15

171 9 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓
(A heart touching story)

written by Noor Eemaan

page29-30

cikin madaukakin mamaki mummy tace "Aabaan, Hanan! kun san tane?" amma sam hankalinsu baya tare da ita musamman Aabaan daya ke jinshi cikin farinciki mara iyaka adalilin ganin Abrar, tabass baya ko tantama decent ce  tsaya agabansa, agabansa ma cikin gidansu, duk da ta kara girma akan da, amma ko yana magagin bacci baze taba manta fuskartaba, dama all this while itace? amma ya kasa gane ta...

kusan lokaci daya suka karasa gabanta shi da Hanan, beyi tunanin abunda ze faru ba, beyi tunanin cewa akan be dace ba, shi dai burinsa kawai yasa ta a kirjinsa ko ze ji saukin ciwon sonta hadi da radadin rasata dayayi abaya...

cikin zafin nama ya manna ta a kirjinsa, yayinda ya lumshe ido  yana jin saukin radaddin sonta a kirjinsa, cikin muryansa dake son bayyana rauninsa yace

"where have you been decent one? i so much miss you please stay with me ok?"

Abrar kuwa shiru tayi ta lafe akirjinsa sai faman raba idanu kawai take, kukan Hanan ne yadawo dashi nutsuwarsa, tace

"bestie Abrar daman kece? meyasamiki, yasake taba ki ne?  dan Allah ki gayamin Abrar"... Abrar kara shigar da kanta jikin Aaban take hadi da boye fuskarta, kukan hanan ne ya karu domin ta fahimci ciwon Abrar yafi na da tunda har ta kasa ganeta...

cikin mamaki su mummy ke bin Aaban da kallon domin basu taba tunanin cewa ze iya wanna rudewar akan mace ba, macen ma mara cikakken lafiya, cikin wani sabon rudewan mummy tace "ba magana nake muku ba, nace kun santa ne!!!" mum ta kara fada  a tsawace

sai lokacin Hanan tace "mummy Abrar ce fa, Abrar kawata damuka hadu a cyprus"

cikin sake daure kai mummy tace "ban gane ba, daman tana da tabin hankali ne?"

kuka Hanan tasa tace "mummy ba tabin hankali bane, my bestie is not insane matsananci damuwa hadi da firgici ne ya haddasa mata wanna halin datake ciki yanzu haka"...

mummy zata sake magana daddy yace "mummynsu duk ku zauna mu tattauna wanna maganar a nutse domin nima kaina ya daure, saboda ina mata kallon sani, kallon Aaban dake rugunme da Abrar har yanzu idanunsa alumshe daddy yayi,  murmushi  yayi dashi kadai yasan ma'anar yasa kana yace abokina zo ku zauna muyi magana"

sai lokacin yabude idanunsa dasuka sanja launin, yayinda yake jin zafin ciwonta, meyasa duk haduwarsu baya taba ganinta cikin yanayi mai kyau, yakuma fahimci wasu abubuwan daga maganganun Hanan, a hankali ya rabata da kirjinsa ya riko hannunta, saurin sake shigewa jikinsa tayi, be hanata ba, ya tafi da ita ahaka tana gefen kirjinsa kan kujera suka zauna yayinda ta shiga boye fuskarta tamkar me jin tsoron kada akamata.

Hanan kasa hakuri tayi tace "yanzu bestie na baki gane ni ba, nice fa Hanan"

Aaban kallon Hanan yayi yana cike da mamakin yanda har Hanan ta santa har haka, Abrar kuwa tsura mata ido tayi kana ta fashe da dariya hadi da dukan Aabaan tana masa alaman ya kalli Hanan, cikin rashin jin dadi halin datake ciki ya kama hannun datake dukansa dashi ya matse cikin nasa hannun kana ya dora hannunsa kan lips dinsa alamun tayi shiru, kallonshi tayi sai kuma tayi shiru kamar wacce ta fahimci maganarsa...

gyaran murya daddy yayi yace " Mummynsu idan na fahimce ki, wanna Abrar itace kikeso Abokina ya aura ko? shin baki taba haduwa da ita bane?"

cikin mamakin da be gama sakin mummy ba tace "daddynsu haka maganar take, domin Aaban ya shiga mayuwanci hali abaya akan son wata patient daya ce ya hadu da ita, saide yace mun ya ganta ahalin na  mara kyau domin an mata fyade ya sinceta, nikuma nace masa da raina dai bazan bari wacce bata tare da mutuncinta ta shigo cikin zuri'a ta ba, na kuma ce masa kawar Hanan Abrar ze aura, domin na yaba da nutsuwarta duk da cewa ban taba haduwa da ita azahiri ba... Ajiyar zuciya ta saki kana ta cigaba da cewa; sai dai yanzu na kasa gane komai, domin naji Hanan tace kawarta ce Abrar, ga Aaban daya nuna shima yasanta,  gashi naji kaima kace kana mata kallon sani, daddynsu am totally confused na kasa gane komai"...

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now