52

2.6K 155 0
                                    

Kallon kitse

dubi dan gyalen da kika dauko saika ce budurwa, kefa yanzu matar aure ce.
Kayi hakuri bazan sakeba."
da gaske kike?
Uhm."
toh shikenan, na hakura, amma yanzu ina neman hakkina."
na shiga uku uncle, kayi hakuri."
"kinsan Allah bazan iyaba, nayi hakuri sosai baby, wancan zuwan danayi dan bakya jin dadi ne shiyasa na kyaleki.
"Allah yanzu ma banda lafiya.
Shine kuma zaki biki? Kuka ta saki, tana bashi hakuri, sai dai uban gayyan bai saurara ba, tubeta yayi yana lasarta, ji yake kamar ya hadiyeta, dan kyau. Jikinta har wani sulbi yake yi, data ga da gaske yake, dole ta sakar masa jikinta baki daya, dan bata manta da ranar farko ba, irin azabar data sha dan haka yau ta bashi hadin kai duk da bata ji bambacin sa dana farko ba, tayi kuka har taji babu dadi, idon nan nata kamar jan riga ya zama, a haka barci ya dauketa, shikuma ya fita masallaci dan sallar la'asar. Koda ya shigo har ta shiga wanka itama, yana zaune a kujera gefen bayin yana duba wani littafin larabci, ta fito daga bayin, yanayin tafiyarta ya gano taji jiki, a haka tayi sallah, da yake rigarta mai dogon hannu ne, data idar saita rasa yadda zatayi, ta nutsu, saita tsinci kanta da cewa uncle na idar." ya dago ido ya kalleta, "toh me kike so ayi maki ko baki gaji ba? Da gan-gan yayi mata wannan tambayar, a'a ka kaini gidan kunshi."
bazaki ba."
kayi hakuri.
Toh ban duba baby na ba ai."
kayi hakuri.
Yaushe zaki bari in dubaki? Shiru tayi, ashe baki son tafiya?
Idan muka dawo." ya mike tsaye, very good, ya wannan gidan yayi miki kyau? Bata amsa ba yaci gaba, "ina son in saya ne, sai dai ban riga dana gama tunani ba.
Zo muje kiga yadda gidan yake.
Gidan yanada girma sosai flat mai dakuna sai aka yiwa mai gidan sashensa daban, gidan ya hadu, sai dai bata ce masa komai ba, shidai keta duminsa, da zasu tafi, sai da ya sumbace ta son ransa, sannan ya ajiyeta gidan kunshi, data shiga har anyima su hafsat, nan fa suka tareta da tsokana, sai da suka ga idonta yayi rau-rau, sannan suka daina, sai da suka kebe itada lawisa a dakin auntyn lawisar, take ce mata, ke kinga yanda idonki suka kumbura, sannan duk kwalliyar fuskar babu." hannunta takai kan uwani, ta cire mata dan kwalinta, gashinta ya zubo jikin gashin ma ajike, lafiya kuwa?
"wulakanci zakiyi min? Wallahi kema kin kusa shiga sahu.
Aini nawa ba soja bane."
ai ba daga nan ba, koda banga ango ba nasan kema sai ido ya raina fata a wannan ranar, amma dama lawisa kowa ya gane abunda ke damuna?
Kai 'yar uwa, sai dai inke kika fada, waya sanki nan, sai dai su hafsat da suka sanki. Inaso kidan saki jikinki, da an ganki dai an san mai juna biyu ce, dan cikin yadan fito, gashi kinsa doguwar riga."
kai lawisa da gaske wata na hudu fa kenan."
toh Allah ya saukeki lafiya."
ameen.
Haka sukai ta hirar su cike da nishadi.
Washe gari akayi mothersday, sai dai sam jafaru yaki yarda uwani taje, da yake inna bata gida, dole ta hakura. A ranar yaso ya sameta, sai dai yana jin tausayinta, saboda yasan irin wahalar da ita da yayi jiya.
Ranar jumma'a aka daura auren lawisa da yusuf, za a tafi kaita kaduna acan zata tare, abokan biyu sun sha kuka, a haka suka rabu, da jafar ya dauko su zuwa gida, bayan sun fita daga motar jafar yace zonan baby, muyi hira." ta bata fuskarta, dan ta riga da tasan irin hirar jafar, dan haka saita fara tafiya da saurinta, wai zata shiga gida, da sauri yace daughter rike min ita karta gudu." tana jin haka kuwa ai ta artaya aguje, sai cikin gida, su kuwa suka sa mata dariya.
A dakinsu bayan sun kintsa kwanciya, hafsat take cewa uwani, "ke ban fada maki ba, gobe nan iyayen isma'il zasu zo gaisuwa.
Kai don Allah? Ai gara yazo, dan haka kice gobe zamu ci da baki.
"ni kuma guest wa na hadu dashi a wannan bikin." ihu suka yi, "wa kika hadu dashi?
Wan lawisa ne. Uwani ta zare ido, "kaddai ince hamza?
"shikuwa ashe kin sanshi? Aikuwa yau kwana biyu kenan muna zance dashi. Yace min wannan shekarar ya gama bautar kasa, har ya samu aiki a jos." hafsat tace ashe kin zama 'yar jos?
Uwani kuwa idonta sun kada sunyi jajir. Bata iya cewa komai ba, duk farin cikinta ya koma ciki, in banda hafsat data gano, da yake ita tasan hamza na tare da uwani a da kenan, cikin dabara ta janye fa'iza zuwa falo, sannan ta dawo, "ba dai tonama kanki asiri zakiyi ba uwani? Hawaye daya makale cikin idonta suka gangaro, "hakuri zakiyi uwani tunda haka Allah ya kaddara."
nifa hafsat farin ciki nayi da wannan batun, saboda na riga dana san son da yake min shiya shafeta, dan haka nafi kowa farin ciki wallahi. Allah yasa ayi damu." hafsat ta rungumeta, "amin uwani, Allah ya kara mana kaunar junan mu.
Ameen.
Haka kuwa akayi washe gari akayi tambayar aure anan gidan kanin mahaifin su hafsat da yake dama shine waliyyin su, an yanke sadaki da kuma ranar aure, ya kama nan da wata uku.
Tuni uwani ta fara kamuwa da son jafar, tun randa ta shiga dakinsa taga littafai iri-iri na addini da qur'ani, sannan ta lura duk bayan la'asar zaka ganshi yanata karatu. ( toh bari muji shin jafar shiriya ce ta zo masa ko yay).

Sannan ta lura duk bayan la'asar zaka ganshi yana karatu, ko kuma yana karatun alqur'ani mai girma, a wannan zuwan nashi shima ya lura da hakan, da yadda ta bashi hadin kai, sai dai ita abunda yafi damunta shine sam! Bata da hutu daya kyalla ido ya ganta, toh shikenan fa, saiya like mata, har sai ya biya bukatarsa, sannan zai rabu da ita, a haka suke, amma inna bata san wainar da ake toya waba.
Sai da ya kusan sati uku a kebbi sannan ya soma shirye-shiryen komawa kaduna.
Yana zaune a falonsa uwani ta shigo tare da sallama, "haba baby tun dazu nake jiranki." ya tarbeta yana sunsunar gashin kanta, daya sha gyara, "baby ina sonki ina son kamshinki, baby ki soni dan Allah." ya hadata da bangon falon ya soma kissing dinta, itama a wannan lokacin ta iya maida martani, dan haka ta saki jikinta sosai, tsotsanta yake sosai, har tsayuwar taso ta gaggareta, sureta yayi zuwa dakin barcin shi, a wannan rana ta kauda kunya, ta bashi hadin kai dari bisa dari, saida suka murji junan su sosai, ya tabbatar ya yi mata abunda zata yi kewarsa, sannan ya barta,
sai da suka sami sukuni sannan yake ce mata tazo suje kaduna tare, ajiyar zuciya tayi, "uncle inna bazata bari ba."
ki gaya mata zata bari baby.
Ni dai kayi hakuri." ya shafa kuncinta, sannan yace, "promise me, you will take care of your self, don Allah ki daina yawo, baki san ina sonki ba, ina kishinki kuma baby." sai da dan dauki lokaci sannan tace "i promise." ya kara rungumeta, sai da suka ji an kira sallar azahar sannan suka shiga wanka, tare sukayi, suka fito dauke da alwala sukai sallah, ya dauki karamar jaka da zaiyi tafiya da ita, ya bude ya fito da wata 'yar karamar waya pink sony erison mai kyan gaske, ya mika mata, kan cinyarsa ta zauna tana yi masa godiya, shikuwa in banda aikin kallonta ba abunda yake yi, "baby kina sona? Tambayar tazo mata a bazata, dan haka saita sa hannu ta rufe fuskarta, ya rungumota fadamin baby, ina so inji ko hankalina zai kwanta, nan ma shiru tayi, "baby wannan kunyar taki tana wahalar damu baki daya...."
kofar falon aka kwankwasa, mal. Mamman ne, ya bude kofar, "yallabai inna ke tambaya ko ka fasa tafiyar ne? Agogo ya kalla karfe biyu saura, tana nan mal. Mamman dauko min jakar in shiga inyi mata sallama. Ya kamo hannun uwani suka kama hanyar cikin gida, nan suka ci karo da inna. Da sauri uwani ta fisge hannunta, inna tayi kamar bata gani ba, "auta an fasa tafiyan ne?
A'a inna yanzu zan wuce.
Uwani maza dauko masa kwanon nama na kicin."da sauri ta shiga ta dauko, sannan ya kama hanya, sai da ya fice sannan suka koma gida ita da inna.
Tunda jafar ya tafi, uwani ta tsinci kanta da kaunarsa, shiyasa fita ma ta daina, sai inya zama dole. Inna ta lura da yanayinta, sai dai bata ce da ita komaiba, sai tsananin kula data ke mata. Ita kuwa uwani tunda cikinta ya fito sosai, dan yanzu ya wuce wata biyar, a ko yaushe zaka ganta da hijabi tana boye-boye, sannan kunyar inna ta shigeta, haka kawai ta tsiri zaman daki. In kuwa suna tare ta dinga noke-noke kenan. Inna kam ba ruwanta, saima kara shiga ranta data yi.
Sannan tana kara janta ajiki. Shagwaba kuma ya karu, dan sai abunda take so ake girkawa a gidan.
Shikuwa jafar, yana isowa aka tura shi imo state yin course din wata uku, haka ya shirya ya tafi, ba wai ya daina harka da mata bane, a'a saidai tun lokacin daya san uwani a shimfida, sai ya ji duk wata mace bata burge shi, in dai a harkar nan ce, dan haka ya rage sosai, a yadda baka zato, sannan shan giyarsa ma tunda ya samu karbuwa gun inna ya rage, ba kamar da ba, da zaita shanta kamar ruwa ba.
A wannan lokaci ma in banda ya shata sau daya a wuni, shima dan ya zama dole ne.
Bikin hafsat ya matso, saura sati uku, aka yanke shawarar hamza ya fito inda gaske yakeyi, ai kuwa babu bata lokaci ya fiton, dan haka aka maida biki na mutum biyu,.
Inna taji dadi sosai, dan dama tana son hamza, a cewarta yaro ne mai sanin ya kamata.
Ana saura kwana goma sha daya amare suka sauka kebbi dan nan za ayi komai. Suna shiga suka rungume junansu, baki daya lokacin cikin uwani yana wata bakwai, babu batun boye-boye, ya fito sosaim su hafsat sai tsiya suke mata, tun da suke ta faman shirye-shirye, inna kuwa kullum idonta akan uwani, haka zata ajiye mata abinci dan tasan ta da ci, sannan saita tabbatar data ci abinci sannan zata kyaleta, ana saura kwana biyar daurin aure, gidan ya cika duk 'yan uwa sun iso, na nesa dana kusa, da yake gidan inna babban gidane ba a samu matsalar masauki ba.
Anti zainab da anti salaha tunda suka iso suke son ganin uwani, yadda 'ya'yansu ke basu irin labarin kyan data yi, suna zaune a falo suna hira, har ma da shatu, su uwani suka shigo, ta na sanye da riga da zani, sai babban gyale data yafa, tana shigowa idon kowa a kanta, ai saita ji kunya, da sauri ta karasa daki, aka kwashe da dariya baki daya.

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now