11

171 3 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓

Written by noor Eemaan
wattpad@NoorEemaan

Page21-22
Amma dauriya irin tasa ya sa ko afuska bai nuna ba, hannun mummy  ya daura afuskarsa ba tare da yace komai ba tsahon lokaci, mummy kuwa sanin halin danta data yi  yasa bata furta komai ba sai dan kansa ya sauke hannunsa hadi da ware idanunsa dasuka yi jaa tashi daya, cikin husky voice dinsa yace "mom zamuyi maganan but not now please" ba musu ta jinjina masa kai alamun amincewa
"tnx" yace yana barin wurin cikin sauri...

kan gadonsa ya haye ya fada cikin duniyar tunanin gaba daya tunaninsa ya tsaya cak ya rasa meyake ji gami da abrar "tausayi ne  ko so" domin shi bai taba soyayya ba bare ya sani, abu daya yasani yana jin abu mai girma da baki bazai iya furtawa  a kanta ba, tabass yana bukatar mai bashi wanna amsar gwauron numfashi ya saki hadi da lumshe idanunsa ahankali kamar wanda aka wa dole  yace "please come back to me decent one"....

bayan sati biyu wanda yayi daidai da dawowar amal daga serving, mummy taji shiru aaban bai ce mata komai ba ranar wata lahadi da misalin karfe sha daya na safe mummy ta nufi dakin shi domin jin ta  bakin sa, knocking mummy tayi taji shiru hakan yasa ta tura kofar ta shige yana kwance flat akan gado yayinda ya rufe fuskarsa da rigar abrar nan dai data yayyage komai daya faru aranar daya fara ganinta sai zuwan masa kwakwalwarsa take daki-daki, cikin mamaki mummy ke binshi da kallo ganin rigar mace a fuskarsa yaye rigar tayi wanda yayi daidai ta wata katuwar ajiyar zuciya daya saki ahankali ya ware sexy eyes dinsa dabasu fiye girma ba ya sauke su kan mummy....

kara mayarwa yayi ya rufe, girgiza kai mummy tayi domin halin aaban sai shi, bubbuga kafansa tayi tace "tashi muyi magana" ba musu ya mike ya zauna still idanunsa arufe a maimakon maganar daya kawato sai tace
"son rigar wace wanna!!!"
sai a lokacin ya bude idanunsa ya kurawa rigar ido na yan seconds kana ya ware jan  labbansa yace
"rigar ta ce"
"ita wa?" mummy ta tafada cikin mamaki

"mum i don't know her"
yafada muryansa nason fito da rauninsa sai dai dakakkiyar zuciya irin tasa yasa baza'a fahimci hakan ba.

"are you serious ? wait! are you sure you are ok son?"

da dariya na cikin dabi'arsa da babu abunda zai hana shi yi, domin ya fahimci mummy na tunanin ko baya cikin nutsuwa da hankalinsa ne...

"mum am absoutely fine"

"no you are not son! da lafiyar ka kalau da baza ka ce min baka san mamallakiyar wanna rigar ta hannuna ba, ta fada tana daga rigar, toh ya aka yi kasamu rigar"?

kamar bazai yi magana ba sai kuma yace
"rigar wata patient dina ce, na kasa mantawa da ita" ya fada yana sake sauke wani ajiyar zuciyan.

"son ka fada soyaaya" mummy ta fada
cikin tabacci.

abunda yake son sanin kenan dan haka cikin sauri ya riko hannunta yace "mum are you sure? you mean i have fall in love?"

cikin murmushi mummy ta gyada kai hadi da cewa "son kasan ni mahaifiyar ka ce ko?  baya ga haka na baka shekaru masu yawa, kasan kuma dole na fika exprience akan rayuwar duniya, so tell me ya aka yi ka sameta? ni babarka ce kayi sharing damuwarka dani, kuma nasan cewa baka da waccce ta fini aduniyar nan right?"

jinjina kai yayi alamun "eh"

"good boy, so tell me who's the lucky girl?"

hannunta ya rigo yafara tunanin yadda zai yi dogon magana domin idan akwai abunda ke bashi wahala toh dogon magana ne "mum i dont no how to explain,.... but na hadu da ita ne aranar da na yi night duty na kuma dawo da safe nayi wanka na koma har kika bani breakfast kin tuna?
jinjina kai mummy tayi alamun
ta tuna nan ya shi bata labarin komai.....

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now