21

143 9 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓

Written by NoorEemaan

Page41-42

...........ya dau good ten minutes yana tsotsan hannunta yayinda idanunsa ke a lumshe, daga karshe ya dauke ta suka fito, tsadaddiyar wayarsa ya dauka ya daukesu selfie wanda suka yi matukar kyau take ya dora a screen di'n wayarsa, sai ya zamana kana kunna wayar hoton zaka gani baro baro... kwantar da ita yayi a gado ta mike zumbur alamun bata son kwanciyar kenan, ga idanunta sun nuna alamun bacci. "In goya ki?" Ya tambayeta.
Itama sai ta maimaita tambayar dayayi mata, murmushi yayi domin inta maimaita abunda yace hakan hakan na bashi nishadi kwarai, juya mata bayan yayi ta kuwa dane tana kyakyale dariya mai tafe da kuka take yaji ranshi ba dadi domin ta kwana biyu bata wanna kukan ba sai de dariyar, bubbuga bayanta ya shiga da dayan hannunsa yayinda dayan hannu ke tallafe da bayanta, zagaye dakin ya shiga yi da ita, ta dau mintuna talatin kana ya ji jikinta ya saki alamun tayi bacci, kwantar da ita yayi, ya karo gudun Ac din hadi da rufeta da duvet...

"Ni ga kagu bikin nan yazo in dauke kyakyawar Amal dina, wai bikin ma daura kwana nawa?" Dariyar farinciki Amal tayi c kana tace "saura 1week ta gwadawa da hannayenta...

"Allah ya nuna mana domin na kagu, gobe su anty raheenat zasu kawo lefenki, sai kuma yace; yawwa my Amal na tuna shine anyi bikin babban yaya babu ko gayyata sai labari naji?"

Tabe baki tayi kana tace "sweet Adam kayi haku'ri ni wallahi wanna aura dan dai babu yanda zan yi ne dana dakatar da shi domin yarinyar Sam bata yin min ba, gata maha...."

"Haba my Amal wanna wani irin magana ne" ya dakatar da ita, ai yanzu dolenki ki so ta domin ta shiga cikin family dinku wai ma yaushe har kika fara irin wanna halin?"

Shiru tayi tana nadaman maganar a gaban sweet Adam din'ta domin bataso tayi masa laifi saboda tsananin son datake masa, "am sorry" tace domin ta fahimci be ji dadi ba...

Suna cikin haka sai ga Abrar ta fito da gudu tana dariya cikin shigar Pakistan ta zagaya bayan babban mansion din, yayinda Adam ya kura mata idanunsa har sai da ta bace masa, Amal ta cika tayi fam ganin yanda yake bin Abrar da kallon domin ita kam wani tunani ne ya darsu a ranta, kamar zata sa kuka tace "haba mana sweet Adam miye kake wani kallon ta?" Sai lokacin ya dawo da kallon sa kanta yace "is not what you think Amal, yarinyar nan tayi mun kama da kanwar Anty raheenat"... Tabe baki tayi tana cewa
" meye kuma ze hada wanna mad girl din da Anty raheenat?" Be ji dadi sam data ce mad girl ba, dalili kuwa shine ya kasance shi mutum ne me matukar girmama dan Adam ko awani yanayi yake aciki kuwa, amma afili sai yace

"Bazaki gane bamy Amal, kije zan kiraki yanzu gida zan je" fuuuuuuu ta bi hanyar da Abrar tayi, domin ita kam sam bata yarda da abinda yace ba, har wani kishin Abrar din ke tsukarta (kuji ye min Amal fa, meye na wani kishi ita da take matar aure, matar yayanki?)

Da kallon yabi Amal yana girgiza kai ko meye abun fushi? Sai de be ji dadin yadda suka yi sallama ba, yana kokarin shiga motarsa ya hango Aaban ya fito yana waige-waige, fasa tada motar yayi har Aaban ya kara so, hannu ya mika mishi yayinda suka yi musabaha cikin mutunta juna kana Adam ya bashi uzirin cewa baya da matsaniyan daurin auren sa, daga karshe ya masa Allah ya sanya Alkhairi, Aaban ya amsa da ameen kana ya shiga zagaya gidan domin neman inda Abrar ta yi.

Abrar na ta faman tsalle domin so take ta sinko Apple, har Amal ta karosa Abrar bata lura ba, hannun Abrar ta finciko hadi da bata mari sai ta nuna ta da yatsa tace "wallahi daga yau duk ranar da sweet Adam ya zo gidan nan kika fito da shegiyar kafar nan sai ballasu kin dawo gurguwa mahaukaciya kawai" sai ta sa hannu ta murza bakin Abrar da karfi ta rankwasheta a kai, kana ta yi mata wani mugun tura daya sa tayi taga-taga zata fadi... Karaf a idon Aaban daya taho yana kallonsu, cikin zafin nama ya riketa hadi da shigar da ita cikin faffad'an kirjinsa ya sauke ajiyar zuciya ganin bata kai kasa ba, yayinda ya kafe Amal da wani kallon yayinda fuskarsa ke daure tamau...

Amal kuwa bakinta ya shiga karkawa, fuskarta kuwa ya bayyana tsananin tsoron sa, domin bata taba zai zo wajen ba, tama zata ya fita hospital, ahankali ya raba jikinsa dana Abrar, baiwar Allah kuwa bata san me ake ba, ta koma bishiyar ta shiga tsalle, yana zuwa ya daga hannunsa da nufin bata kyakyyawan fari, sai kuma ya tsaya cak da hannun yana kokarin rarrashin Kansa, tunda yake be taba kai hannu kan kannensa ba da nufin duka, ba kuma ya so ya fara a yau, yasani baya dukansu, amma hakan be hana su jin tsoro hadi da girman sa ba...

Cikin wata murya da amonsa ke fitar da tsananin bacin rai dayake ciki yace "Amal! Amal!!Amal!!!, sau nawa na kira ki?"...

Cikin karkarwan baki tace " s...sau...u...u ku"

"Good, daga yau koda da wasa na kara ganin kin yiwa matata kallon bazan bare har ki kai wanna filthy hands din naki kan jikinta, I swear to God how made me, sai karya miki hannu, bace min anan" Ya kara sa atsawace!

Da mugun gudu Amal ta bar wurin tana kuka, ajiyar zuciya ya sauke kana ya nufi inda Abrar ke ta tsallanta, tattausan murmushi yasaki yayinda yake jin kallon ta na tafiya da bacin ransa, hannu ya mika ya tsinko mata wani babban tufa, cikin sauri ta nufeshi tanason karba, sai ya daga hannunsa mai dauke da Amal din sama, tsalle ta shiga yi tana kokarin kamo hannunsa amma ya ki bata damar hakan, itama ta ki hakur'a, ganin ze gajiyar da ita ya sashi sauke hannun ya shigar da ita kirjinsa kana ya nufi bakinta da apple di'n, ahankali ta bude small cute lips din'ta ta ciji Apple di'n, Kansa ya daura a saman kanta yace
"am sorry decent one, so sorry for what Amal did to you".

Shiru kake ji daga bangaren Abrar sai karan taunan Apple din'ta dake tashi, sai data cinye Apple din kana ya riko hannunta suka nufi cikin gida....

Suna shiga suka ga daddy zaune yana kallon sunnahTV, " barka da hutawa dad" yace yana kokarin wucewa
"yawwa barkanmu, Abokina dan zo mana"
Ba musu suka dawo ya zaunar da Abrar kan kujera yayinda shima zauna

"son ya batun lafiyarku India?"

"Tana nan dad, anjima zan je inyi booking flight" Aaban ya amsa wa daddy with full respect.

"A'a abokina, kubar tafiyar nan ba yanzu ba, da kallon mamaki Aaban ya bishi yayinda fuskarsa ke kokarin bayyana damuwa....

Noor Eemaan😉✍

Zuwa dare zan sake baku page 43_44.

SHARE✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now