30

2.1K 162 0
                                    

Kallon kitse
30

Jafar a daren ranar kasa bacci yay, dan gani yake bazi iya auren uwani ba, she is too toung." ya fada afili, shikam ai ko 'yar shekara sha takwas bai iya aurenta,, balle 'yar mitsitsiyar yarinya kamar wannan.
Shi yafi son matan da suka waye, wadanda suka iya soyayya, ba irin wadanan yaran kauyenba, da basu uya ko gyaran jiki ba, saika ga mace, har mace, amma common kula da jikinta bazata yiba.
Yayi ajiyar zuciya, tareda juya kansa, "it cannoy be possible, bazan iyaba! Duk a fili yake zancensa.
Tsaki yaja ya tashi ya shiga toilet yayo alwalah, ya soma nafilfili kamar yadda ya saba.

***** ***** ****
uwani wanda a makaranta anfi saninta da Aisha Dalhatu duk da ba wani shekaru gareta ba, amma Allah yayi ta da wayo, tana tsaka tsakiya wurin ilimi, wato average a turance kenan.
Uwani irin yaran nanne da suke da surutu kamar yadda kuka sani tun farko, tanada fada sosai, in kayi da ita, dan hakane bata shiga lamarinka, dan ma kada ku bata.
Lawisa ita ta kasance mai hakuri shiyasa suke zaune lafiya da uwani, sannan sunfi shiri da hafsat, saboda hali ya zama daya da uwani, itama bata da hakuri, duk da bata kai uwani fada ba, sai dai fa'iza itama ba kyaleba, shiyasa basa shiri da uwani sosai, sannan fa'iza ta zama irin 'yan matan nan da suke nuna komai su suka iya, wani bai iyaba.
Shiyasa a kullum suke fada da uwani, ko dan ita fa'iza tana zama a Abuja ne?oho!
Kamar kowane hutu yanzu ma ansamu hutun mid-term break dan haka fa'iza ta shigo gari itada hafsat.
Uwani ce zatayi sauka tun watan daya shige, sai akayi shawar a bari sai su hafsat sun sauka, sai a shirya walima, dan haka shine aka sa shi dai-dai da mid-term break dinsu,
haka kuwa akayi, dama ana shirin haka jafar ya fado
suna zaune baki dayansu a falo, suna ta hira, inna ma tana zaune tana 'yan karance-karancenta, daga sama sukaji sallamar jafau, hafsat da fa'iza da sauri suka mike suna fadin, "Oyo-oyo uncle."
suka rungumeshi, shikuwa cike da fara'a ya rugumesu yace, "a'a daughters yaushe agari?," suka fada masa, suka sami wuri suka zauna, suna kara gaisawa.
Uwani kam tana gefe ko kallo basu isheta ba, ta maida hankalinta kan t.v tana kallo. Ya dubi inda take, "ke baki gaisuwa ne?
Ta dan wayance tace, "dama inaso in gaidakai uncle, so nake su hafsat su gama nasu." sai a lokacin ya gaida inna, yace, "ke tashi ki dauka min abinci na."
ta mike ta fita binta da kallo yayoi, gaskiyane uwani ta girma, dan ba abunda yafi daga masa hankali irin kirjinta, nan gaba inta kara zama mace ba karama  za ayiba.
Kodai ya yadda da shawarar bashir ne? Kai no tayi karama dayawa, zai hakura har sai ta kai munzalin sanin ciwon kanta.....
Ita ta katse masa tunani da ajiye abinci a gabansa, idonsa sai akan kirjinta.
Da sauri ya dauke idonsa, kai su jafar ba dama, dole yasa yaci abincin amma tunaninta na tare dashi, yana satan kallonta, a daburce, namiji kenan!
Hafsat ta matso kusa dashi tace, uncle gift din me zaka bamu? Gobe fa walimar saukar alkur'ani mai girma zamuyi."
"kai don Allah, inna ba a fadamin za ayi sauka a gidan nan ba?
"toh kaida yaushe ka shigo gidan, da har zaka san abunda ake ciki?
Ya sosa keya, "kai inna kidaina tuna baya mana, am back for ever, tace Allah yasa."
ya dubesu "toh me kuke so?
"kome ma kasai mana mungode uncle."
"hakane badamuwa am going to suprise you, insha Allah."
haka dai sukai ta hirarsu, har karfe goma na dare, sannan ya fice daga daga gunsu, sun shige daki, suka ci gaba da hira, irin tasu ta 'yan mata. Fa'iza tace, "bara nayi gulmar uncle. Kunga yadda uncle
ya canza kuwa, sai kace irin halfcase din nan, yayi kyau wallahi." hafsat tace, kinsan nima abunda na gani kenan, gashi dan gaye, gaskiya duk macen data sameshi tayi sa'a, dan ba karamin haduwa yayi ba, uhm kinga kafarsa kuwa, fari tas kamar wanda baya taka kasa, ance shi soja ne, toh amma kamar baya wahala....ke kinga yanda ya goge kuwa? Kinsan ance doctors a sojoji sunfi jin dadi, dan su an daukesu musamman ne agun aikinsu."
ita dai uwani saurare takeyi, dan tun shigowarsa tasan ya samu lafiya, dan ta shaida kyawun nasa.
Babu abunda ke damun jafar irin yadda inna bata saki jiki dashi ba, sam bata shiga harkarsa kamar da, lallai yayarda da abunda bashir yace masa, dole ne ya fuskanci irin haka, gashi kuwa yana gani.
Yayi tsaki, zaije ya nemi shawarar baba yunusa, dan abun ya isheshi, dakyar bacci ya daukeshi.
Washe gari tunda safe su uwani suka tashi, suka gyara gida kamar yadda suka saba, masu kujeru suka shigo da kujeru a tsakar gida, an fara jerawa, a lokacin jafar ya shigo cikin gida, ya sami inna zaune a kujera, tana karin kumallo, ya nemi wuri dab da ita ya zauna.
"inna ina kwana?." ta amsa cike da fara'a, saidai abun da ya lura dashi, kamar fara'ar bata kai cikiba.
Ya matso ya laika kwanon abincin data keci, waina ce miyar allaiyahu, tasha man shanu, zaisa hannunsa, saiya lura da tabata fuskarta, ya tuna da inna ba abunda tafi so kamar su zauna suci abinci tare, amma gashi kyamarsa ma

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now