3

280 10 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓

✍written by noor Eemaan

sorry guys nayi mistake a page din baya maimakon nasa 3-4  sai na 2-3 yanzu zamu tashi ne a 5-6 fatan an gane.

page 5-6
ganin wanna budurwan data taimaka mata kwance kan nata katifan ga kuma kayan ta a jere a abangarenta kenan itama room mate dinta ce kenan? ta aiyana hakan aranta, jin alamun motsi  yasa wanna budurwan tashi daman ba bacci take ba game take a tsadaddiyyar wayarta.
mikewa tayi ta dawo gadon abrar tana sakar mata murmushi zata yi magana kenan  wayarta yafara ringing amsa kiran tayi tana murmushi
" ya Aaban dina" tafada cikin maganarta mai dan sauri -sauri daga dayan bangaran akace
"yes little hanan how are you doing?"
  "am doing great my sweet yaya"
  "happy to hear that" yafada cikin tsadaddiyar muryansa, kin gama settling komai little?"
"yes yaya gani a dakinmu ma tareda roommate dita"
"ok hope she's good i mean mutuniyar kirki ce?"
"i guess so yaya i just met her today"
" ok bye take care"
"i will ya Aaban, bata da lafiya zaka mata sannu ina nufin room mate dina?"  kit ya kashe wayar, murmushi tayi  tana mamakin halin yayanta bayason magana sam haka kuma kula mace baya cikin tsarinsa da kyar kaga dariyarsa...

abrar datake kallon wanna budurwan tun dazu cikin mamaki don bata yi tunanin tana jin hausa ba, saboda yanayin kalar fatarta yafi kama dana larabawa.
"so sorry for disturbing you, so tell me which country are you from?" murmushi abrar tayi kana tace " banyi tunanin kina jin hausa ba"
"lah kema ashe kina jin hausa"
wanna budurwan tafada, sai suka fashe dariya su duka biyun suna rungume juna.

"gaskiya nayi farinciki sosai musamman lokacin dana gane cewa room dinmu daya, ashe har yarenmu daya"
toh dai sunana hanan abdur-rauf babana dan asalin garin adamawa ne, mummyn na kuma shuwa-arab ce ina da yayye biyu ya Aaban da anty amal, muna zaune a abuja a unguwar maitama tarihi na atakaice kenan"
" kefa?"
"sunana abrar sajeed abbina dan asalin garin nijer ne ammina kuma yar cameroon ce, abbina yarasu yanzu dai ina zaune tareda ammina a gidan mijin ammina dake abuja"

"ayyah Allah ya jikan abbinki, gaskiya komai naki mai kyaune har sunan ki ma, kinsan da farko wallahi nazata ke irin black american dinan ce domin yanayin kalar fatarki mai kyau ce" hanan tafada cikin iyakar gaskiyarta

"ai nima nazata ke balarabiyar riyad ce" abrar ta fada, sai sukayi dariya atare.

"oops surutuna yasa na manta ban tambayi jikin kawata ba, so how are you feeling now?"
" feeling more better alhamdulillah nadan ji dadin jikina nagode da kulawa"  abrar tafada tana murmushi
" never mind my dear" zan nuna miki yanda zaki na saita pad din, gashi da yawa aka siyo min daga gida sai mu dinga amfani dashi kafin mu siyi wani, kinsan tun ina10years nafara ganin period" zaro idanu abrar tayi cikin madaukakin mamaki tace    
" are you kidding me"
abrar ta fada cikin rashin yarda.

"i swear  hanan ta fada tana dariya kinga lokacin ban kaiki bako?"
"Allah mai halitta abrar tafada tana jinjina kai haka dai suka cigaba da  hirarsu wanna abrar tasaki jikinta ba laifi wanda rabon data yi hira haka tun da alhaji shettima ya shigo rayuwarsu, ga hanan akwai surutu kam, can sai ga cikon ta ukunsu da kayanta yar america  ce mai suna linda robbet nan suka cigaba da hirarsu gwanin burgewa...

"NIGERIA"
cikin sanda alhaji shettima ya bude dakinsa yafito gudun kada ammi dake kwance tana bacci taji abunda zae fada babban palo ya fito ya kara waya  akunnensa kasa kasa yace " hello kwaro ya akayi ne kayan nan sun iso kuwa?"
daga can bangaren akace " Allah ya ja da ran alhaji ai mun sha da kyar, saura kiris daka ji an garkamemu" ajiyar zuciya alhaji shettima yasaki kana yace afili yace "toh gobe mu hadu a guest house dina"
"an gama ranka ya dade" kwaro yafada cikin muryansa mara dadin amo.

washegari kamar yadda alhaji shettima  ya fada suka hadu da kwaro a guest house dinsa inda suka tattauna akan gurbataciyyar harkansa ta shigo da barasa daga waje, kuma har ila yau Allah be basu ikon kamasu ba,  bayan kasuwancin sa dayake babu wanda yasan alhaji shettima na wanna harkan daga shi sai yaransa su kwaro, bayan sun raba tsadaddiyar giyan wa customers dinsu ba karamin riba aka samu ba shiyasa alhaji shettima yace baya iya hakura da harka domin yana samun kudi masu tsoka wanna kenan...

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now