20

173 10 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓

Written by NoorEemaan✍

Page 39-40

.......... Gaba daya jiyayi zaman office din ya ishe shi, company ya bari ya nufi gida kamar wani zautacce shi kadai sai surutu yake a mota, ai ranar gaba daya ma'aikatan gidan suma sun san oga baya cikin hayyacinsa, domin ya fita da mota yafi sau a kirga duk cikin neman su ammi daga baya ya dawo cikin gidan ya zauna cikin rashin sanin madafa, shi yanzu burinsa ya gansu domin daga uwar har yar yana bukatarsu domin suna da amfani agareshi ba kuma yaso asirinsa ya tonu a gari....

A yau asabar dubban jama'a suka shaida daurin auren AABAN ABDUR-RAUF MAI FATA TARE DA KYAKYYAWAR MATARSA ABRAR SAJEED. Aaban dake sanye cikin tsadadiyyar gezna fari da aka yi masa dikin babban riga, tsadadiyyar zaran dinki ya kasance golden, hula da talkaminsa sau ciki suma kalan shigarsa ne, hannunsa kuwa rolex watch ne me tsada gaske.... yana jin an shafa fatiha wani sanyin dadin ya shiga ratsa jini da sokan jikinsa, kana kallon sa zaka hango wani shirtattacen  murmushi shimfu'de kan kyakyyawan fuskarsa,... Bayan jama'a sun fara watsewa ya nufi wurin daddy dake ta gaisawa da jama'a, a bazata daddy yaji Aaban ya rungumesa hadi da furta
"nagode dad Allah ya kara girma"
Bubbuga bayansa daddy yayi hadi da cewa "godewa Allah son, Allah ya baku zaman lafiya"
"Alhamdulillah, ameen ya Rabb dad" ya fada cikin muryan dakeson bayyana yanayin farincikin dayake ciki...

Daga wurin daurin auren reception aka wuje direct a wani hada'dden hall, wanda kuma ya kasance zallan maza ne a wurin, Aaban Allah-Allah yake a tashi ya je ya ga decent one dinshi, domin arufe take adakin wanda hakan ya kasance umarnin mummy ne wanda shi be san dalilinta nayin hakan ba.... (Mummy kuwa tayi haka ne domin kada ta fito mutanen biki su ganta ta, ta rasa amsar basu)

Da misalin 12 na rana aka watse daga taron babu bata lokaci ya nufi gida, domin burinsa kawai ya jita a kirjinsa, yaji wannan feelings din na kasancewarta halalinsa, musaddiq ne ya tuko su a tsadaddiyar motar Aaban di'n da yau ya fara hawanta, shi musaddiq din dariya hadi da mamakin abokinsa yake domin be taba tunanin cewa ze so wata ya mace aduniya haka ba, domin baro-baro ya karanci zumudi a fuskarsa, amma shi Aaban  matsewa yake shi ala dole kada a ganosa...

Isarsu cikin farfajeyan gidan yasa sauke wata ajiyar zuciya me karfi, Wanda yasa musaddiq bushewa da dariyar mugunta, ko kallansa Aaban din be yi ba ya fice a motar....

Yana shiga falon nasu ya ga  mata da yawa duk da cewa ba'a gayyaci mutane  ba se dai yan'uwa na jiki amma ba laifi sunyi jama'a, dafe kai yayi domin yanzu zasu sa masa ciwon kai domin dayasan da mutane a falon, toh da ta baya ze shiga part dinsa, wata yar'uwar mummy ce ta fara hangonsa, guda tasaki, yayinda sauran suka fara tsokanar shi ango-ango na amarya, ina amaryan taka? Ko rowar ta kake mana? Be basu amsa ba kawai ya gaishesu ya wucewarsa, "miskili kafi mahaukaci ban haushi" wata tsohuwa ta fada, sarai ya jita amma ya shareta shi yana mamakin idan aka kira shi miskili, she dai yasan ba miskili bane shi kawai bayason yawan magana da shiga abunda ba ruwansa...

Mummy ya hango tsaye a dinning table tana shirya aminci, "first love" ya kirata cikin dadin muryansa da amonsa ke fitar da zallan farinciki da yake ciki

"my son" mummy ta kira shi tana sakar masa murmushi, rungumeta yayi yayinda hadi da cewa
"thank you so much mum"

"Don't mentioned my son, ina fata baka manta da sharadi na ba ko?"

Jinjina mata kai yayi,
"Good ga abinci na hada maka nasan baka ji komai ba, zan aiko Amal ko Hannan su kawo maka"
Hannunta ya sumbata hadi da barin wurin still be ce komai ba.

Bude kofar part dinsa yayi ya shige, yana kokarin rufewa, yaji sallamar Hanan, bude mata kofar yayi hadi da bata hanyar shigowa, dire abinci tayi a kan dressing mirror hadi da rungunme Aaban tace

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Donde viven las historias. Descúbrelo ahora