23

2K 154 0
                                    

KALLON KITSE PRT (23)

inna gashi nikam na koshi, dazun nan naci abinci."
"yauwa na tuna uwani akwai wani kaya da salaha, dauko in gani." da sauri ta mike, suna ina inna? Ta tambaya, "suna cikin wadrope din kayan ki." ta dauko, kayane kala uku shaddabiyu da lace daya a dunke suke, "uhm wannan dinkuna da salaha keyi muku kamar abunda za a sawa 'yar tsana?.
"gaskiya inna dinkunan sunyi kyau, tasan irin wadanda nakeso, dama ni bana son manyan kaya."
"eh mana, nasan kyace haka, kinfi so kisa kaya duk ilahirin suranki a fili ko?
"toh inna ba inasa abaya ba, in zan fita aibaki ganiba."
"na lura da hakan, amma ai ba koda yaushe bane.
Inna yanzu fa su ake yayi, ko bakiso nima inyi yayi?
"inaso uwani amma a lura da kama kai, kinsan ita 'ya mace anfi so a ganta da kamun kai sosai."
tace, hakane inna, zan kula bari inje in gwada ko zasuyi min." ta shiga daki, inna tabita da ido, a lokacin indo ta shigo.
Uwani ta shigo tana juyi, "inna ya kika gani? Inna ta tabe baki, sunyi kyau." indo ta kalleta tana dariya, "wannan wane iri dinki ne kuma, ya matseki uwani, ke dan Allah yayi miki wannan cikan kirji haka, ina ke ina wadan nan kayan? Ki kai a buda maki su." a shagwabe take magana, inna kin ganta ko?
Nidai haka nakeson kayana."
nima dai haka nace wannan kaya kamar na...." uwani ta katseta da, inna ni dan Allah kudaina cewa haka." ta rinka buga kafa a kasa cike da shagwaba, indo dariya ta rinkayi, "lalai duk wanda zai daukeki gun inna nan taki, saiya yi da gaske, shagwabar taki kullum karuwa ta ke."
"inna kin ganta ko, babba batada magana saina a rabamu."
ki kyaleta kinji ba inda zaki.
Habawa yarinya dole ki bar inna taki watarana." haka zaman nasu yake a kullum gwanin sha'awa.
Uwani haka ta zama kamar gwal gun inna, a koda yaushe suna tare, hatta nanda makota inna zata shiga, toh tare zasu shige shi, in tana nan.
Uwani dai ta zama babbar budurwa, dan komai nata ya fito ya batse, batada jiki sosai, amma akwai cikar kirji, sai kunya da Allah yayi mata.
Tana shiga na english wears, saidai bata taba bari ta fitar da tsaraicinta a waje ba, dan tana aza hijabi ko abaya, ta rufe shigarta ruf!
Makarantar da take zuwama suna sa hijab dan islamic school ce, tanada kawaye, amma tafi shiri da lawisa, itama lawisa anan kebbi take zama iyayenta, saidai gidansu babban gidane, irin gidan nan ne da duk 'yan wa da dan kani, saidai kowa da sashensa. Sun shaku da lawisa sosai, tun suna j.s one suka hadu, gashi yanzu zasu shiga s.s 2, lokaci kenan ba wuya!
Tare suka shigo da lawisa suka iske anyi baki a gidan, dan haka cikin daki suka wuce, inna ta kirata, uwani baki ga su hafsat bane?." ta fito a guje, "ina take inna?
"bata waje? Kila tana gun indo."
da gudu suka karasa dan dama su hafsat ma sun saba da lawisa, suna isa suka fada kanta suna ihu, indo tace, "wadannan yara ba kwa  girma, kullum haka kuke." ta fice ta barmusu dakin, "yan iska." inji hafsat, waya fa nake kuka tsinka min."
"dawa kike wayar?
"zakuji ne, meye na sauri na baka na zuba? Za a kara bugowa, sai kuyi guesing." uwani ta kwashe da wata uwar dariya, "kaddai wannan katon mutum daya nace makin ne?
"kedai shine, amma yanzu fa badama dan inayi dashi." lawisa tace kina nufin kina sonsa?
Hafsat ta rangwada ido, "eh ina sonsa." guda uwani tayi,
"Allah ya kawomu hafsat za a zama matar aure!."
hafsat tabita suka fara zagaye dakin suna dariya, "kedai ce matar aure, saboda zaki rigani yin aure."
"wazan aura? Nida ko son bansaniba, ke kuwa tun yanzu kin fara shi, wai su fa'iza fa." (diyar zainab kenan wanda suke sa'a daya)
tana nan zuwa, amma sai hutu, nima da kyar mama ta bari nazo, ran lahadi zamu koma."
toh Allah kaimu."
***** **** **** *****

jafar kuwa, ya sami shekaru hudu rabonsa da kebbi, suna sheka soyayya da yake hankalinsa ya dan kwanta, har kiba yayi.
Ita kuwa gimbiyar tasa harda teba tayi don kiba, gashi kibar sam batayi mata kyau ba, don dama ta kwana biyu, a kalla yanzu zata kai shekara arba'in da biyu.
Ana cikin haka da yake jamila ta dawo zama dasu, tunba yau ba, itama tayi kiba sosai abinta, duk abunda taga dama shi takeyi, samari kuwa ba irin wanda basa shigowa, shidai baya magana, amma abun naci masa tuwo a kwarya, dan tun abun nadamunsa har ya cire shi a ransa.
Rannan suna zaune a falo shida gimbiyar tasa, sai take ce mishi, tana so tayi tafiya zuwa maiduguri, ya kalleta baice mata komaiba, dama in zatayi tafiya, aiba neman izni takeyiba, saidai ta shirya ta tafi abunta, ta narke a jikinsa, "doctor bakace komaiba." yaja hancisa kamar mai mura yace, ba damuwa, Allah kaimu."
haka kuwa akayi, washe gari ta wuce da mota ta tafi, don tana tunani inzata dawo ta biya wani kauye wurin sabon malaminta, acan gun shanshani take dama kowacce zuwa tayi dole yayi amfani da ita sau ashirin da bakwai, dan haka aikinta ya gada, awannan zuwa ta nemi sassauci
akan ita ta gaji da wannan, dan haka shanshani ya amince, amma da sharadin zata rage kwanciya da mijinta. Tace,

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now