34

1.9K 151 0
                                    

KALLON KITSE

Can kasar somalia ne, kasan inaso abani major dan haka, dole ne saida course ko ince maka dole muje yaki ba yadda bata kasancewa, nidai kutayi min addu'a Allah ya dawo dani lafiya."
insha Allahu zamuyi addu'a jafaru, kuma za a dace, dan Allah mai karbar addu'a ne ako da yaushe." a sanyaye ya wuce gida, abun mamaki uwani ya gani tareda wani tsaye suna hira, bai taba tsammani yana son uwani ba, sai aranar dan wani irin kishi da bakin ciki ya kai masa wuya, ji yake kamar yayi ihu, sai dai yasha jinin jikinsa ya wuce ta gaban su, dan yaga irin mutumin daya fishi.
It kuwa data lura dashi, saita kara sakin jiki, tana ta kecewa da dariya, tareda fadin kai hamza bakada dama wallahi." cike da nishadi, saida karfe tara saura sannan ta shigo gidan, takai wajahen zauren da zakabi ka shiga gida, saiji tayi an jawota, kamar wata kaza dan rashin nauyinta, a tsorace tace, "wayyo!" jafaru ya hadata da bango ya matseta, ita kuwa ta runtse idonta, tana bashi hakuri, "waye wannan dan iskan yaron, dana ganshi tare da ke waje?
Gabanta bama faduwar uku yakeyi ba, goma yakeyi, dan data kalleshi, yadda fuskar ta zama kamar ta zaki, amma saboda tsiwa iri tata, sai cewa tayi, "meye ruwanka dashi? Saurayi nane, shi nake so!."
"ni kike fadawa magana? Hannunsa taji cikin rigarta, dai-dai cibiyarta, a lokaci daya ta kwalla wata irin kara wanda shi kanshi sai da ya razana, yayi saurin sakinta, yana saukar da numfashi yace, "gobe ma in sake ganinki dashi, saikin gane kurenki wallahi." daga can bayansu inna ke kwallawa uwani kira, tana fadin subhanallahi, lafiya? Da gudu uwani ta bar wurin, ta karasa cikin gida tana kuka, ta rungume inna, ke lafiya? Me akayi miki?."
daga can jafar ne yake magana, "inna tadi take da daddare."
"da gaske ne uwani?
"karyane inna."
"ni nake karya?." yayi kamar zai zo gurin, da sauri ta gudu ta boye bayan inna.
Toh ai saikayi hakuri ko? Tun da ko mutuwa najin kunyar mahaifi."
"inna yarinyar nan fa ta rainani, Allah zan daddakata.
A'a babbalta zakayi, wato ina baka hakuri, amma bakaji ko? Ai nasan nan gaba har ni saika doka, dan agane wannan soja daka shiga ka zamto wani tantiri a rayuwarka."
sai a lokacin ya sauka, saidai bai daina huci ba, saikace kumurci, "inna ayi hakuri, dama nazo ne ince miki zan koma wurin aiki, an nemeni zan wuce course somalia, addu'arku nake bukata, dan kinsan ba zaman lafiya akeyiba a yanzu haka, inna kiyafe min, kiyi min gafar abunda nayi miki," kwalla saida suka cika idon inna, amma sai tayi na maza tace, "toh Allah kiyaye, ya kuma baka abunda kaje nema na Alkairi."
tunda ya shigo kebbi ba randa yafi jindadi kamar wannan daren, dan addu'ar da inna tayi masa, yasa inna ta yafe masa, har a zuciyarta, toh amma meyasa bazata bashi uwani ba?
Washe gari tunda safe ya bar kebbi cike da kewar 'yan uwansa, saida yabi ta gusau yayiwa zainab bankwana, sannan ya wuce kaduna, da yake ta abuja zasu wuce, sai anan ne zaiyi bankwana da salaha, ranar asabar suka wuce, Allah ya dawo dasu lafiya (ameen)

**** **** **** *****

Tunda jafar ya tafi uwani da inna sula sami sakat, dan duk sun saki jiki, uwani harda sa hamza tayo yaje ya gaida inna.
Inna kuwa ta amsa masa a cewarta ta san yanada mutinci, saboda dan babban gidane, soyayya sosai suka kulla kusan kullum saiya zo gidan hira. Ayau ma yazo sunata hira cike da nishadi, shin wai yanzu saura shekara nawa ki gama school?." kanta a kasa tana murmushi cike da jin kunyarsa, "yanzu mun fara jarabawa, zamuyi hutun first term, na s.s 2 kenan."
Ah ashe da saura uwani nidai na matsu." ta kara fadada murmushinta tace, "tun yanzu? Nifa so nake ma in wuce universty?."
gaskiya bazan iyaba uwani, sai dai in baki sona wannan kam." sai a lokacin ta dago idonta, sukai ido hudu, da sauri tasa idonta kasa tace, toh ai kaima student ne."
hakane, toh amma ai kafin nan da shekara na gama, sai in wuce service, ko kuma in bari har sai na aureki tukunna." tayi saurin ware ido a ranta kuwa, tunani takeyi, anya ayi haka? Gaskiya ita tafi son ta auri mutumin daya mallaki hankalin kansa sosai, da dai zaiyi hakuri nan da shekara hudu sai a fara maganar aura, a lokacin itama ta kara girma sosai, amma ai inta gama secondary iyakarta shidda......
"uwani ya katse mata tunani, "kina saurarena kuwa? Ta murmusa, eh meka gani ne."
kirr, wayar hamza ce ke kuka, yayi saurin mikewa, "kinga har na sha'afa mama na can na jirana, bari zanje indawo, inkuma ban dawo yau ba, sai gobe idan Allah ya kaimu, koya kika gani?
Yayi dai-dai ta kama hanyar gida, gara ka tafi kada ka bata mata lokaci."
haka soyayyarsu ta kasance, sun shaku sosai, haka ma da inna itama tana son abunda uwani take so, dan haka hamza ya zama na gida a kullum zaizo harda shi a girkin gidan.
Inna na zaune a falo, uwani da lawisa suka shigo kamar wadanda aka jefo, inna tace wannan wace dabi'ace kuma, kamar wadanda aka jefo?
"wallahi inna mun gaji, yunwa mukeji, kinsan yau muka zana jarabawar karshe, sannan an bamu hutu a yau din."
"toh Allah bada sa'a,

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now