16

146 9 2
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓
(A heart touching story)

this hole page this dedicated to my lovely niece nafeesat (feenah), much love my fee❤.

written by noorEemaan

page 31-32

kamar koda yaushe binta da idanu yake  baya ko gajiyawa  da kallonta, yayinda sunanta daya ji Hanan na kira ke masa yawa a kirjinsa, (Abrar) "you re so special my decent one including your name" ya fada cikin shauêkin sonta,  tabass shi so babu ruwansa da kyau, kudi, wayewa, talauci, hankali ko rashinsa, mutum kan kamu da gashi ko da be shirya ba, hakika zafin soyaayar dayake mata baya jin akwai wanda ze yiwa masoiyarsa irinsa, domin a kallon farko a kuma haduwar farko zuciyarsa ta buga domin ita kadai, babban damuwarsa yanzu "mummy" domin so yake ya mallekata ta zamo halalinsa ko da ayau ne shi ashirye yake, kara binta da kallon yayi ganin yanda take hargitsa masa kayansa awardrobe a kalla ya gyara dakin yafi sau a kirga yau domin musamman yaki zuwa aiki saboda kula da ita, amma daya gama zata sake hargitsa dakin, sadai sam be damu ba matukar hakan ze bata farinciki, abunda yafi damunsa waye yake bibiyar rayuwarta? shine amsar dayake son sanin...

ganin yadda take sosa kai hadi jikinta yasa jin ba dadi, domin tabass tana da bukatar wanka dama wanke kanta, saboda tun ranar daya sake haduwa da ita rabonta da wanka gashi bata yarda da hanan bare yasa tayi mata duk da be manta gargadin mummy ba, cije lebbansa yayi kana yace
"mummy why!"
domin data amince da a ranar ze sanar da daddy cewa a aura masa ita domin ya samu daman kula da ita yanda ya kamata.

sai kuma yayi tunanin hada mata ruwan wanka ko zata iya wanka da kanta, mikewa yayi ta kuwa biyosa abaya, bayan ya hada mata ruwan wanka yace
"my decent one kiyi wanka kinji ina jiranki"
itama cewa tayi "my decent kiyi wanka kinji ina jiranki" tafada cikin kwaikwayonsa, murmushi yayi kawai ya fito hadi da rufe toilet din...

yana zaune yana jiran fitowar, ya kuwa ji karan bude kofa, kurawa hanyar ido yayi yana jiran karasowarta, "ya salam" yace bayan ta bayyana gabansa domin gaba ta jika kayanta da ruwa batareda ta cire kayan  ba, ruwan har diga yake a kasan tiles, kusa dashi tazo ta zauna tana kankame jikinta alamun sanyi domin Ac na kunne, cikin tausayinta ya bude wardrobe dinsa ya dauka rigar sanyi mai kauri yasanya mata wanda yayi mata yawa, shi be san yadda ake kula da mutum ba, besan abunda ze mata taji saukin sanyin dake shigarta ba, Ac ya kashe kana ya riko hannunta ya kwantar da ita kan gadon hadi da lullubeta da bedsheet, kallonsa kawai take bata ko kiftawa yayinda hakoranta ke karo da juna "daf da kunnenta yace
"i love you"
cikin kunnensa yaji dariyarta na tashi da karfi, kallonta kawai yake cikin matsananci sonta, sai ta maimata maganarsa ta ce " i love you" yayinda ta cigaba da dariyar har bacci yayi nasaran dauketa...

Ajiyar zuciya ya sauke domin tana bukatar bacci, hakan zesa kwakwalwarta ya dinga samun hutu, dakin ya shiga gyarawa bayan komai yadawo tsaf tsaf, yaji ringing wayarsa na tashi saura picking call din yayi domin bayason ta tashi, number asibiti ya gani, dafe kansa yayi domin yasan kwanan zancen... yana dagawa yaji ance

"hello sir an kawo wani patient yanzu cikin mayuwanci hali your attention this needed please"

runtse ido yayi yayinda yasake waresu kan Abrar cikin rashin jin ba dadi yace " i will be there in a jiffy" ya katse wayarsa...

wanka yayi cikin sauri ya shirya, kana ya fice yana waiwayon Abrar yana fatan kada ta farka har ya dawo...

fitarsa da awa biyu kuwa ta farka da kukanta, yayinda ta shiga hargitsa dakin kamar ba dakin daya gyara ba, sai kuma ta mike ta sauko kasa, ai kuwa tayi arba da mummy, amal, hadi da hanan dake kwance, domin tun dazu takeso mummy ta tashi ta haura saman ya Aabaan domin duba jikin Abrar, amma mummy taki tashi kamar ma ta fahimci abunda takeson yi, Abrar kuwa ganin mummy yasa ta rabe jikin bango tana mata kallon tsoro, harara mummy ke jefa mata hadi jifan ta da mugayen kalamai, Abrar abin tausayi yayinda Hanan ke jin zafi abunda ke mummy keyi sai de bazata iya cewa komai ba...

"mtsssssweew mummy ni wallahi kada mahaukaciyar yarinyar nan ta zauna da bikina a gidanan dangin Adam su raina mu, kawayena ma ajina ya zube a idanunsu, (kasancewar bikin Amal saura wata daya, da saurayinta Adam wanda sun dade tare tun tana level 2 a jami'a).

mummy kuwa kasa bawa Amal amsa tayi saboda takaicin abinda ke cinta arai ace kamar ita danta ya rasa wacce yakeso sai mai tabin hankali, kuma wacce bata tare da budurcinta, itakam ina zata kai wanna abun kunya, idan har daginta ma suka ji wanna labarin ai ta  banu, tabass taso Abrar tun kafin ma ta ganta, amma banda yanzu....

"mummy kiyiwa anty amal magana ta daina zagin bestie na, na shafa fada ita ba mahaukaciya ba ce"

wani mugun kallo mummy ta antaya mata, bata kara cewa komai ba tanufi wajen Abrar dake rakube har yanzu sai de tana zuwa wajenta ta cigaba da boye kanta cikin jikinta, Hanan na riko hannunta ta ruga sama bangaren Aaban aguje, dariiyar mugunta Amal ta sakarwa Hanan, kuka Hanan tasa ta nufi dakinta....

bangaren alhaji shettima kuwa zaune suke a guest house dinsa shi da yaransa su kwaro, "anya kwaro kuna aikin ku kuwa? ace har yanzu baku ganta ba duk tsayinç kwanakin nan?" alhaji shettima yafada cikin damuwa

"ai oga muna kokari fa, har dare muna nemanta, amma ko me kama da ita bamu gani ba, Amma oga mezai hana mu bincika asibitin daka sa muka dauko ta kwanaki, kila wani ya buge ta tana can" kwaro ya fada cikin muryansa ta yan jagaliyya bakinsa har wani karkacewa take, yayinda yake muzurai da kwala kwala idanunsa masa launin ja.

dariyar jin dadi alhaji Shettima yayi yayinda yake shafa katon tumbinsa cikin jin dadi yace "wato kwaro kana da kaifin tunanin shiyasa nake yinka, kana da tukwuci na musamman haka za'a yi kuwa domin yanzu zamu  tafi, tare da ni za'a je domin wanna karon zan je ne amatsayin ni  ne mahaifinta bata tayi..."

gaba daya suka mike suka fito haraban gidan, kana suka shiga motar alhaji shettima kirar BMW kana suka bata wuta isar asibitin kuwa alhaji shettima  yace kwaro da saura su zauna cikin motar, manu ya biyosa domin shi yayi shigar mutunci kaf cikinsu, babu musu suka zauna yayinda kwaro yace
"amma oga kana ganin matsala kawai ka bugo waya mu shigo, domin muna tare da kayan aiki"...

murmushi jin dadi alhaji shettima yayi yana jinjina kansa.

daidai lokacin Aaban ya fito yayinda waya ke makale akunnensa da alama waya yake kuma me muhimmanci, ga jakar aikinsa a hannu wanda ya nuna  gida ze je domin gaba daya hankalinsa naga decent one dinshi, daidai ya fito daidai lokacin alhaji shettima suka taho... kafada da kafada haka Aaban da alhaji Shettima suka wuce juna... cak alhaji shettima ya tsaya hadi da waiwaya wa ya kalli Aabaan....

manage please yau aiki ya min yawa a gida.

SHARE✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌

Noor Eemaan😉✍

kucigaba da comment domin shi ze dinga karfafa min gwiwan typing, insha Allah inason kammala book dinan kafin ranar sallah idan kuma be yu ba toh, sai bayan sallah domin ina tafe da books masu zafi bayan sallah'n  son so nake muku jama'ata💖

https://chat.whatsapp.com/FEfWeTiufpk96my8yNBeaM

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now