26

1.9K 150 0
                                    

KALLON KITSE PRT (26)

daga wannan namiji ya fita sai wanan ya shigo, ta zauna gab da ita, tace "inaso muyi magana ammi." ta dubata sosai cike da kula tace inajinki.
"toh ki sallameshi kana, ko muje dakina." muje dakin ko zaifi,"
inaso ki shirya muje office din su jafar ki bashi hakuri, inaso in koma gidana Ammi, na gaji da zaman gidan nan." sai a ranar magajiya ta tausayawa rayuwar 'yarta, dan ta gano tana tare da kaunar jafar, ba kadan ba, dan haka ba musu ta dauki gyale, "wane shiri zanyi? Tayi murmushi nagode Ammi
hakuri ta bawa mutumin data ke tare dashi dazun tace, zasu iya haduwa anjima.
Jafar na tare da patient koda suka isa secreatry dinsa da sauri ta isar masa da sakon matarsa na waje, tana son ganinsa. Tsaki yayi yace, tace mata ta jirashi har saiya gama ganin marasa lafiya tukunna, ta fada mata, Ammi tace "kifada masa ba ita kadai bace, tare da mahaifiyarta ne." yace su isa, da suka shiga yana tsaye da uniform dinsa, da farin coat wanda doctors ke sawa, da suka shigo suka nemi wuri suka zauna,
yadda fuskarsa babu annuri yasa ta kara rudewa, kuma yayi mata kyau yakara kwarjini a idonta,. Bayan sun gaisa Ammi ta soma bashi hakuri, da hannunsa ya dakatar da ita, "Ammi ba komai na hakura.
"toh kasan ya kamata ta koma gidanta ko?
"eh hakane tana iya ta koma, yadda Ammi taga sun sami shiga yasa ta gyara zama tace, "toh ya batun jamila, kasan dai baka kyauta bako jafaru, in kai ne akayiwa haka ai..... ," ya katseta, "Ammi kin fadi abu mai muhimmanci na amince, bana so ta so da abunda ya wuce.
Da sauri marliya ta mike ta riko hannun Ammi suka fita, yabi bayansu da kallo, yana neman kariya daga sharrinsu, bayada matsala yanzu inbanda yaje ya nemi gafarar mahaifiyarsa, koda yake ya tura takardar neman hutu, dan dama yakai shekaru uku bai dauki hutu ba.
A ranar ta tattara yanata-yanata ta koma gidan mijinta, abun mamaki ta iske jamila a gidan abun na daurewa marliya kai, wai me jamila take nufi ne? Tatambayi kanta, ta karasa ciki, jamila na kwance kan kujera tana cin cingam, sanye da wani guntun wando sai 'yar farar vest ajikinta, tayi saurin zama tna yiwa marliya kallon ke banza ce, anan gidan, bata yadda da hakan ba, saida taji wayarta na ringing, da sauri ta dauka, saboda jafaru ne, yace da ita, jamila na gidan ba ruwanki da ita, don ba zamanki takeyi ba, ki sani inada ikon ajiye abunda naga dama agidan tunda gidana ne, inkinga zaki iya zama to, in kuma bazaki iya ba saiki juya ki koma gidan uban naki, saina shigo."
kwalla ne ya cika a idonta, kamar zasu zubo sai tayi ta maza ta hadiye su, jamila ta rinka dariya kamar taji abunda ake cewa acikin wayar. Tana fadin, "yaya dai marliya baby, kin sauko ne, ko kuwa har yanzu kina kan bakanki, nasai kin kasheni? Kiyi hakuri muyi zaman hakuri, ki yagi naki rabon nima inyagi nawa, tunda abun business ya zama."
batace komaiba taja jikinta zuwa dakin barcinsu, taji shi a rufe, jamila ta kara kwashewa da dariya, har tana faduwa, "dakin Oga(jafar haka take kiransa) zaki shiga? Dakin gane kurenki, kinyi sa'a na rufe dakin da yau sai kinyi dana sanin shiga masa daki, ta nuna dayan dakin dake kusa dana baki, "kina iya kiyi amfani da wannan, in kinaso." marliya tace,
"jamila kinsan duk wulakancinki nafiki iyawa ko? Dan haka kibi a hankali,
A da kenan marly, yanzu kam nima na isa yanka, nayiwa kaina alkawari nima saina rama wulakancin da kikamin marly, bazan taba mantaki ba a rayuwa, kece sanadin lalacewar rayuwata, ke kika maidani haka, nazama abun nuni a 'yan uwana, inada yayye uku mata da maza biyu, duk sunyi aure bandani." kuka ta saki mai tsumar da rai, ko kai kaji irin kukan da jamila keyi, saika tausaya mata.
Nan da nan jikin marliya yayi sanyi, tasan tabbas itace sanadin  da jamila ta zama abunda ta zama, dan cutarwa tasan ta cuta mata, toh amma meyasa zata nemi shiga rayuwarta da mijnta? Batasan tana iya komai akan wanda keson rabata da jafaru ba? Jamila ta katse mata tunani," wulakanci yanzu na fara yi maki marliya." tayi wuce tayi shigewarta dakin data ke zama aciki, bakin ciki kam marliya tayi shi, kuma tun ba yau ba, abun yafi na kullum, tasan tanada hannu a lalacewar jamila, ita taso hakan tunda ita ta nemeta, "zan gwada mata ita karamar 'yar iska ce, sai nayi sanadinta, mu zuba nida ita mugani." A nan falo ta zauna tana jiran shigowar jafar.
Bai shigo gidan ba sai kusan sha biyu da rabi, abun ya daurewa marliya kai, lallai ba karamin juriya zatayi ba dan yadda take zaton al'amarin ya wuce haka,
a yau ma haka ya shigo gidan a buge, ta mike tsaye tana fadin sannu da zuwa." ko kallonta baiyi ba, ya wuce dakinsa, tayi saurin bin bayansa. Saida ta shiga dakin sosai yace, "ke me kike nufi? Anan zaki kwana kome? Ta tsaya tana kallonsa galala, baki sake, toh ina zanje? Ko ka manta ni matarka ce?
"ban manta ba amma inason privacy from now on, saboda haka kije ki zabi daki ki zauna, duk lokacin danake bukatarki zan nemeki."
yana gama fadin haka ya shige bayi. Ita kuma tayi tsaye tana kallon kofar bayin,

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now