7

2.5K 172 1
                                    

KALLON KITSE PRT<>7<>

inna kina bata yarinyar nan da yawa, shiyasa take iskanci data ga dama. Ta buge masa kafa tace "nafadama ba ruwanka da yarinyar nan tunda bakai takeyiwa ba, ya kalli uwani data shige jikin inna tana kallonsa, ya hade fuska tare da harararta.
Da sauri ta rufe idonta, sai a lokacin ya soma gaida inna.
Inna tace bana amsawa, tunda shigowa kayi, kasani gaba kana yimin fada, saikace 'yarka.
Haba inna dan na fadi gaskiya?
Toh ayi hakuri ni albishir nazo miki dashi. Tayi fara'a tana duban shi.
Inna na sayi form na N.D.A a kaduna, makarantar sojoji zanje inyi.
Ta bata fuska auta makarntar sojoji kace?
Hakane inna kuma insha Allahu zan samu, dan ta hanyar wani tsohon soja mahaifin lawal abokina zai taimaka min....."
kayi min shiru dan Allah ya maganar zamanka doctor? Inna ai wannan ba matsala bace, ina nan a matsayin likita, zanjene kawai na samu cos da trainina na sojoji, shikenan fa. Don Allah inna ki amince min, saboda inada ra'ayin zama likita, kuma soja.
Inna tace toh ni bazan hanaka ba dan yanada kyau yin hakan, amma jafaru shekara nawa zakayi?
Haba inna wane irin shekara? Wata tara ne fa zanyi.
Ta tsura masa ido nadan wani lokaci, sannan ta kara ajiyar zuciya, toh jafaru aure fa?. Yayi murmushi,
inna dama nasan abunda zai dameki kenan, amma inna 'am still young shekarata fa ashrin da bakwai, yanzu bama cika ba. Zanyi aure inna 'don't worry' da akwai sauran lokaci.
Toh Allah sa albarka auta, ya kuma kare min kai, yaushe zaka tafi? Saimun rubuta jarabawacikin watan, sai sunan ya fito a list, sannan zansa ranar tafiya, Allah ya nuna mana ya kuma bada sa'a.
Amin inna haka nake so ki karayi min addu'a, ta harareshi. Dama kasan kullum muna cikin addu'ar.
Indo ce ta shigo falon a'a saukar yaushe kato? Yayi murmushi da har hakoransa suka fito, wato indo bazaki daina kina da wannan suna bako? Kin san zan zama soja? Tayi dariy ba'a dai kake, wane irin soja kuma?
Allah zanjje N.D.A Insha Allahu.
"toh fa aure fa? Ka isa aure fa? Zanyi amma ba yanzu ba.
Indo tayi jim sannan tace Allah bada sa'a.
Ya fadada murmushinsa, "waiku da mutum ya taso sai afara maganar aure? Tayi dariya inda kauye kake, daka ajiye mata uku,
yace keni bana ra'ayin mata biyu balle uku, soja fa nace miki zan zama, cikekken soja kuwa mata daya yakeyi.
Dalla can inda bamu san inda gugar zanar takeba, sojoji nawa keda mata, har hudu ma?. Ya mike nidai daya zanyi. Ina kuma zaka abincin fa?
"yanzu zan dawo zan shiga gidan su safwan ne"
toh a dawo lfy, inna kinji jafaru inda yasa kai kuma? "bakiga nayi shiru ba? Halin sak! Dana mahaifinshi, shima in gaya miki ra'ayinsa daban yake dana mutane, akwai lokacin da 'yan uwansa suka sashi gaba, wai sai yayi aure, da yake mun dade muna haihuwa yaran basa zama, dakyar zainab ta fara tsayawa, sai dai ya sake aure shi kuwa yayi musu mirsisi yaki yayi auren nan.
"hakane fa toh Allah bai daura masu sonyin auren bane, amma fa anya jafaru zai iya dauriyar mahaifinsa?
Toh zamu gani, Allah ya nuna mana, ke uwani tashi kidauko abinci kici. Indo tace nasan shigowar jafar yasa tayi shiru kamar bata dakin, shine kadai maganin rashin jinki.
"kai indo yanzu har wani rashin jine da uwani?
Inda shatu tana nan data baki labarin na jafar, dan ita tasan shi kamar yunwan cikinta.
"ai fa kam, koda bansan na yarintarsa ba, shima din akwai rigima.
Da result ya fito jafar ya zama cikekken likita, zai iya aiki a kowane asibiti, da yake shi likitan mata ne wato 'Garnicoligist'. Inna kam farin ciki sosai tayi shi, ya soma neman aiki anan babban asibitin kebbi da wata private 'godiya specialist hospital.'
a private din aka daukeshi, da yake shikam yanada kwazo, cikin lokaci kankani jama'a suka fara son aikinsa, hatta ma asibitin yaga canji, cikin 'yan kwanakin nan daya zo asibitin. Sam baya wasa da aikinsa, lokacin aiki, aiki ne sai da daddare ne daga wannan sai gaiya ce shi party sai ranar da ba aiki, saiya wuce sokoto dan acewarsa matan sokoto sunfi wayewa.
*** *** ****
suna tare su dukansu, sun hadu a sokoto, safwan shikam anan sokoton yasami aiki, shikuma bashir a lagos yasamu, yana aiki awani kamfanin kawunsa. Bashir yace ni kana bani mamaki wani irin soja kuma? Bayan ka gama wahalan zama cikakken likita wurin shekara takwas, ka kwashe, shine yanzu kuma zaka kwa-kwalowa kanka sabon aiki?. Safwan ya shafa gashin kansa yace shifa na gani?
"ku bazaku gane, na riga na rubuta exams din anan N.D.A, ku kam is just for nine months, aiba wani da dewa zanyi ba.
Toh Allah ya taimaka (amin),
"inaso ma in fada muku nifa aure zanyi". Inji safwan, kai dan Allah yaushe" gara ka bude mana kofa dan nima inaso inyi." inji bashir.
"eh toh zai iya kai mext year zanyi"
"ashe zan rigaka, saboda ni na gida zanyi, "yar kawuna zan aura, anaso nanda wata biyar, jafar ya kalle shi kace dai zaba maka ita akayi?

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now