6

200 9 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍇🍇

Written by noor Eemaan
wattpad@noorEemaan

Page11-12

cikin sauri sauri yake tafiya da ita yayinda abrar ke kwance a faffadan kirjinsa tamkar mataciyya, nurses dake duty suka yi saurin turo gadon nan na marasa lafiya, ko kallonsu be yi ba ya shiga office dinsa da ita, sororo nurses din nan suka yi suna kallonsa " ko dai kanwarsa?" daya cikinsu ta tambaya.

Wata daga cikinsu na shirin bada amsar suka ji ya bude kofar, fuskarsa a dinke tsaf yace akawo masa box din treatment yana fadin haka ya koma office  dinsa,  cikin sauri aka kawo masa, har nurse din ta nemi taimaka masa ya dakatar da ita, ba musu ta fice domin kaf ma'aikatan asibitin suna matukar girmama shi domin sosai yake musu kwarjini...

key ya murza ajikin kofar cikin tafiyarsa dake nuna shi din cikakken namiji ne mai ji  da kuruciya,  ya nufi dan gadon dake office dinsa ya yaye labulen daya rufe gadon domin babu wanda zai taba tunanin da mutum kwance aciki, kura mata idanu yayi tausayinta fal zuciyarsa be taba ganin rashin imani irin wanna ba yarinya yar karama akawa wanna mumunan aiki, shin yaushe za'a daina yiwa yara mata fyade? yaushe za'a daina keta musu haddin su, yaushe za'a daina wulakantasu? duk ya jerowa kansa wadannan tambayoyin aransa...

sanin cewa tana bukatar taimakon gaggawa yasa shi fara yaye doguwar jikinta sama  hadi da runtse idanunsa kana ahankali ya ware su awajen "damn it" ya fada yana buga gefen gadon da karfi, a akaro na farko bayan girmansa yaji hawaye masu dumi sun biyo kuncinsa, domin ba karamin ciwo taji ba jiyayi dazai ga wanda yayi wanna barnan da babu abunda ze hana shi farka shi gida biyu, cikin kwarewa yake aikinsa yayinda idanunsa sukayi wani ja tamkar garwashi, duk wanna dinki dayake yiwa abrar ko motsin bata yi domin zaka yi tunanin bata da rai a yanda take kwancen, bayan ya gama ya daura mata drip hadi da mata wasu allurori domin yaji jikinta da zafi alamun akwai zazzabi.....

hannu yasa akugu yana zagaye office dinsa hakan nan yaji wani radadi na domin sa azujiya, bacci da gajiyan dayake ji duk sun kaura a idanunsa, kan kujeran office dinsa ya dawo ya zauna yana mai daura kansa a table,   bayan wasu mintuna dayake tabaccin cewa ruwan ya rage ya mike ya cire mata, kallon saman rigarta yayi yaga ayage  tabaccin sunyi kokawa kenan? baya jin ze iya fita da ita dakin hutu da yaggegen rigar jikinta can tunanin wani riga daya siyo wa kanwarsa ya fado masa, wanda yake yawan mantawa baya kai mata gida locker ya bude ya dauko rigar hadi da warware ta rigar mai kalan sea green ne, sanya mata yayi hadi da janye na cikin daya yage kasa yalwataccen gashinta daya rufe mata fuska ya shiga tattare mata shi zuwa baya...

Har karfe biyar na asuba bata farka ba sai ya tafi masallaci yana hanyar dawowa ya lura da motarsa abakin gate, dafe kansa yayi domin shaf ya manta, kuma ikon Allah key din na jiki motar ayanda ya bari, rufe motar yayi ya nufi cikin asibitin yana fatan ta farka...

Tana nan a kwance still tamkar gawa, kallonta yayi na yan mintuna kana ya dauke ta cak ya nufi dakin hutu da ita, bayan ya gyara mata kwanciya, yaji  knocking abakin kofa, runtse idanunsa yayi domin ahalin dayake ciki bayason takura  ahankali ya motsa bakinsa "come in" yace still be bude idon ba, wata nurse ce ta shigo mai matsakaicin tsayi t "sir an kawo wani mara lafiya yana ta bleeding" ta fada cikin damuwa tashin hankali hadi da satan kallon abrar dake kwance ya kai kusan minti biyar bai bude ido ba bai kuma bata amsa ba, har  ta cire rai da samun amsarsa taji yace " i will be there right away" cikin murna ta fita, duk da tasan cewa baya duty, amma ya  amince, tabass kowa asibitin ya shaide sa yana da wanna halin kwaran matukar ya ga mara koda baya duty ya kan bashi taimakon gaggawa unlike sauran doctors din, kadai barshi baya shiga harkan kowa haka kuma baya fara'a, sannan tana mamakin wanna mara lafiya wacece da har ta samu matsayin  da doctor da kansa ke jinyar ta da wanna tunanin ta fita...

bayan yaje ya duba mara lafiya ya dawo ya tarar still bata farka ba, gashi bakwai har da minti arba'in yana da bukatar yayi wanka, zai je ya dawo domin yana saka rai kafin ya dawo ta farka, zoben hannunsa ya kalla baya mantawa sanna dayace germany wani course ya siyowa kanwarsa ita, saidai yayi mata kadan yatsan ta na kusa da karami ya kuma yi mata yawa a karami yatsanta, shima a iya saman yatsan ya tsaya masa, yana matukar son zoben sannan  zallan na diamond ne har  daukan ido yake, cirewa yayi daga yatsan shi da kyar kana ya kamo hannunta ya zira mata a yatsanta  nakusa da karami yatsan ta kuma yayi cib a kyakyawan hannunta, shi kanshi bai san dalilin sa nayin hakan ba kawai ya tsinci kansa da aikata hakan ne, gashinta mai uban yawa ya shafa hadi furta "get well soon" cikin sauri ya fita be bar asibitin ba sai da ya yi  kiran nurse dazata kula da ita kafin ya dawo...

"hello kwaro kaji abunda na gaya maka ko koda wasa kada ka bari asamu matsala ku kawo min ita ko ta wani hali"

"an gama alhaji" kwaro ya fada
"yawwa yi sauri ina gida daka daukota ka min waya sai mu hadu" kit ya kashe wayar yana kallon ammi dake shararan baccinta har yanzu ko motsi batayi ba, gumi ya share yana fatan kada a samu matsala, lashe labbansa yayi tuno da moment din daran jiya...

"kin zama tawa domin bana jin zan barki ki kufce min, dole in cigaba da lasar zuman ki abrar daddy's girl" ya fada abayyane yana dariyan samun nasara...

kwaro tare da manu suka shiga asibitin basu wani sha wahala ba suka gano dakin datake, nurse mai kula da abrar na zaune kusa da gadon taji kawai an bude kofar tana shirin magana kawai taji manu ya fito da wata sharbebiyyar wuka daga kasan booth din kafarsa sai kyalli take" kina magana zan falle kanki" manu ya fada yana muzurai, hannu tasa ta rufe bakinta tana hawaye, cikin sauri kwaro ya dauke ta ya fita da ita yayinda manu ya cigaba da tsareta da wuka kasancewar safiya ce babu wasu mutane hakan yasa babu wanda yasan halin da'ake ciki, bayan kamar minti 7da fitar kwaro manu ya shaka mata wani kyalle ahacinta take jikinta ya saki ta fadi kasa ko juyowa be ba ya fita cikin sauri ya tarar da kwaro cikin motar suka bar asibitin cikin sauri motarsa su kwaro na fita na doctorn nan nashigowa, domin ko breakfast yakasa yi babu yanda mummynsa bata yi da shi ba yaki, karshe dai sai a basket ta bashi tace lallai yatafi dashi...

bayan ya daidaita  parking motarsa ya fito hadi da daukan basket din abincin ya nufi cikin asibitin ko office dinsa bai je ba ya nufi dakin da abrar ke kwance... wani abu mai kama da tsoro na neman dirar masa adalilin mugun ganin dayayi, sadai sam baya son wanna tsoron  ya samu muhalli azyciyarsa domin jin tsoro baya daga ciki dabi'ar sa, gadon da abrar ke kwance wayam bata nan, ga nurse hannatu a kwance a kasan tiles cikin fitar hayyaci...

cikin sauri ya shiga bata  taimakon gaggawa, domin ita kadai ce zata basa amsar dayake son sani, bayan awa daya ta farka tana ta sakin atishawa,  dago kan daza tayi taga idanun doctor nan sunyi jajur yana yana mata wani kallo, gabanta ya fadi sai ta fashe da kuka domin batasan yaza ta ce masa ba, runtse idanunsa yayi kana ya waresu ahankali " a enough!!!" yace cikin tsawan da bai san ya iya ba.

take jikin hannatu ya fara rawa " ina take? i said where is she?" ya fada yana nuna gadon ga fuskarnan ba alamun wasa" wa...su...ne suka......... nan ta fara bashi labarin komai cikin rawar murya.

" ya ilahi fattaqun" ya fada yana hargitsa kwataccen suman kanshi, be kara ce mata komai ba ya fita daga dakin, office dinsa ya nufa ya rufe kansa ya aciki yama rasa yanayin da zai fusalta  kanshi aciki...

"good job kwaro zaku ji alert dana je gida" alhaji shettima ya fada yana kallon abrar dake kwance abayan motarsa.
"Allah ya biya oga godiya muke" kwaro da manu suka hada baki wurin fadin haka....

ta kofar baya alhaji shettima ya shiga da abrar ya mayar da ita dakinta ya kwantar hadi da komawa dakinsa wanka yayi ya fito, ya ga ammi zaune kan gado hannunta dafe da kanta, kamar gaske yace " hajiyata sannu kin tashi?" da kallo take binshi ba tare da ta amsa ba jiyayi gabansa yabada ras! "ko dai tasan abunda ya faru ne?.... wata zujiyar tace ai bazata taba sani ba" domin an bashi tabaccin matukar mutum ya sha maganin nan toh sai ya dau awannin masu yawa yana bacci ba tare da yasan inda kansa yake ba.

"alhaji kalli tara saura banyi sallah ba, gaskiya bazan sake shan wanna maganin ba" ajiyar zuciya yasaki ganin ba abunda yake tunani bane...
"Toh shikenan hajiyata an gama duk yanda kikeso haka za'a yi"  bara nayi sallah'n na dubo jikin abrar ta nufi toilet cikin sauri yana ganin shigar ta yasake zuba wanna maganin cikin shayin daya sa aka hada domin baya jin ze iya barinta taga abrar awanna halin da take ciki....

YANZU LABARIN YA SOMA👌AM SURE YOU GUYS WILL ABSOUTELY LOVE THE HEART TOUCHING STORY JUST KEEP ON FOLLOWING MY PEN.

NOOR LOVES YOU ALL💞

PLS SHARE✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌
https://chat.whatsapp.com/FEfWeTiufpk96my8yNBeaM

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now