48

1.9K 137 0
                                    

Kallon kitse

kinga sai in shirya kenan."
ke uwani ban baki labari ba, na hadu da wani a bikin Nana dana fada miki zanje sati daya daya wuce."
kai dan Allah ya yake? ya hadu?
Toh bawai ya wani hadu bane tunda yanada mata."
kaji ki fa, dan mutum nada mata shine rashin haduwarsa?
Hum uwani kenan, bafa mata daya ba biyu gareshi, nikam bazan iyaba." toh in Allah yayi shine mijinki fa ya zakiyi?
"kedai bari 'yar uwa yanzu haka su inna (kakarta) sun san dashi, da yake family frinds dinmu ne....kai namij baida kunya, ko kinsan babban dansa warina ne?
Dan yana da da warinki shine me?
Gaskiya bazan iyaba uwani, nafa san matarsa ta farko, yadda take, je kiga yadda ta maida aunty murja ko mai aikin gidan albarka..."
kai don Allah, a'a nima naji tsoro amma ba nan take ba, zai iya yuwa ke kiyi nasara akanta."
uhm-uhm uwani bazan iya ba."
"ke dai baki sonsa ne ko?
Uwani ta tambaye ta.
Ajiyar zuciya tayi, "ba wai bazan iya son yusuf bane, a'a sai dai sam bana son ma in fara son nasa, saboda gaskiya matarsa nake tsoro, gashi iyayensa har sun fara kawo Baba zancen, nikuma har yanzu ma ban yadda nayi hira dashi ba. Uwani iyaye na nason wannan abun menene shawararki a gareni? Yau kwana biyu kenan da Baba yamin maganan yusuf, ya kuma nuna min yana so, itma Iya haka, itama tafi so, saboda mahaifiyar yusuf suna mutunci sosai da ita." kwallah suka ciko a idonta, na rasa mafita uwani, yau kuma Baba yace in fada masa amsata, me zance uwani?
Itama uwanin cikin hawaye take, saboda itama tanada nata matsalar, ta riko hannun lawisa tace, 'yar uwa nima a yau zan fada miki tawa matsalar, a ganina lokaci ne yayi da dole in fada miki, kin san yau wata na kusan takwas
da matsalar data adda beni, ta hanani sukuni, kullum take kadar dani, tare da hana min kwanciyar hankali....

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now