29

156 7 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓

Written by NoorEemaan

Wanna page din sadaukarwa ne ga sisters dina much love (bloodlines)❤

Page57-58

(Not edited)

Sosai dariya ke cin sa amma bai yi ba, kasancewar dariya ba dabi'ar ba ce, bai taba tunanin cewa ita din matsoraciya bace sai yau...

Wani tsallen daya dara na baya yayi, wani mugun ihu ta saki, cikin kuka sosai tace "pure heart na fasa cin naman, ka bari kada na mutu ban hadu da Ammina ba"... Ta kai karshen maganar tana sake rungume shi da kyau.

Cak! Ya tsaya, domin kalamanta sun yi matukar ta ba zuciyar sa, domin ba hakan bane manufar sa, yayi hakan ne domin sanyata farincikin bai yi tunanin cewa hakan zai tsoratata balle har ta furta wanna kalami mai taba zuciya ba...

Cikin wani salo ya dawo da ita gabansa sai ya zamana suna fuskantar juna, da hannu daya ya shiga shafa fuskar ta ya ce" Ana aseef wifffy (kiyi haku'ri wifffy) ban yi da niyyar sa ki kuka ba, na yi hakan domin sanya ki farinciki, am so sorry ok?"

Cikin tsoron da bai gama tsakin ta ba  hadi da tausayin sa tace "ni ba ka min komai ba fa, kawai ina tsoron mashin ne, kayi haku'ri ka jiiii?" Ta ja karshen maganar.

Murmushi mai taushi ya sakar mata hadi da bata Sumba a kumatun ta, bayan shi ya sake mayar da ita, kana ya tayar da mashin  di'n ya shiga Jan su a hankali, duk da haka matsoraciyar sai da ta kamkame shi....

Hada'dden wurin siyar da nama irin daban daban suka nufa, kowa na harkar gabansa yayin da mutane ke cike a wajen makil tamkar ba dare baa, suna zama babu dadewa waiter ya zo da menu, pappersoup yayi mata ticking da table water, yayin da ya yi wa kansa ordering only soft drink.

Babu jimawa aka kawo musu, tun kafin Abrar ta fara ci take hadiyan yawu, duk da uban kunyan da ke dawainiyya  da ita ganin jama'a hakan bai hanata fara shan romon naman ba, domin ta ga kowa harkan gaban sa yake...

Da cokali ta fara cin naman, ganin hakan bai mata ba ta ajiye spoon din hadi da sanya dogayen yatsunta ta fara gutsiro naman,... Aaban hade hannunsa yayi cikin na juna yana bin duk wani motsinta da kallo, kallo na zallan so, bai yi tsanmani  ba yaji romon naman ya fallasa a kan farar rigarsa, sakamakon wani kyakyyawan ja da tayi wa naman... Cak ta tsaya da cin naman yayin da ta kwabe fuska  cikin rashin jin dadi hadi da turo bakinta tace "pure heart am so..."

"Shhhh" ya ce yana kallon fuskar ta yayinda murmushi ke kan fuskar sa har yanzu, romon daya dan bata gefen bakin ta yasa hannunsa ya fara goge mata hadi da cewa "you dont have to say sorry decent one, domin ina son duk wani abu da kike yi yanzu, i enjoy looking at you like this..." Ya fada idanunsa cikin nata.

Murmushi ta sakar masa yayin da kwallan  suka cika idanunta, kwallan farincikin samun gwarzon namiji daya tamkar da dubu, mai son farincikin ta.

"I love you" tace a kunya ce.

"I so much love you too, with all my heart" kana yace "no more talk, cinye naman ki ok?"

Jinjina masa Kai tayi, murmushi kan fuskar ta  cigaba da cin naman ta, bayan ta cinye duka domin ko daya bata bari ba, tambayar ta yayi a karo mata ta ce a'a ta koshi, bill dinsu ya biya suka bar wajen... A hankali yake driving lifan din, yayinda suke hirar su ta soyaayya har suka isa gida....

" BAYAN KWANA BIYUI"

Bayan duk sun gama breakfast, gaba daya duk sun dawo falo suna hira, Hanan sai tsokanar Abrar take, amma ta kasa mayar mata saboda kunyar su mummy. "Hanan ki kiyaye ni fa, daughter dawo nan kusa dani ki zauna" Mummy tace tana yiwa Hanan hararan wasa, a kunya ce Abrar ta dawo kusa da Mummy ta shige jikinta, tana yi wa Hanan kwalo a fakaice...
Kallon so da birgewa Aaban ke binta da shi, yana farincikin yadda Mummy ta dauke ta a matsayin y'a da suruka a yanzu.

Wayar Mummy ce ta fara ringing, murmushi dauke kan fuskar ta ta daga kiran sakamakon sunan Amal da ta gani a rubuce kan screen di'n wayarta, "lafiya Amal na ji muryar ki haka?" Daga bangaren Amal kuwa sanar da Mummy tayi cewa mahaifin Adam ya samu hatsari yau kwana biyu, salati Mummy tayi kana ta shiga fada kan rashin gaya musu da Amal bata yi ba tun ranar da abin ya faru ba, haku'ri ta bawa Mummy hadi da bata uzurin cewa bata da nustuwa shiyasa bata sanar musu da wuri ba....

"Toh shikenan, muna nan zuwa, wani asibiti kuke?"

"Ai muna gidansu Adam, domin baban yace ba ya son zaman asibiti likita ke zuwa safe, rana, dare duba shi" ta karasa cikin sanyi murya da alama basu shirya da Adam din ta har yanzu ba..

"Allah ya tsare gaba"

Da " ameen" Amal ta amsa tana katse wayar...

"Mummyn'su meke faruwa ne?"

ajiyar zuciya Mummy tayi kana ta sanar da shi, jajantawa yayi kana ya umarce su dasu shirya domin zuwa duba majinyanci.

Kasa da awa daya duk suka shirya tsaf kana suka dau hanyar zuwa gidan su Adam, tun a hanya zuwa gidan gaban Abrar ke faduwa Wanda bata san dalili ba...

Bangaren Amal kuwa, a sanyaye ta sauke wayar daga kunnen ta, tana kokarin komawa dakin da aka kwantar da baba, domin wayar da zata yi ya sanya ta fitowa
daman, Kicibis suka yi da Adam dake kokarin fitowa, dauke kai yayi tamkar bai ganta ba, Wanda hakan ya sanya ta fito da kwalla "sweet Adam" ta kira shi, "lafiya" yace ba tare da ya juyo ba, ta baya ta rungume shi tace "ka sausauta min wanna hukunci ya yi min tsauri, na tuba" ta karasa tana sakin kuka...

Kamar kukan bai dameshi ba, haka ya zareta daga jikinsa ya bar wajen... Sai dai sosai kukan ta ke damun shi, yayi haka ne saboda gaba, tasan cewa dan Adam ba abun wulakantawa ba ne, a duk halin da yake ciki tunda Allah da kanshi ya karrama dan Adam, wane mutum yace zai wukalanta shi saboda wani dalili nasa Maras tushe....

Da kallo Amal ta bishi tana share hawayen fuskar ta tana fatan ya sauko  su cigaba da rayuwar su yanda suka saba, domin ta gasu hakan nan, ta kuma dau darasi, dakin ta kamo, ta yi wa su Ammi sannu kana ta zauna kan ta a kasa, "ya haka Amal ki saki jikin ki mana, ko bakya jin dadi ne?" Ammi ta tambaye Amal  tana kallonta.

Kunyar ammi mai yawa ce ta dirar mata, domin tasan cewa anty rahilat na sonta sosai, ta yaya ita kuma ta ki jinin ta a baya? Tabbas babu wata uwa da zata so hakan, ajiyar zuciya ta sauke tace"Anty babu komai"  ta ce tana murmushin yake.

"Toh ai shikenan" Ammi ta ce tana mikewa hadi da cewa "bari na dauko miki mutumin ki nasan ma yayi sanyi yanzu( tana nufin kunun aya, kasancewar Amal na son shi)ammi ta karasa tana barin wajen, jinjina kai Amal tayi tana jin zuciyar ta na karyewa.

Barin Ammi dakin, yayi dai dai da shigowar su Daddy Wanda Adam yayi musu jagora har zuwa dakin inda majinyacin ke kwance...

kuyi manage kafin gobe, wallahi bacci nake ji sosai, daurewa nayi domin farincikin ku, much love my people.😘

Share✔
Vote✔
Comment✔
Edit❌

NoorEemaan
07082281566

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now