1

848 23 2
                                    

🍇🍇MIIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓

Written by noor Eemaan

All characters in this story are all drawn from my imagination, any resemblance of story or life style should be consider as a coincidence.

Ban yarda ajuyamin labarina ta ko wacce siga ba, sannan duk wanda yayi daidai da yanayin rayuwarsa yayi min afuwa🙏

The experience writer of RAYUWAR FAHEEMAH and now👇
MIJIN AMMINA NE SILA

In the name of Allah most glorious, most merciful.

Page1-2
*ASALINSU*

Rahilat yar asalin cameroon ce, su biyu kadai iyayensu suka haifa, ita da yayyarta raheenat, tun tasowarsu basu san wani dangin nasu ba domin suma haka iyayyensu suka taso yan siraru, yau da gobe wasu sun mutu basu kuma sun bar garin domin neman na kai domin sosai suke fama da talauci akauyen nasu.

kwance tashi har Allah yakawo wa raheenat miji aka yi biki wanda mijin mai suna nadeem kauyensu ke gaba dana su rahilat, akwai ranar da su rahilat baza su taba mantawa da ita ba, ranar da aka yi ruwan sama mai karfin gaske wanna yayi sanadiyan rayuwarsu domin ko gawarsu ba'a gani ba, rahilat kuwa tana gidan yayarta raheenat, ta yi dare sai tayi zamanta dasafe sai tayi sammakon tafiya domin daman maa( mahaifiyarsu) tace mata matukar ta kai sakon yamma tayi mata ta zauna zuwa safiya domin hanyarsu bata da kyau, ai kuwa a washegari labari ya je musu, hankali tashe sukayi kauyensu, sosai sukayi kuka ganin gidan nasu tamkar mutum mai rai be taba rayuwa a ciki ba, har bukkar dasuke kwana ba alamarsa domin ruwan ya tafi da komai da kyar nadeem mijin raheenat ya rarrashe su suka koma kauyen da raheenat ke aure...

Su raheenat sun cigaba da kula da rahilat iya iyawarsu, bayan shekaru hudu rahilat ta hadu da wani buzun saurayi dan nijer me suna sajeed wanda kasuwanci ya kowashi nijer, ya rasa ubanshi tun yana karami yana tare da mahaiiyarsa tare da yan'wanshi a babban gidan shi dake nijer domin yana da wadata, silan ahaduwarsu kuwa aranar raheenat ta aike rahilat kasuwa yayinda sajeed yazo kasuwar kauyen domin kasuwanci sa babu abunda ya dau hankalinsa kamar nutsuwarta da kuma brown skin dinta domin kyakyawa ce ajin farko amma ba fara bace, sabanin shi dayake fari sosai, be bar kauyen ba sai da ya datsa soyaayar sa azujiyar rahilat...

Bayan makonnin hudu yadawo tareda iyayensa domin a nema masa auren rahilat, duk da an kai ruwa rana kafin mahaifiyarsa ta amince domin acewarta tafi son ya auri yar nijer din, babu bata lokaci aka saka sati biyu masu zuwa da labarin talaucin su rahilat ya riski ummi mahaifiyar sajeed take takara jin tsanar rahilat domin ita kam bata son hada jini da talaka haka akayi auren suka kaita nijer wanda su raheenat jikinsu ita da nadeem asanyaye suka dawo asanadiyyar irin tarban wukalanci da aka musu

Haka ta cigaba da zaman hakuri a gidanta wanda tare da mahaifiyar sajeed har ma yan'uwansa na jiki ke zaune a babban family house din nasu, sosai rahilat ke zaman hakuri dasu, wurin mutane biyu kadai take jin dadi a gidan daga sajeed sai kanwar sajeed zulaihat wacce ke so rahilat sosai, sannan idan sajeed na gida basa takura mata domin duk wani nauyin gidan shi ke dauke musu shiyasa idan yana gari basa taruka mata bare sata aiki.

Bayan shekaru biyu rahilat ta haifi kyakyawar yarta wacce ta dauko brown skin din rahilat, duk wahalar nakudan da rahilat take ummi na ji amma bata ko leko ba, sai da zulaihat ta dawo daga makaranta hankali tashe ta kira wata unguwarzoma ta karbi haihuwar sai dai rahilat ta galabaita da kuma zub da jini sosai, domin ta kyar ta haihu saboda karfinta ya kare...

Kwanan ta biyar da haihu sajeed ya dawo daga tafiyan harkan kasuwancinsa, yayi murna sosai yama ki ajiye baby, su zulaihat sai dariya suke masa rada mata suna yayi kana ya kallesu fuskarsa dauke da murmushi yace Allah ya raya mana ABRAR SAJEED.
Dan'uwa menene ma'anar sunan yayi dadi, abrar ya nufin (mai tsoron Allah) masha Allah suka fada a tare domin sunan yayi musu. Zuhailat ummi bata shigo bane? ban ga kowa ba tun shigowata sajeed yatambaya inda- inda tafara yi domin batasan mezata ce masa ba duk da abunda ummi keyi bata jin dadi sam. bata jima da fita ba ka shigo rahilat tayi saurin fadi, cikin gamsuwa da jindadi ya jinjina Kansa, ajiyar zuciya zulaihat ta sauke ahankali tana yaba kyakyawan haleyan rahilat azuciyarta...

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now