan nakaba, in kuwa kaki toh sai kaje kayi tayi, amma nikam ba ruwana, kuma bazansa albarka ba, don haka kaje kayi tunani. Tashi tayi ta wuce daki.
Shi kuwa idonsa sunyi jajir, kaman garwashi ahaka indo ta shigo, ta same shi, ta gaishe shi acika ya amsa dan batama ji abunda ya fadaba, ya mike ya fita fuuu. Kamar iska. Indo daki ta karasa, ta iske uwani kwance akan cinyar inna suna hira.
"uhm uwani ta inna, zanso inga ranar rabuwanku, lallai ba karamin aiki bane.
Inna tayi dariya, ai nima ina wannan tunanin, ke dai indo uwani tace, kai inna kema kina biyewa babba ( indo kenan, haka take ce mata), nifa ba wanda zai rabamu saidai mutuwa ko inna?
Eh hakane uwani kedai kyale indo.
Toh shikenan Allah ya nuna mana, nikam nasan akwai ranar rabuwa, inna miya samu jafar ne, yadda na ganshi gaskiya akwai abunda ke damunsa.
"ke rabu dashi wai aure zaiyi, amma shine zaije can ya dauko mana 'yar maiduguri shuwa arab, nikam gaskiya ba dani za ayi wannan abunba,, na taba gani ba labari aka ban ba, akwai wani abokin mahaifinsu daya auro su, duk arzikinsa suka kwashe, shine shi kuma zai dauko min ya kawo, toh badaniba.
"inna ki barshi yayi, kinsan fa ya dade baiyi auren nan ba, kar aje yakiyi kuma.
Saida ya fasa indo amma badai wannan yarinyar ba, kinsan tunda ya fadamin zancen auren wallahi hankalina bai kwanta ba.
Toh inna kiyi addu'a Allah yayi mai yiwuwa.
"inayi indo, saidai gaskiya ba wannan yariyar ba.
Jafar kam fitansa gidan kawunsa kanin mahaifinsu Alhj. Yunusa halidu ya samu, yayi sa'a kadai ne a falonsa, ya zauna suna gaisawa, jafaru yaushe a garin?
Tun jiya baba, ai jiya da yamma na shigo akace min kaje bunza.
"andawo lafiya? Ya bukata.
"lafiya lau ya bashi amsa.
"ya hanya kaima da aiki? Yace "lafiya lau, kawu addu'arku muke so ako da yaushe.
"ana nan anayi jafaru, ya zancen auren ka? Ya kamata ka ajiye iyali haka nan jafaru.
Ya sosa keyarsa, hakane baba, wallahi maganar ita tasa nazo, amma inna taki bani hadin kai, dan Allah baba kasa baki ta amince nasan in bata amince ba, auren nan bazaiyi tasiri a gunaba.
Yace ka kwantar da hankalinka zamje in sameta, 'yar inace yariyar? Ya amsa masa 'yar maiduguri ce, amma a warri suke zaune.
"ba komai, ita kake so?
Eh, baba indai inna ta amince, sun mace in tura aje neman aurenta.
"toh shikenan yaushe zaka koma?
Inasa ranan lahadi, yau saura kwana hudu,
bakomai insha Allahu za a shawo kanta, amma inaso kaje ka fadawa kanin nan nata na sokoto, kasan tana shawara dashi,
yace toh zanje gobe nagode baba.
Nan suka ci gaba da hirar su, bai bar gidan ba sai karfe goma da rabi, koda ya shiga cikin gidan inna ta rufe kofarta. Yasan danshi akayi saurin kulle kofar.
Washe gari gaisuwa kawai yakai. Ya wuce sokoto. Da azahar sai gasu kebbi dama shima kawun nasa ya matsu yaga yayi auren, sai bayan la'asar suka isa gun inna. Tana ganinsu tasan maganar daya kawosu, don haka suna gaisawa Alh. Yunusa yace "fatima nasan kisan dalilin zuwan mu? Munzo ne mu nemi alfarma gareki, kiyi hakuri ki bari ya auri wacce yakeso, yaran yanzu ba a yi musu dole don haka nake cewa ki sassauta masa, don son Annabi.
Hashimu yace "yaya kindai san jafaru ba yaro bane, dazaije ya dauko abunda zai cuta masa,
tace nidai gani nayi duk matan da sukenan basuyi masa ba, har sai yaje can maiduguri ya dauko?
"fatima ba inda aure baikai mutum, so nawa anayi, sai kiga wanima daga nan yaje kasar sin (china) yayi aurensa, duk abunda Allah yayi yinsa shine dai-dai, kedai kisa albarka ki kuma yi masa addu'a.
"toh ai shikenan me zance? Yaje yayi tayi nikam ba ruwana, amma Allah yasa albarka.
"haba yaya ya zakive ba ruwanki, baki amince ba kenan don Allah kidaina haka, yaya hakuri fa muka zo baki.
"toh na amince Allah yasa ayi a sa'a.

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now