2

285 10 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓

written by Noor Eemaana

page2-3

ganin yana tunkaro su yasa ammi kara firgita a dari ta juya domin su gudu, sai kawai suka ji  ma'aikatan gidan sun sa dariya gaba dayansu, alhaji shima ya fara dariya gaba daya kasa motsi ammi tayi ganin  workers din gidan na dariya wanda sai yanzu ta lura dasu  dukkaninsu maza ne,  abrar kuwa kuka tasa tana cewa " ammi kinga abunda nake ce miki ko,"? ta fada da yaren buzanci, murya alhaji ce ta katse mata amsar dataso bawa abrar "ashe hajiya ta haka kike da tsoro ?yafada yana kara fashewa da dariya domin ya kasa riketa. Ajiyar zuciya ammi ta sauke ganin ba abinda take tunani bane, nan workers din suka dinga zuwa gabanta suna gaisheta cikin sakin fuska take amsa musu kana suka nufi cikin gidan mamakin irin dukiyar alhaji   fal ranta...

*1 MONTH LATER*
zuwa yanzu ammi ta zama yar gida domin lafiya lou suke zaune da alhaji, abrar kuwa har yanzu bata sakewa da alhaji daga gaisuwa shikenan, a daki take wuni  duk yanda alhaji yaso  ya jawota jikinsa ta ki bari  ammi kuwa tun tana damuwa da halin da abrar da tsiro dashi har ta hakura domin tayi fadan tayi lallashin akan ta dauki alhaji shettima amatsayin uba amma sam ta ki yarda, da ammin ta fara maganan zata sa kuka.

zaune alhaji shettima da ammi suke akan hada'ddun kujeran falon da girma falon kadai ze kai 100/100.
"hajiya?"
"na'am alhaji" ammi ta amsa.
"ki sanar da abrar cewa ran monday in sha Allah zasu fara jarabawan waec da neco domin na gama mata komai na registration ga exams card dinta da uniform" ya fada yana  mika mata wani leda mai kyau.
kasa magana ammi tayi gaba daya hawaye sun ciko idanunta tama rasa bakin godiya ashe zata samu wand ze meye gurbin musu sajeed? shiyasa akullum yaumil alhaji ke kara  matsayi aranta dalilin kaunar da yake nunawa tsoka daya a miyar ta wato(abrar).
n
"alhaji nago.... shhhhhh cewar alhaji shettima kana yadora ai abrar na dauketa tamkar yar dana haifa don uba ya sauke wa yarsa hakkin dake rataye awuyansa sai ya zama abun godiya har haka, murmushi ammi tayi kana ta bashi side hug bubbuga bayanta yayi kana yace ta kaiwa abrar kayanta domin ta fara shiri  ba musu ta mike ...
Kwance take tayi matashi da hannayenta tayi zurfi cikin tunani tamkar wata babbar budurwa mai tarin damuwa, girgiza kai ammi   dake tsaye abakin kofa tun dazu tayi kana ta karaso  bakin gadon ta zauna
"abrar"
shiru ba amsa adan tsawace ta sake kiranta hadi da girgizata, dawowa hayyacinta tayi ganin ammi ce yasa ta fara kokarin tashi zaune hadi da cewa
"ammina"
"abrar mekikeso ki mayar da kanki ne eyeh? Gaba daya kin daurawa kanki damuwa kina yar karamar ki dake  meye matsalarki? meye matsalarki abrar amsa min"
"ba...bu komi ammi ta fada muryanta na rawa" shikenan tunda haka kika zabawa kanki ,dakin ya dau shiru na mintuna uku kana ammi tacegashi inji alhaji ya biya miki waec da neco akwai uniform da wasu abubuwan dazaki bukata aciki, in kin ga dama kuma karki gode masa. Ammi ni banason wani abu daya fito daga hannunsa , toh zaki iya zuwa ki gaya masa  haka ammi ta fada cikin fushi kana ta dafa kafadarta ta cigaba da cewa koda wasa abrar kada ki bar alhaji yasan baki kaunarsa, domin zan saba miki aranar kuma ki biyoni ki masa godiya ki kuma saki fuskarki ammi ta karasa hadi da ficewa, jiki ba kwari abrar tabi bayan ammi tana kokarin daidaita yanayinta"

"da...ddy  nagode Allah ya kara arziki. Abrar ta fada kamar batason yin magana murmushi alhaji shettima yayi cikin jindadin ta kirasa da "DADDY" ameen daddy's girl ya fada yana shafa kanta ajiyar zuciya ammi tayi ganin  bata kwabtsa mata ba. Abrar  kuwa wani iri take ji ganin ta kira mutumin data k i jiki da daddy wanda batasan dalilin tsanar ba, saidai tayi hakan ne don farinciki ammi, kuma tayi farincikin domin ta gani afuskarta mikewa tayi domin komawa dakinta alhaji shettima yace" abrar bazaki zauna tare da mu ba har yanzu dai baki gama sakin jikin ki ba, sae da ta runtse idanunta kana ta juyo tace
"ina dan jin baccine daddy tafada  ok toh it's alright yafada yana mai da hankalinsa wurin ammi suka cigaba da hirarsu...
ranar monday abrar tafara zuwa zana exams.
dinta kuma alhamdulillah bata samun matsalan komai domin makarantar masu kudi ce, bayan wasu watannin ta gama exams dinta sai jiran fitowar result...

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now