17

153 9 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓
(A heart touching story)

written by noor Eemaan

page-33-34

kura masa ido yayi yayinda yake jin wani yanayi atare da kyakyawan saurayin da ko fuskarsa baya gani, haka kuma yaji hankalinsa gaba daya ya raja'a ga wanna saurayin wato Aabaan.
"oga ya kana yawa ne, kazo mu tafi muyi abunda ke gabanmu ko ya?" manu ya katse masa tunaninsa cikin muryansa wanda daga ji zaka tabattar da cewa shi din mashayine...

Ajiyar zuciya alhaji Shettima yasauke batare da ya kuma bawa manu amsa ba suka nufi cikin asibitin still hankalinsa naga Aaban,.... duk wani ward dake cikin asibitin suka duba amma babu ko me yanayin kalar fatar Abrar bare me kamaninta, guiwa asanyaye suka fito yayinda alhaji Shettima ya kurawa daidai inda motar Aaban ke fake dazu ido, sai de yanzu motar bata nan, huci mai zafi ya furzar ya kasa gane dalilin daya sa tunanin wanna saurayin kasa barin zuciyarsa.
"oga da dukkan alamu bakuyi nasara ba domin naga fuskarsa tayi ja jawur kamar jan kosai" kwaro ya fada ko dar be ji ba, alhaji Shettima ya saba da maganganun kwaro domin akwai yaba wa mutum magana mara dadi musamman idan ya shahu, maimakon ya bashi amsa se yace "kwaro baku ga wani saurayi tsaye a kusan da motata dazu ba?"
"Allah ya ja da ran oga ina mu ina lura dashi tunda ba abunda ya kawo mu ba kenan".
alhaji Shettima be kara cewa komai ba ya bawa motar wuta suka bar asibitin.....

bangaren Aaban kuwa yana isa gida ya tarar da mummy zaune kan kujera, gaisheta yayi ta amsa ba yabo ba fallasa, hakan ya kuma taba zuciyarsa domin ba haka ta saba tarban sa ba, part dinsa ya nufa yana fatan har yanzu Abrar bata tashi ba, mummy da kallon takaici ta bisa ganin wai saboda Abrar ya daina night duty ita shekara nawa tana fama dashi akan ya daina aikin daren nan amma yaki sai yanzu saboda mahaukaciya ta aiyana aranta....

yana shiga dakinsa ya dora hannu a kugu ganin yadda dakin ya dawo kamar ya shekara be ga gyara ba, kallonta yayi yaganta zaune da kayansa riga da wando ta dora saman doguwar rigar jikinta, murmushi dabe shiryaba ta tsubuce masa, domin kayan sunyi mata yawa matuka, cikin tafiyarsa ta lafiyayyen namiji ya shiga takawa zuwa gareta, kusa da ita ya tsaya yayinda ya kura mata idanunsa masu matukar kyau, sai a lokacin ta lura da shi, dariya ta shiga yi kana ta hau saman gadon sosai ta shiga tsalle tamkar yar shekara 5 kallonta ya dinga yayinda murmushi ya kasa barin kyakyawar fuskarsa, gasashiyar kaza mai romo daya siya mata ya bude mata ledan hadi da janyo yar table din glass ya dora akai, hannunta ya kamo ya zaunar da ita yayi mata nuni da naman, take kuwa ta fara ci da hannu biyu, hadi da debo romon da hanunnta ta dinga sha, kura mata ido yayi yana mata kallon birgewa... sai daya gama more kallonta kana ya shiga gyaran dakin domin duk gajiyan daya debo baya jin ze iya zama haka cikin dakin, bayan ya gyara ko ina ya dawo hayyacinsa kana ya bude sif dinsa domin daukan kaya sawa saboda so yake yayi wanka ana daf da kiran magriba, jiyayi ta rungummesa ta baya tana goge idanunta abayansa, kallon hannunta dake rungume akirjinsa yayi yaga gaba daya ta shafa masa ruwan romo da mai hannunta farar rigarsa, saurin juyo da ita yayi yaga tana ta runtsa idanunta, da alama tasa yaji ne idon, sai kuma ta sake daukan hannun yajin tana murza idon dashi, kamo hannun yayi ya nufi toilet da ita cikin sauri, sabulu yasa ya fara wanke hannu kana yasa tattausan hannunsa ya shiga wanke kyakyawar fuskarta sai daya tabattar dacewa yaji ya fita, bayan ta bude ido ta kalli kanta amadubin dake gaban sink, sai ta kuma juyawa ta kalle shi hadi da kyakyale dariya, kumatun ta yaja kana ya riko hannunta suka fito, direct kuwa ta nufi wurin sauran kazarta, cikin hanzari ya dauke ya shiga yagowa yana sanya mata a baki, haka ya dinga yi mata har ta cinye tas, hannunsa ta kamo ta sa harshenta ta shiga lashe hannun, kallonta kawai yake batare da ya hanata ba sai don kanta ta sakar masa hannun, a kwandon shara ya zubar da ledan kana ya shiga toilet, shower ya sakar wa kansa yayinda ya dafe bango da dukkanin hannayensa ruwan na dukan lafiyayyen farar fatarsa, yayinda tunanin yadda ze mallaki Abrar ke yawo azuciyarsa, yasani baya da matsalan komai se mummynsa yakuma rasa ta yadda ze bullowa al'amarin...
cikin toilet din ya sanja kaya kana ya busar da sumarsa da hand dryer ya fito, yana fitowa aka kwalla kiran sallah beyi wata wata ba ya bude kofar baya ya nufi masallaci dake cikin gidan, bayan ya dawo ya ganta kwance bacci ya dauketa, rigar nan ta tattare izuwa wajen cinyarta, take idanunsa suka gano masa kafarta da daya tafi daya kumburi, cikin sauri ya karasa gadon bayan ya gyara mata rigan, kafafun ya dora kan cinyarsa, ya kuwa ga daya yafi daya kumburi nesa ba kusa ba, dafe kai yayi cikin tausayinta yanzu dama kafarta tayi targade take tsalle tsalle hadi da gudu? shin bata jin zafi ya tambayi kansa, shi kam be taba lura ba domin rigar daman har kasan kafarta ta rufe gashi bata yi wata alama daze sa ya ankara ba, yama rasa yaushe taji wanna targaden? Gwada taba kafar yayi yaga bata motsa, sake tabawa da dan karfi yayi domin so yake ya gyara mata, takuwa farka ta sakar masa ihu hadi da kai masa bugu, be hanata ba har ta gaji ta daina, hadi da takurewa waje daya,
"am so sorry" ya fada yana kallonta, mutuniyar ko kallon gefensa bata yi ba.

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now