10

196 5 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓

written by noor Eemaan
wattpad@NoorEemaan

page 19-20

sai da ta tabattar da tayi nesa daga gidan da alhaji shettima ya kaita kana ta tsaya jikin wata bushiya tana sauke numfashi, kuka takeso take har ta sauka kan guiwowinta domin jitayi kafafunta sun gaza daukarta ta kai kusan mintuna ashirin awanna halin...
hanan ce ta taho tana waige waige ko zata ga abrar, ai kuwa tun daga nesa ta hangota da gudu ta karosa wajenta hadi da dafata afirgice abrar ta dago kanta ganin hanan ce yasa ta rungumeta cikin hanan kukan tasa, kukan tausayin abrar sun dau tsahon lokaci kana suka tsagaita
"abrar waye ya dauke ki? ya miki wani abu?" cikin damuwa hanan ta jera mata wandanan tambayoyin.
"hanan so yake yaga bana numfashi adoron duniya sannan hankalinsa zai kwanta harnan cyprus ya biyo niiiiii" ta ja karshen maganar cikin kuka...
"what! kina nufin mijin ammi?"
"eh shine "
"innalillahi wa inna ilahi raju'un, amma babu abunda yamiki ko?" hanan ta tambaya cikin damuwa
jinjina kai tayi alamun "eh" ajiyar zuciya hanan ta sauke tace "thank God"
ganin nisan dake tsakanin wajen da cikin hostel din ba nisa yasa suka karasa akafa...

bangaren alhaji shettima kuwa ya kai kusan awa daya yana rike da maransa domin ba karamin buguwa yayi ba bayan ya dan ji dama dama ya koma hotel din daya sauka, washegari ya koma nigeria cikin rashin jin dadi domin sosai yaso yasake lasar zumanta amma duk da haka zai biyo mata ta wata hanyar....

tun daga ranar da abunan ya faru abrar ta sake shiga damuwa fiyeda na baya, ta sake ramewa sakamakon tsoro da firgici gani take alhaji shettima zai sake zuwa har hostel dinsu, bata da aiki sai kuka- kuka tun hanan na lallashi har tayi shiru ta zuba mata ido, wata rana cikin dare suna bacci, abrar ta fara kyakyata dariya sosai dayayi sanadiyar farkawan hanan da linda, gaba daya ta hargitsa dakin ta sanja masa kamanin komai hannuta ya taba sai da buga shi da kasa, in mai fashewa ne yafashe, linda kuwa makurewa tayi can karshen gadonta tana zaro idanuwa (kun san turawa ajebo's ne basu son ganin tashin hankali😂) cikin sauri hanan ta nufe ta shiga jijigata "abrar what are you doing to your self? ki daina dan Allah!" dif dariyanta ya dauke kurawa abrar ido tayi na tsawon mintuna sai kuma ta fashe da kuka mai tsuma zuciya..
"hanan kisan me?
"a'a" hanan ta amsa cikin tausayinta
"idan mun kamalla karatun mu na zama lawyer, sai na maka shettima mijin ammina akotu, kuma idan alkali bai yanke masa hukunci daidai da zalunci daya yi mun ba sai na yanke masa da hannuna ta fada cikin fitar hayyaci hadi da kallon hannun nata, addu'oi hanan ta tofa mata babu jimawa kuwa bacci ya dauketa ajiyar zuciya hanan ta sauke hadi da rufe ta da bedsheet, sai lokacin ta lura da linda dake takura da bata cikin damuwa babu abunda zai ta yin dariya
" linda she's fine now, you can now go back to sleep"
"are you sure?" linda ta fada atsorace
"yeah sure" hanan ta amsa tana haye gadonta, tunani ta shiga yi fatan ta kada abunda take zargi ne ke damun abrar, dole gobe ta kaita hospital adubata gashi daman gobe basu da lecture duk da cewa babu wasu kudi a acct dinta amma zata kira ya aaban ya turo mata da wanna tunanin ta kwanta bacci...

washegari hanan tace abrar ta shirya zasu asibiti ba musu ba tambaya ta shiga shiryawa domin yanzu ba bakomai dake tambaya akansa ba saboda tsananin damuwan dake ranta, itama hanan shiryawa tayi sai a sannan ta fara dialing number aaban...

yana dakin gymming dinsa yayinda yake daga karfe cikin kwarewa gaba daya ya hada gumi ringing din wayarsa daya shine ya sa shi ajiye karfen ahankali hadi da mikewa, latsa kore yayi kana yayi sallama cikin muryansa mai dadin amo, amsawa abrar tayi hadi da gaishe shi, sannan ta fara cewa "uhmmm hmm ya aaban ina wanna kawata ta school bata da lafiya inaso...... you know banason dogon bayani just go straight to the point" jinjina kai tayi kana tace "i want money" kit ya kashe wayar bayan kamar minti taji alert ya shigo zaro ido tayi lokacin data ga yawan kudin daya turo duk da cewa tasan yayanta bai iya bada karamin kyauta ba amma tayi mamakin yawan kudi, sake dialing numbers shi tayi tana ji ya daga tace"yaa aaban nagode sosai, sai kawai yaji muryan abrar ta cikin wayar ta ratsa ta kunnuwansa tace"hanan let's go"
jiyayi wani yanayi na shigarsa haka kawai yakeson sanin mallakiyar mai zazzakar murya nan don haka yace "hanan who is that?"
"my best friend" bai kara cewa komai ya kashe wayar... da kallon mamaki tabi numbers yayinda take murmushi "wai yau ya aaban da kansa ya tambayi wata mace?"
"mummy most hear this" tafada tana murmushi, suna hanyar zuwa asibiti hanan ta fesa wa mummy cikin murna da mamaki mummy tace wacece? dariya hanan tayi ganin yanda mummy tayi maganar cikin zumudi "mummy abraer ce fa" ta fada tana kallon data fada duniyar tunani bayan sun gama wayar mummy ta jima tana mamaki domin ada tayi tunanin danta bashida cikakken lafiya, sai kuma tayi masa sha'awar auren abrar din domin tana son yarinyar hakan nan duk da bata taba ganin ta ba, hanan na yawan fadin kyawawan hallayenta, amma hakan baya nufin zata yi masa dole, duk da cewa shi din mai yi mata biyayya ne...

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now