45

2K 151 0
                                    

Kallon kitse

shine yanzu zanji daga sama ance kayi aure? Wannan wane irin cin fuska ne? Memwkon ta bashi tausayi, haushi ne ma ya kamashi, ita ta manta lokacin data ke cewa, ya aureta, bai amsa mata, ya fada a ransa.
Ta katse masa tunani da ya ji tace, "it is over Oga bazan lamuntar ganinka da wata ba it is over." ta kara maimaitawa, tare da barin wurin, yama kasa motsi, don dai baiso ta fadi hakan ba, duk a cikin 'yan matansa yafi ji da ita, ba dan komaiba, sai dan ta iya kwanciya da namiji, sam bata gajiya da abunda ya keso.
Toh amma shi bazai iya aurenta ba, dan gaskiya ba zai yadda ya fada tarkon daya shiga a baya ba. Zai dai zauna da ita a haka, yadda suke, sannan zai biya mata bukatunta, amma bazai iya aurenta ba.
Duk abunda akeyi a kunnen marliya, dan haka ranar ruwane kawai bata zuba a kasa tasha ba, tunda suka bata da jafar, yau ne ranar data yi farin ciki a rayuwarta, har ma ta manta da yadda farin cikinta yake, sai yau ta tuna.
Shima kuwa yana zaune anan inda yake kamar gunki, gaskiya yana jin dadin zama da jamila, dan haka da sauri ya mike yabi bayanta, koda ya isa ya isketa tana kwashe kayanta, da sauri ya isa gunta, "haba jamila ki tsaya mana muyi magana."
bata daina abunda ta keyi ba, ya isa gunta ya rungumota ta baya, yana yi mata magiya, "haba jamila ki saurari abunda zance mana, kinsan ina son zama dake."
"naji kana son zama dani amma baka sona. Ta fada tana jiran amsa, sai dai bai iya cewa komaiba, ta juya tana kallonsa cike da bacin rai a tare da ita, "dama ba sona ka keyi ba? Ta tambaya, nan ma shiru yayi dan gaskiya ta fada, baya sonta.
Taci gaba da cewa, Oga ni zaka cuta? Na gode, amma bazan iya ba, na gane ba sona ka keyi ba, yaudara ce tsakanina dakai, so ka keyi in zauna ka rinka biyan bukatarka dani, toh bazan dauka ba."
ta dauki jakarta ta wuce zuwa bakin kofa sannan ta juyo ta kalleshi, hawaye tab da fuskarta, jeho masa makulli tayi, "ga gidanka nan, Allah ya hada kowa da rabonsa." ta wuce zuciya ta kai shi da har bai iya cewa komai, shirin barin gidan yayi, mashayarsa ya wuce, saida ya cika tab sannan ya wuce gida.
A yau satin su inna daya da kwana biyar, da yake saura musu sati daya su dawo, dan hakane uwani ta rasa inda zata sa kanta, a makaranta kuwa saura wata daya su fara zana weac sabo da haka nema suke ta fama da karatu."
ana saura kwana biyu inna ta dawo jafar ya isa kebbi, da yake ranar jumma'a ne sannan bai taso da wuri ba, yayi dare, koda ya isa har su indo sun kulle dan dama tunda inna ta tafi tare suke kwana da indo.
Washe gari sai ganinsa sukayi daga sama, abun ya basu mamaki, ita kam uwani jinin jikinta tasha, saboda irin kallon daya ke yi mata, sam baya so, inya na kallonta ko hada ido sukayi, baya dauke ido daga gareta, ko meyasa? Shikuwa sha'awace, kauna ce, so ne, kai komai ma ji yake akan uwani, kullum kara kyau take yi, shiya rasa ko shi kadai ke ganin haka? Yayi ajiyar zuciya toh meyasa ita bata jin abunda yake jine? Ya tambayi kansa.
A wunin ranar sun wuni sunata faman gyara wuri, da kuma shirye-shiryen kayan abinci, dan haka jafar da kansa yaje yayi cefene, a daren sukayi farfesu, suka soya naman kaji, harda dambun nama da duk wani aiki da shirye-shirye sunyi a wannan rana, saida suka gama sannan suka shige.
Washe gari jafaru ya shiga cikin gida yanata kwala sallama, amma ba a amsa ba, ya leka kicin nan ma bakowa, har ya dauki cinya kaza da aka soya, ya fara ci ya shiga cikin falo, nan ma bakowa, kai tsaye dakin uwani ya shiga, gabansa ne ya fadi dan uwani ce a kwance tana bacci, vest ce a jikinta, wadda bata da nauyi da gajeren wando na ainihin vest din
, tayi masa kyau sosai. A hankali ya kulle kofar da key, ya ajiye makullin saman wadrope dinta, ya tube jallabiyar dake jikinsa, ya rage daga shi sai gajeren wandosa.
A hankali ya hau gadon ya kwanta daga gefenta, inda zai iya ganin fuskarta dakyau, saida yayi mata kallon minti hudu sannan ya soma hura mata fuskarta, a hankali ta fara bude idonta, sukai ido hudu da jafar, da saurin gaske tayi niyar mikewa, amma saita kasa saboda jafar ya riketa, a firgice tace uncle.....uncle

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now