23

143 4 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓

written by Noor Eemaan

masoyan mijin ammina ne sila ina matukar godiya da soyaayar da kuke nunawa books dina, na ga texts dinku bila adadin a group dina da ma sauran groups a bisa rashin jina da baku yi ba jiya, tnx all,  here is your favorite book, so happy reading😊

Page 45-46

Ya dauki tsawon mintuna biyar a haka ba tare da ya ko sumbace ta ba, yayinda kyya wawan idanunsu ke cikin na juna basa ko kiftawa.... A hankali ya zare bakinsa ganin mood dinsa ya fara canzawa, kanta ya kwantar kan cinyar sa hadi da bubbuga bayanta, luf Abrar tayi bata ko motsin kirki, bata dauki lokaci mai tsayi ba bacci ya dauketa, jin ta daina motsi ya sa shi leka fuskarta... Ajiyar zuciya ya sauke domin fatan sa kenan tasamu bacci, lumshe idonunsa yayi tunanin yadda aikin zai kasance fall zujiyarsa.

*SYRIA*
Cikin tafiyarsa ta burgewa yake taka matattakalan benen jirgin, yayinda Abrar ke kwance har yanzu tana bacci kan faffadar kafadansa... Taxi ya tsayar ya gaya masa ya kai kaisu hotel mafi kusa da airport din,  babu jimawa suka isa hada'dden hotel di'n,... Aaban ya biya mai taxi hakkin sa kana ya kara daukan Abrar a kafadansa, cikin sauri ma'aikatan hotel din suka dauki jakarsa, kudin yan Awannin da za su yi ya biya kana ya karbi mukullin dakin... Kwantar da ita yayi kan gado ya shiga toilet domin yin wanka domin ya warware gajiyan jikinsa, ya dauki tsahon mintuna 30 yana wankan kana ya fito daure da towel a jikinsa, yayinda ruwa ke diga a kan hair dinsa.
singlet da boxer ya saka, kallon Abrar yayi ya ga tana baccin har yanzu, kayanta ya shiga cire mata a hankali kana ya daga ta cak zuwa toilet...

Cikin jacuzzi ya sanyata a hankali, bata rai tayi cikin baccin a sakamakon ruwan daya ratsa jikinta, murmushin shaukin sonta ne ya subuce masa.... Domin  yadda tayi ba karamin kyau ta kara masa ba, ruwa ya debo a tafin a hannun sa ya shafa mata... A hankali ta fara bude idanunta dake cike da bacci har yanzu, wani kyau ya ga idanunta sun kara masa, labban sa ya dora akan nata ya bata light kiss, fuskarta ya fara wankewa, mistakely shower gel di'n ya shige idonta, kara ta saki kana ta shiga goge fuskarta a singlet din sa, gaba daya ya rude ganin ta cikin wanna halin, fuskarta ya kamo ya shiga wanke mata cikin sauri- sauri sai da ya tabattar sabulun ya fita kana ya shiga wanke mata sauran jikinta, a towel ya nado ta kana suka fita, lotion mai kamshin gaske ya shafa mata kana ya sanya mata blue jeans da riga fara, full, long hair dinta ya taje mata, yayi mata parking da farin ribbon...

Kamo fuskar ta yayi yana kallon baiwar kyau da Allah yayi mata "so cute" yace mata hadi da kamo kumatun ta, itama kumatun sa ta kamo  tace "so cute" murmushi yasaki kana ya kira hotel din akan su kawo abinci, babu bata lokaci suka fara knocking, bude kofar yayi ya karbi abincin... kan cinyarsa ya dora ta suka shiga cin abincin, duk da fiye da rabin  abincin Abrar ce ta cinye...( acici lolz)

Bayan sun gama ya fita hadi da rufe Abrar a dakin, wani flight yaje yayi booking wanda ya samu jirgin da zai tashi nan da awa uku zuwa India. Bayan ya koma ya tarar da Abrar kwance shiru ta kura wa waje daya ido, jikinsa ya jingina da kofa, yana binta da kallon tausayi da matsanancin sonta,  a hankali ya tako zuwa gareta hadi da Sanya fuskar ta cikin tafin hannunsa yace "decent one please ki daina tunani is not good for your health ok" kallonshi tayi kawai take, sai kuma tasa dariya mai tafe da kuka alamun ciwonta ya tashi, cikin rashin jin dadi ya rungumeta, idanunsa a lumshe yana bubbuga bayanta alamun rarrashi....

* MUMBAI INDIA*
Bayan sun sauka india a birnin mumbai, hotel ya sake kama musu, washegari da safe suka nufi babban hospital din mai suna "CITY HOSPITAL" babu bata lokaci suka gana da babban doctor kwakwalwan mai suna "IRFAN WAJEED KAPOOR" wanda tare suka yi karatu da Aaban din a nan India, kuma tun a nigeria suka gama magana da Aaban akan ciwon ta...

Bayan duk sun sake yi mata gwaje-gwajen daya dace, kana suka sa ranar yin aikin jibi, wanda aikin nada hadarin gaske, kila ta dawo da memory'n ta ko kuma a samu a kasin haka domin ciwonta ya zama chronic sosai,  a hakan ma dan tana samun kulawa ne....

Jiki Aaban ya yi sanyi haka suka bar asibitin, yana fatan a dace, wuraren shakatawa ya kai ta irin daban-daban, sosai ta dinga yin shirmanta yana biye mata, wanda hakan ya dan debe masa damuwar da yake ciki...

Daga karshe ya kaita  inda ake siyar dasu snacks a bakin hanya kuma sosai taci... yana cikin biyan mai snack's din kawai ya ga tasa gudu tana raba'wa ta tsakanin motoci, gabansa ne ya bada dam! Bai san nawa ya biya mai snacks din ba, haka ya shiga binta da zafin nama, gaba daya ya neme ta ya kara sa... Hankali tashi ya shiga kotsawa ta tsakanin motocin hadi da kwala kiran sunanta... can ya hangonta tsallaken titi tana cigaba da kuka, shima tsallakawan yayi, ya kara gudun domin ya cin mata...

hannunta yayi nasaran damkewa kana ya riko ta gaba daya zuwa jikinsa yana sauke wata katuwar ajiyar zuciya hadi da lumshe idonsa...
"bazan juri rasa ki a karo na biyu ba, please karki sake haka decent one". Ya fada yana sake kamkameta a jikinsa, Abrar kuwa dariyar ta kawai take hadi da ajiyar zuciyan gudun data tika, taxi ya tsayar suna koma hotel dinsu....

*BAYAN KWANA DAYA*
Yau ya kasance ranar daza'a yiwa Abrar aiki, sosai Aaban ke cikin wani hali na matsanancin damuwa, sai dai kasancewar sa namijin gaske yasa kai tsaye bazaka fahimci hakan ba...

bayan sun shiryata cikin uniform mai kalan blue, suka nufi dakin Operation din da ita, cikin sauri ya kara sa gareta hadi da riko hannunta daya, yayinda ya dora dayan a kan fuskar shi yace "wifffy... Allah ya bada sa'a, I know zaki dawo da memory'n ki domin ke jaruma ce, I love you" yarasa hadi da bata hot kiss a goshi...

turata ma'aikatan hospital din suka shiga yi zuwa dakin operation, yayinda ya ke jiyo dariyar ta dake tashi sosai hadi da kuka... da baya da koma ya zauna a kujera, sai a lokacin wani tunani ya zo brain dinsa, shin idan ta dawo dai dai zata gane shi? Shin zata karbi shi a matsayin mijinta?  Shin ya zata ji idan taji labarin auren dake kanta? Gaba daya kansa ya kulle, kwantaccen sumar sa ya hargitsa yana fadin "ya Allah"....

ban yi editing ba, saboda ban da time kuyi hkr, much love my fans😘.

SHARE✔
VOTE✔
COMMENT✔
EDIT❌

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now