24

165 11 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓

Written by Noor Eemaan

EID MUBARAK TO YOU MY FANS, ALLAH YA MAIMAITA MANA💫✨🌝 💞

page 47-48

haka ya cigaba da zama a wajen idanun sa kuri kan kofar operation din, babu abunda ke tashin sa sai Allah...

yana cikin wanna halin yaji wayar sa na ringing, a hankali ya zaro ta cikin aljihun sa  ba tare da ya duba wanda ya ke kiran ba ya kara wayar a kunne, "Son how are you?" jin saukar muryan Mummy a kunnuwan sa ya sa shi lumshe ido kana ya ware su a hankali... "Am fine" ya amsa a kasalance

"No you are not son, gayamin menene"...
Ajiyar zuciya ya sauke yace "Mum an shigar da decent one dakin operation".

Shiru mummy tayi yayinda ta kasa tantance halin da take, a wani bangaren kuma ta na matuk'ar mamakin tsananin son da danta ke yi wa Abrar di'n... "ka kwantar da hankalinka son, everything will be fine, Allah ya bata sa'a" Mummy tace tana katse wayar...
bai iya amsawa a fili ba har ta katse wayar.

Bayan awannin takwas doctor Irfan ya fito tare da abokan aikin sa, cikin wani irin zafin nama ya kara sa wajen doctor, cikin turanci yace;
"doctor Irfan how is my wife? As she regain her memory?"...

murmushi doctor Irfan ya saki ganin yadda Aaban ya rude gaba da ya, ya kuma yi mamaki hakan domin bai yi tunanin Aaban zai so wata mace so soon har ta kai ga aure ba, domin a lokacin da suke school shi shaida ne akan cewa mata basa gabansa, duk da suna kawo kansu gareshi,  kafadan sa ya dafa yace "please calm down doctor Aaban, ka karfafa jikin ka da ma zuciyarka, sai kace ba jarumin doctor'n dana sani ba".

"Irfan you won't understand, she's my life, inaso in ganta tana rayuwar farinciki kamar kowa"...

"In sha Allah  komai zai zama normal" yanzu muje office dina in maka bayani ya fad'a yana kamo hannunsa, ba musu Aaban ya bishi....

bayan sun zauna, yace "Aaban you have to calm down sanan zaka fahimci bayanin da zan maka. jinjina kai yayi alamun "toh" 

doctor Irfan ya hade hannuwansa cikin na juna kana ya fara cewa "the opperation went sucessful, duk da mun sha wuya matuka kafin komai ya daidaita, yanzu jiran farkawan ta zamu yi, zata kai awa biyar zuwa shida kafin ta tashi, muna fata  ta dawo da memory'n ta"...

Ajiyar zuciya mai karfi ya saki kana yace "Thank you so much Irfan"

hannu Doctor Irfan ya mika masa suka yi masabaha yace " don't mentioned Doctor Aaban, you deserve it" domin baya taba manta taimakon Aaban gare shi ba, lokacin suna makaranta... haka dai suka cigaba da taba hira wanda yawanci Irfan din ne ke magana.

*SOME HOURS LATER*
cikin mutuwar jiki yake bude kofar dakin hutun da aka ma yar da ita wanda ya kasance na zallan glass ne, yayinda yake jin zuciyarsa na bugawa so fast, amma mutum ba zai fuskanci haka ba saboda jarumtar sa, tun daga nesa ya kura mata ido, fuskarta tayi fayau yayinda fatar ta ke fitar da sheki hadi da haske na musamman da ya kara mata kyau ainun...

bakin gadon ya zauna ya lalubo tattausan hannunta cikin na sa, kana ya bawa hannunta kyakyawan sumbata, ya kai awa daya a haka bata farka ba, sosai ya fada duniyar tunani, domin baya so ta nuna bata san shi ba idan ta farka domin baya tunanin zai jure hakan.

"AMMI NA!!!"..... Abrar ta kira sunan Ammi da mugun karfi, da ya shi dago kansa cikin sauri yayin da gaban sa ya bada ras!

"decent one kin tashi, ya jikin ki? ina yake miki ciwo yanzu? please ki mun magana" ya fada a rude fuskar sa cike da damuwa.

kallonta ta kai inda ta ji wani unique voice, kura masa ido tayi tana tunanin waye wanna hadadd'en saurayin? me yake yi tare da ita? me kuma take yi a hospital? amma ta kasa tuna komai, abu daya ta tuno, gudunta daga gidan mijin ammin ta, da haduwarta da wani mutumi da ko fuskar sa bata sani ba ta dai tasan ta nemi taimakonsa...

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now