12

180 7 0
                                    

🍓🍓MIJIN AMMINA NE SILA🍇🍇

written by noor Eemaan
wattpad@NoorEemaan

page 23-24

daidai ta saitin aaban ta wuce saidai sam bai lura ba domin hankalinsa naga wayarsa sai data yi gaba sannan ya juyo asakamakon wani kamshi daya bugesa gashi yanayin bugun zuciyarsa ya sanja amma ko gefen fuskarta bai gani ba domin ita ma kanta na kasa ne....

bayan ya gano inda hanan take, suka yi hirarsu da bai wuce minti goma ba wanda yawanci hirar hanan ke yinsa kana ya mike dan tafiya sai lokaci hanan ta marairaice tace "ya aaban please kabari bestie na tazo ku gaisa tare muke"
"a'a hanan i have to go zan yi missing jirgi"  ya fada bayan ya bata wani kyakyawan jaka da alama shopping yayi mata babu yanda ta iya, hugging dinshi tayi kana suna ki sallama cikin kaunar juna, zama tayi tana sauraren zuwan  abrar....

cikin sauri abrar ta taho domin tasan hanan na jiranta, kamar yanda suka wuce juna dazu haka ma wanna karon, sai dai saurin da abrar kiyi yasa ta dan bugesa batare da tasani ba, cak ta tsaya yayinda zuciyarta ya bada ras! manyan idonta ta zaro batare da tajuyo ba tace
"am sorry please"
aaban shima kasa motsi yayi datayi magana jiyayi kamar yasan wanna muryan "amma a ina?" ya tambayi kansa juyowa yayi yaga har tayi nisa still bai ga  face dinta ba, kafada ya daga irin i dont care dinan  ya fita...

tun daga nesa hanan ke zabga mata harara domin taso kwarai su gaisa da aaban, kunshe dariyarta abrar keyi tace "afuwan bestie hanan"
bata rai hanan tayi tace "ba wani nan gashi kin ja ya tafi baku gaisa"
"ba komai ai zamu gaisa wata rana tun da ana tare" da haka ta lallaba hanan...

haka rayuwa ta cigaba da juya musu da dadi da akasin haka domin matukar ciwon hanan ya tashi tofah basu da sauran kwanciyar hankali, bangaren mummy kuwa alhaji abdur-rauf ya kan zo yayi kwana biyu ya koma, hakan yasa bata yi masa maganar ba amma tasa aranta matukar yazo hutu mai tsayi zata tuntube shi da maganar auren aaban din  kasancewar harkokin kasuwancinsa sun fi yawa a kuwait.

"BAYAN SHEKARU UKU"

wanda yayi daidai da gama karatun su abrar acikin wadannan shekaru abubuwa da dama sun faru ciki har da zuwan hanan sau biyu nigeria, yayinda abrar taki zuwa domin tsoron abinda alhaji shettima zai mata, hanan tayi tayi da ita tabi ta zuwa gidansu taki yanzu dasuke dab da komawa nigeria ciwonta yafi tashi akai akai domin firgice da take kasancewa aciki kullum.

ayau zasu yi taron yaye dalibai, duk wani  dalibi daka gani fuskarsa dauke da farinciki amma, banda abrar dake cikin fargaba hadi da matsananci tsoro...
wurin taron yayi matukar haduwa ga iyaye, malamai hadi dalibai ta ko ina, hanan bakinta yaki rufuwa adalilin ganin daddyn ta cikin iyaye azaune domin bata yi tsamanin zai samu zuwa ba, taron yahadu domin suna gabatar da komai cikin ilimine da sanin ya kamata daga karshe aka kira wanda ya zo na daya a gaba dayan makarantar domin a bashi kyautar karamawarsa, wanda ya kasance dan asalin cyprus din ne, tabass da abrar bata cikin halin damuwa da ita ce zata zo ta daya saboda kwazonta domin har malamai na yabonta, fitowa saurayi yayi cikin murna yayinda iyayensa suka fito aka basu gift din suka yi hoto gwanin burgewa, sai mai gabatar ya kara cewa wacce tazo ta biyu itace "ABRAR SAJEED"....
jitayi kanta ya dau wani dummm domin bata yi tunanin tayi wani abun arziki  da har zata zo ta biyu ba, sai lokacin naga kyawun da abrar ta kara da girma kirarta ta  cola cola ya kara fitowa, brown skin dinta yasake kyau da kyalli ataikace komai nata ya sanja, yanayin jikinta na tafiya da ne da shekarunta, kasanewar yanzu ta shiga shekaru sha tara a aduniya.

asanyaye take tafiya domin har zuciyarta bata ji dadin rashin ganin ammi ba, take mutuwar abbinta ya dawo mata sabo hawaye sun ciko idanunta amma bata basu daman zuba ba, tafi ne ke tashi raf raf ta ko ina a wajen domin nutsuwar ya burge mutane da dama domin kallo daya zaka mata kasan cewa ita din mai nutsuwa ce, cikin sauri hanan ta turawa daddyn ta text msg tace

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now