28

157 6 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓
(A heart touching story)

Written by Noor Eemaan

Not edited

Page 55-56

.......haka suka shige motarsu driver ya ja suka fice daga gidan, da kallo alhaji Shettima ya bisu kamar ya rusa kuka, domin ya ga samu ya ga rashi, ga Abrar nan ta zo har gaban sa amma ba halin daukar ta domin ta fi karfinsa, saboda bambamcin a bayyane yake bazai iya ja da su Daddy ba, ga kishin Aaban din dake cin sa arai, "shi din waye da har zai rike ta a jikinsa?" Ya fada a bayyane...

Cikin mutuwar jiki ya koma cikin gida, yayinda ya tarar da wayarsa na ringing,  number Kwaro ya ga ni baro baro a rubuce kan screen din wayar sa, cikin sauri ya daga hadi da karawa a kunnensa

"Oga akwai matsala fa, hukuma ta kama mu yanzu a hanyar dawowar mu, daga mu har motan barasa (giya) gamu a tsakiyan su" kwaro ya fada cikin tashin hankali ...

Kasa tiles alhaji Shettima ya zube ya shiga birgima yayinda yake ta maimaita "na shiga uku shettima" tamkar wani zautacce... Maganar kwaro ce ta sanya shi dawowa nutsuwar shi "ya haka kuma oga? Mun fi ka shiga tashin hankali fa, domin mu dari muka shiga ba uku ba, gasu sun zagaye mu da manyan manyan bindigogin su jira kawai suke mu bude motar"

"Kwaro ku bi ta kan yan iska da motar ku taho, kafi kowa sanin cewa naira na gugan naira har million dari na sa aka yi order barasan nan saboda riban da muka samu a baya, ta ya ya kake tunanin zan juri rasa wadan nan zunzurutun kudade'n?"

Kwaro kallon manu da ya hada uban gumi yayi yana daf da sa kuka yace "manu oga ya ci kai fa, ta ya ya zamu iya wucewa gaba daya suna zagaye mu? sarai alhaji Shettima yayi abinda yace amma sam bai damu ba yace; kwaro ku yi  duk yadda zaku yi ku kubuta daga hannunsu, idan haka bata samu ba toh kada ku bari sunana ya fito cewa ni na aike ku, zan yi iya kokarina domin ganin an fidda ku, amma kada ku bari sunan... "

"Tau" ya ji karan bingida ta cikin wayar yayinda yaji ihu'n su kwaro ya cika kunnen sa,,, kuka mara dadin ji Alhaji Shettima ya Sa yayinda ya cigaba da birgema yana surutai, da alama ya fara fita a hayyacin sa....

Bangaren su kwaro kuwa, daya daga cikin yan sandan ne ya arbi bindinga dai dai saitin glass din gaban motar take ta tarwatse, hakan yasa su kwaro sakin ihu, cikin kwazo da sanin makamin aiki dan sanda yace "ku fito, kafin na kirga uku in ba haka ba zan tarwatsa kan ku da alburushi"...

Cikin rawan jiki su kwaro suka fito, manu kuwa fitsari ya saki saboda tsananin tsoro dama kwaro ya fishi dakakiyyar zuciya... Cikin mota suka cilla su bayan an sanya musu handcuffs, waya suka  bugawa station din su, take manyan su suka basu umarnin su tafi da giyan, su tarwartsa su hadi da kona su, haka kuwa suka yi wasu sun nufi station yayinda wasu suka ja motar su kwaro.... Mutanen gari musamman wandanda suka tsani giya, murna suke sosai suna kabbara suna fatan a cigaba da kama irin wadannan mutanen masu shigo da giya kasar muslimai....

2 MONTH LATER (BAYAN WATA BIYU)

" innalillahi wa Inna ilaihi raju'un " Adam ya ambata bayan Amal ta gama bashi labarin Abrar, domin ya ganta tana yawan kuka shiyasa ya tambayeta
"tabass wanna diyar anty na ce" in ji Adam

Cikin mamaki da faduwar gaba tace "diyar  anty ka kuma wace antyn taka?"

"Anty Rahilat mana, domin wanna labarin sak irin wanda ta bamu ne, kuma ita ma yarta ta bata dole yanzu in je gida mu tafi gidan  ku dukanmu, domin bana ko tantama wanna Abrar din ita ce  Abrar din Anty na"

  Adam yace cikin tabbaci kana ya kalli Amal  fuska a daure ya sake cewa "yanzu Amal diyar anty Rahilat kika nuna wanna tsanar da tsangwaman? Ya fada rai a bace...

Kuka ta fashe dashi ta durkusa gaban sa domin babu abinda ta tsana kamar bacin rai Adam saboda tsananin son da take masa, rungume kafafunsa ta yi tana bashi haku'ri janye kafarsa yayi yana kokarin barin dakin har ran shi ya ji haushin abinda tayi... Ringing wayar sa ce ya sa shi tsayawa daga barin dakin, " hello baba" ya ce maimakon yaji muryan baba Sai na mama cikin tashin hankali tace "maza kazo Adam baban ka yayi hatsari muna asibitin da muka saba zuwa"... Ai katse wayar ya yi ya fice daga dakin hankali tashe yayin da Amal ta sanya mayafi ta biyo shi, saboda duk  ta ji abinda maman ta ce...

Ninke sallaya yayi bayan ya idar da sallar shafa'i da wuturin sa, domin lokacin karfe sha daya ta yi, mafi yawan lokuta a irin wadanan lokutan yake sallar, kan gadon ya hau
"Wiffffy"
ya kira sunan ta dai dai saitin kunnenta, yarrr ta ji tsigar jikinta ta tashi, bude idanunta tayi karaf suka hada idanu kasa ta yi da kanta tana mamakin tsananin haku'rin sa, domin duk wadan nan tsahon lokutan da suka yi tare bai taba gwada kusantar ta ta ba ko wani abu ba, daga ya rungumeta ko ya sumbaceta a hannu, kumatu, ko goshi shikenan ta aiyana hakan a ranta tana sakin ajiyar zuciya...

"Wifffy" ya sake kiranta a karo na biyu "uhmm" ta amsa a shagwabe, tana turo dan karamin bakinta.

Murmushi ya saki yace "tashi, nasan ba bacci kike ba" ya fada yana daga ta zaune.

Hannunta ya riko cikin nashi yana kallon dacewa da hannuwansu suka yi, domin farin fatar sa da brown skin din ta da ya hadu da juna sai hakan ya bada kala mai kyau, turo baki ta yi ganin yadda ya kurawa wa hannunta ido, a shagwabe  tace
" kana kallon bakin hannu na ko?"

Murmushi mai sauti ya saki ya ce "ai ke ba baka bace, you re brown in complexion which I so much like, na fi son kalar fatar fiye da tunanin ki"...

Murmushi ta yi cikin karfin hali, domin damuwar rashin Ammin ta ya fi komai damunta a yanzu, hannunta ya shiga murza wa cikin wani salo ya ce " Decent one nasan cewa ba dadi rasa babban jigo a rayuwa kamar uwa, duk da tana raye amma bamu san in da take ba, ana kan neman ta muna kuma fatan a dace, please ki kwantar min da hankalin ki domin kada idan mun hadu da Ammi tace bana kular mata da ke " ya kara sa fada da iyakar gaskiyar sa...

Murmushi ta yi wanda har jerarrun fararen hakoranta mai dake da siririyar wushirya a tsakiya ya bayyana, domin sunan Ammin ta kadai daya ambata ya sa ta cikin farinciki...

"In sha Allah na daina" tace cikin zazzakar muryarta da ya hadu da yanayin sanyi da take ciki ya bada amo mai dadin gaske...

Haka kawai yaji yana jin son sa ta farinciki ta hanyar siya mata favorites dinta wato nama, ice cream da chocolate, duk da cikin su tafi son nama sosai.

"Za ki ci nama?" Ya fada yana kallonta
Cikin sauri ta gyada kai alamun "eh" da murmushi farinciki kan fuskar ta.

"Bari in je in siyo miki yanzu zan dawo" ya fada yana mikewa, saurin mikewa tayi itama tana kokarin daukan hijab din ta, kallon ina zaki? yake bin ta da shi.
"zan bika" tace fuska a marairaice
Ba musu ya kamo hannunta suka fice bayan ya sanya mata hijab din, haraban gidan suka fito ya nufi parking space_ wani sabon lifan din sa wanda ya siya kawai dan irin wanna fita musamman ta dare bai fiye son hawa mota ba...

Tayar da mashin din yayi yace ta hau, a tsorace ta hau domin tana tsoron mashin, kamkame shi sosai tayi hadi da kwantar da kanta kan gadon bayan sa suka fice... Mummy da Daddy dake zaune kan gadon dakin Daddy suna shan hirar soyaayyar su, suka kalli juna suna saki murmushin farinciki, domin  kan idonsu su Abrar suka fice kasancewar lalube a dage yake.

Cikin kwarewa yake gudu sosai kan kwalta yayinda iska mai dadi ke kada su, kasancewar kuma babu ababen hawa a titin sosai ya bashi daman gudun son ranshi, yayinda yake murmushi jin yadda Abrar ta kamkame shi, daga karshe ma da ta gudun ya ki sauki ta fashe da kuka domin har wani laayi yake da babur din kamar zai zubar dasu... "Pure heart ka taimka ka rage gudun nan dan Allah!" tace tana kuka da iyakar gaskiyar ta

Shiru ya yi, bai kuma daina gudun ba domin sosai yake jin dadin yanayin da suke ciki "sai na gaya wa Mummy kana gudu dani" tace tana cigaba da kukan.

dariya ce take cinsa amma bai yi ba, wani tsalle ya yi dasu gaba daya daga Babur din har su suka yi sama kana suka sake dira kan kwalta wani ihu ta sa yayinda kukan sakalcin ta ya karu tace "ni ka sauke ni na fasa cin naman"....

Manage pls bana da a enough charge.

SHARE✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌

Noor Eemaan✍

07082281566

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now