13

160 8 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓

written by noorEemaan

page25-26

yayinda zuciyarsa yasake wata mugun bugawa da akan mace daya kadai take wanna bugun wato abrar, ahankali kalamanta suka sake amsa kuwwa akunnensa take tunanin abrar da yanda ya ganta yashe kofar gate din hospital dinsa ya dawo masa... kallonta yayi yaga gashin ta mai uban yawa yarufe dukkanin fuskarta wanda hakan ya hanashi ganin fuskarta, har ya sa hannu domin janye gashin, ko me ya tuno sai ya janye hannunsa, daga ta cak yayi ya dora ta a faffadan kirjinsa hadi da shigar da ita cikin motar domin baya jin ze iya barinta awurin, saboda idan abrar dinshi e awanna halin wani yaki taimaka mata bazai taba jin dadi ba, duk da bai san wacece ita ba amma hakan nan yaji zai iya taimakonta da dukkanin iyawarsa...

aback seat ya shimfudeta kana ya shiga bangaren driving ya nufi gidansu, domin baya jin zai iya komawa hospital saboda dare yayi nisa sosai, tunda yana da kayan aiki agida zai yi mata komai daya dace domin ya fahimci ta suma ne...

isar sa gida kuwa ya tarar da mummy zaune a falo tana jiran dawowarsa domin tun yana mata magana har ya hakura ya saba, domin kullum sai ta jira dawowarsa ta tabbatar ya shigo take iya bacci, kallon kauna yayi wa mahaifiyarsa kana ya karaso hadi da bata sumbata agoshi, cikin tausayin sa mummy ta shafa kansa hadi da cewa

"aaban baka gajiyane da aikin daran nan? nifa abun ya fara damuwa domin, da kana da iyali da bazaka yi wanna night duty ba, jiran daddyn ku kawai nake ya dawo domin yaje gidansu abrar kawar hanan nema maka aurenta, kadinga hutawa son haba dan Allah"

jinjina kai yayi alamun "toh" duk da cewa bayason mummy na kira masa wanna kawar hanan amatsayin matar dazai aura, duk da baya jin ciwon sosai idan mummy ta fadi hakan wanda shi kanshi bai san dalili ba, amma yafison "decent one" (kamilaliyya) wacce ya hadu da ita adaren da bazai taba mantawa da ita, ya kuma zabi kiranta da decent one domin ita din daban take da sauran mata aduniyar shi duk da kaddara data fada mata amma duk wani mai sanin ya kamata idan yaganta ayanda aka mata fyaden nan zai san bada amincewarta aka yi ba, dafe saitin zuciyarsa yayi yayinda wani matsanin kaunarta ke ratsa bango da tsokar jikinsa.... har ya fara taka benen domin zuwa side dinsa sai kuma ya tsaya cak hadi da dafa kansa
"opphs, mummy na manta ina tareda patient (mara lafiya) dana hadu da ita ahanyar dawowa na"

"salati mummy tasaki tace "yanzu son kana tareda patient amma kuma baka bata taimakon gaggawa ba, tukunna ma meyasa baka kaita hospital ba?"

"mum" yafada amarairace kana yace"saboda dare yayi shiyasa ban koma asibiti ba"...

"so where is she now?" mummy ta tambayeshi.
"tana cikin motana" ya bata amsa ataikace.
"muje toh, kada wani abu yasamu yar mutane"
cikin tafiyarsa dake nuna lafiyayye namiji ne shi ya mara mata baya, tana kwance kamar yanda ya ajiyeta, sake daukarta yayi ya dora ta akirjinsa yayinda mummy na biye dasu, duk da tazo ganin fuskarta amma gashinta ya rufe domin babban mainson dinsu awadace yake da fitilu kamar rana...

ganin yana kokarin kwantar da ita akan kujeran falon yasa mummy saurin cewa "son ka kaita dakinka mana, ina tunanin kayan aikin na dakinka, yakamata ka hanzarta tunda tana bukatar taimakon gaggawa, nidai Allah ya tsaremu yasa mutum ce, domin duniya tazama abun tsoro yanzu" mummy ta fada tana daga idanunta sama alamun roko ga rabbu sammawati.

kalaman mummy na karshe yaso sashi dariya matuka, saidai shi ba mai yawan dariya bane, "babu komai in sha Allah mum, just relax"
yafada domin kwantar mata da hankali,
"hmmm ameen son" mummy tasaki ajiyar zuciya.

tamkar babu komai rugunme a hannunsa ya shiga taka benen cikin sauri, bayan shigarsa dakin ya kwantar da ita akan gadonsa yayinda ya shiga bata taimakon gaggawa... bayan ya gama yi mata abunda yadace, ya koma kan sofa ya zauna yana jin sa atakure domin ya saba rayuwa shi kadai a dakin, wanka yayi a bathroom dinsa hadi da sanja kayan jikinsa zuciya jallabiyan maza maroon color duk a toilet yasanya kana ya fito ya kwanta kan sofa ya dan samu bacci kafin akira asuba...

ana kiran sallah farko ya bude idanunsa dake ciki da gajiya, ya sauke su kan abrar dake kwance kamar yadda ya barta, yayinda har yanzu fuskarta ke a rufe da gashinta, banda kirjinta daya ga yana bugu da sauri sauri dazai ce mataciyya ce saboda yanda take kwance ko yatsarta bata motsawa...

ahankali ya sauke kyakyawan kafafunsa kasa ya nufi toilet yayi wanka hadi da daura alwala ya fito, nafiloli yayi kana ya nufi massalaci. Sai karfe shida da rabi ya bar masallaci dake cikin mainson din nasu ya nufo cikin aihinin gidan...

workers ya gani to ko ina suna ta aikinsu, yayinda suke ga gaishe shi cikin girmamawa, part dinsa ya koma still kan sofan ya koma ya kwanta, "ka...ka taimakeni kada ya sake samun galaba akaina, domin idan hakan ya faru zan mutu!!!" ya tuno kalaman abrar, ko waye yake biyayarta? ya aiyana aransa yana sake kallonta, dan tabe bakinsa yayi kana ya lumshe idanunsa bacci yayi awan gaba dashi...

takwas dot yafarka ya bude wardrobe dinsa yana bata rai, shi ala dole yana ataruke komai yanzu a toilet zai dinga yi, kananun kaya masu kyau da tsada ya dauka, ya dau mintuna 30 kana ya fito tsaf dashi, direct part din mummy ya nufa gaba daya suna zaune kan dining table mummy, amal, hanan, tundaga nesa su duka ke kallonsa domin kaunar dasuke matukar yi masa saboda ya kasance tamkar sanyin idaniyansu ne, bayan ya ja kujera ya zauna yace "mum good morning"
"morning dan albarka mummy tace tana shafa sumar kanshi.
"ya aaban ina kwana"amal da hanan suka hada baki wurin fadin hakan, jinjina kai yayi alamun amsawa, sanin halinsa dasukayi yasa basu damu ba.
"son mezaka ci" mummy ta tambayesa.
"mum only black tea" ya amsa
"no son kahada da wani mana, ni har mamaki nake yanda baka jin abunci kuma baka ko ramewa" hanan da amal suka yi dariya kasa kasa, domin kada ya juyosu.
Dafe kansa yayi kana yace " da soyayyen kawai" girgiza kai mummy tayi ta zuba masa hadi dire masa gabansa.
"au son na manta ina patient dinka ta tashi kuwa"?
"noo mummy amma zata iya farkawa a kowani lokaci"... jinjina kai tayi alamun gamsuwa, yayinda amal da hanan suka kalli juna alamun tambaya, yana gama breakfast yayi sallamawa dasu ya nufi hospital...

suna ganin fitarsa amal tace"mummy wacce patient kike magana akai?"
ataikace mummy tayi musu bayani, har hanan tace zata je taganta mummy ta hanata hadi da cewa "kinsan yayanku bayason shishigi ko?"
"toh" tace kana ta fara kokarin kiran wayar ammi domin yau tayiwa abrar alkawarin zuwa, sai dai duk kiran datake yi ba'a dauka, jitayi ba dadi, gashi so take ta kara tambayan address din domin ta manta, fatan ta Allah yasa abrar na lafiya....

"AMMI"
kokarin riketa, domin matukar ya bari takai kasa komai ze iya faru da ita, sai lokaci ammi tafara dawowa nutsuwarta, idanunta kuri kan alhaji shettima tana masa kallon tsoro, kallon matsanincin mamaki, still hawaye na zuba idanunta, ashe abunda tilon yarta mafi soyuwa aduniyarta take fada gaskiya ne? ashe alhaji ke cutar da diyarta duk tsayin shekarun nan bata sani? ashe da gasken ne shi ya ketta mata haddi, yayi mata fyade bata sani ba? ita kuwa wacce irin uwa ce data kasa gane halin da diyarta take ciki? akan namiji, namijin ma mugu azzulumi ta banzantar da yarta, akan namijin karon farko arayuwa ta dau hannu ta mari yarta. me duniya zasu ce akanta? ya akayi takasa gano hakan sai a kurarren lokaci, take duk abubuwan da abrar ke gayamata hadi da canjin data dinga gani atare da ita ya shiga dawowa kwakwalwarta, haba shiyasa tun ganin farko da diyarta abrar tayi masa ta tsaneshi ashe shine silan rugujewar rayuwarta, take wani kuka ne ya kufce mata, kana tayi masa wani mugun hankada ta shiga dukanshi to ko ina tana cewa "mugu azzalumi sai na maka ka akotu, kotu ce zata raba mu da kai dan kaga bamu da kowa akasar nan shiyasa ka cutar da yata hankalin ka kwance, to kasani Allah ne gatanmu zaka ga yanda zaka wulakanta aduniya, natsaneka, tsana mafi muni, kuma basai gobe ba yanzu nakeson ka rubuta min takardan saki domin zama dakai gwara zama da bunsuru, alhaji shettima daya ji azaban duka ya riko hannunta duka biyun ya fara kokarin janta domin kaita dakinta, sai kokarin kwace hannunta take amma takasa domin karfin ba daya bane, gabadaya ya cike da gumi kamar wanda ruwan sama yayiwa duka, ko maganar ma ya kasa bai taba tunanin akwai abunda zai daga masa hankali haka ba, bai yi tunanin cewa haka komai zai gwabe masa har haka ba, dakin ya yi saurin cillata kana ya rufo dakin har da sa key ya rufe, bubbuga kofar ammi take tana cewa "ka bude mun mara imani inje in nemi yata " haka ta cigaba da cewa tana bubbuga kofar da dukkanin karfinta...
fita alhaji shettima yayi haraban gidan gate yagani arufe, hakan yasa shi sanin cewa bata nan ta fita ba, domin be taba kawowa aransa cewa zata iya taka lada ta dira ta kasa ba, ma'aikatan gidan ya tasa gaba daya yace a bazama nemo masa abrar ....

atayani share dan Allah da mazonsa🙏

comment and vote ✔

insha Allah zan fara turo muku littafina mai suna RAYUWAR FAHEEEMAH domin ba kowa yasanshi ba, kasancewar sai dana document dinsa sannan nayi sharing

noor Eemaan loves you all💖

https://chat.whatsapp.com/FEfWeTiufpk96my8yNBeaM

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now