26

154 11 0
                                    

🍓🍓MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓

written by NoorEemaan

page 51-52

........Har sun fara ta ka matattakalan bene ta ja ta tsaya, kallon karin bayani Aaban ya yi mata, shagwabe fuska tayi tace "Ka tsaya ni pure heart in dauko veil (mayafi) na" jinjina kai yayi fuskar sa dauke da murmushi, mayafi da ya dace da kalan kayanta madaidaici ta dauko kana ta fito suka jera...

suna isa falon suka tarar da Mummy, Hanan, Daddy zaune kan hadaddu'n kujerun falon... Durkusawa Abrar tayi ta kwashi gaisuwa wurin Daddy, cikin kulawa ya amsa mata yana yaba nutsuwarta a ransa, Mummy kuwa duk wani motsin ta yana idonta sai dai a fakaice take kallonta, mutuniyar ta Hanan kuwa sai tsokanar ta dake ta ido amma bata ko kalli gefen ta ba saboda kunyar su mummy...,  shima Aaban ya gaisar da Daddy kana yace su fara ci Abincin domin akwai magana mai muhimman ci....

Babu musu suka mike, manyan manyan warmers  masu kyau da tsada ne akan dinning table, sai dai Abrar ta kasa ko da dago idanunta ne, ballantana tayi tunanin serving dinsu, cikin unquie voice dinshi yace
"serve us decent one"
Kasa ko da kwakkwaran motsi tayi, dago idanunta tayi ta kalle shi fuska a marairace tana nuna masa su Mummy da ido
murmushi yayi yace "idan baki yi serving dinmu ba, zan baki kunya yanzu a gabansu"...

Ba shiri ta dauki serving spoon ta shiga zuba musu... a sake yake cin abincin sa, yayinda Abrar ta kasa cin  ko da cokali daya ne, ta kasan table din Aaban ya zuro kafarsa ya shiga taka kafar ta a hankali, dago kanta tayi karaf suka hada idanu, da ido yayi mata nuni da abincin alamun ta ci,  girgiza masa kai tayi alamun "bata ci" duk da tana jin yunwa amma, kunyar su Mummy take ji, shima bai ci da yawa ba ya ture daman shi ba ma'abocin cin abinci da yawa bane, Mummy na lura da ita tana kuma karantar yanayin ta da dabi'un ta a hikiman ce...

Bayan sun dawo falo sun zauna, Daddy yayi gyaran murya yace "Alhamdulillah dukkanin godiya ta tabbata ga Allah daya bamu ikon ganin wanna ranar, muna miki murnar samun lafiyarki Abrar, muna kuma baki hakuri a bisa auran da aka miki ba tare da sanin ki ba, ina fatan dai Abokina ina nufin Aaban ya fada miki yadda abun ya kasance?" ya fada yana kallonta.

jinina kai tayi kana cikin sanyi murya tace "eh ya fada min"

"toh Alhamdulillah, ina fatan bakya fushi da faruwar hakan?"

"Duk wata diya ta gari mai neman Albarkan iyayenta bata taba fushi da su akan yanke duk wani hukunci da suka yanke mata,  dan haka bana fushi daku Daddy domin na dauke ku tamkar iyayena".... Abrar tace cikin girmama wa surukin ta.

"zallan farinciki ne ya bayyana a fuskar Daddy, bangaren Mummy kuwa a ranta tana yaba iya magana na Abrar, amma sam ba za ka gane akan a fuskar ta ba.

"Masha Allah Allah ya albarkaci rayuwarki" Daddy fada.

"Ameen" tace kanta na kasa

Mummy na shirin yin magana Daddy ya daga mata hannu, domin yasan maganar da zata yi... ya kuma dakatar da ita ne, saboda ya san zata iya yiwa Abrar tambayar ta sigar da bata dace ba, wanda hakan zai iya sa Abrar jin wani iri a ranta.

"Am diyata Abrar ko zaki iya gaya.....sallama Amal da Adam ta katse wa Daddy maganarsa, amsawa duk suka yi yayinda fara'ar fuskar Amal ya dauke a sakammakon ganin Abrar.... bayan gaishe gaishe da ya wakana tsakaninsu, sai a lokacin Abrar tace dasu "ina yinin ku" a yatsine Amal ta amsa kasa kasa shima dan ta ga Aaban ne a wajen, Adam kuwa amsawa yayi cikin zallan mamaki, domin yau da suke kusa sosai yama fi ganin kamanin su da Anty Rahilat, "dole inyi wani Abu a kai"  ya aiyana hakan  a ransa domin yana matukar tausayawa Anty rahilat (Ammi) halin da take ciki....

mikewa yayi ya musu sallama, yayinda Amal ta biyo shi a baya domin raka shi, daman ita ta sa rigima akan ya kawota kasancewar tunda aka yi bikin bata zo gida ba.

bayan  Amal ta dawo ta zauna, Daddy ya yi gyaran murya kana yace "diyata Abrar ko zaki iya fada mana tarihin rayuwarki da kuma in da iyayenki suke?"

gabanta ne ya fadi, yayinda tsohon mikin zuciyarta ya tashi, take zafaffan hawaye ya wanke mata fuska, cikin murya kuka tace "Abbina ya rasu, sai Ammina tana gidan mijin da ta aura bayan mutuwar mahaifina"... jinjina kai Daddy yayi cikin gamsuwa kana yace

"ko zaki iya gaya mana dalilin daya sa kika baro gidanku cikin tsohon dare?"

take ta fashe da kuka domin ta kasa rike shi, tsakanin cinyoyinta ta shigar da kanta ta shiga rera kuka mai ban tausayi, daya taba zukatan wasun su, yayinda Aaban ke jin wani zafi a dalilin kukan ta, shi da za'a biye ta tashi ba zai bukaci jin asalin ta ba, domin  ita yake so ba wani abu da ya shafe ta ba zai iya rayuwa da ita a haka..., take idanunsa suka sanja launin izuwa jaa, lumshe idanunsa yayi yayin da kukan ta ke ratsa dodon kunnen sa....

ta kai mintuna 10 tana kukan babu wanda ya ce da ita ka la, Hanan kuwa tuni ta fara hawayen tausayin kawarta kallon Daddy tayi tace "please Daddy a bani dama in fada nasan komai, bestie baza ta iya cewa komai yanzu  ba"

Wani kallon Mummy ta wurga mata tace "toh iya yi ke aka tambaya?"

Shiru Hanan tayi tana girgiza kanta alamun a'a...

Dago kumburarrun jajayen idanunta Abrar  tayi kana cikin rawar murya mai hade da kuka ta fara da bada labarin asalinta, mutuwar Abbinta, zuwansu Nigeria, haduwar Ammi da alhaji Shettima da aurensu... Sai da tazo dai dai wurin fadin ranar da MIJIN AMMI (wato Alhaji Shettima) ya fara yi mata fyade kukanta ya karu, domin har wani sama sama numfashin ta ke yi, sai da ta kai kusan mintuna sha biyar kyawawa kana ta fara bada labarin komai, da rashin amincewar Amminta, da biyota Cyprus da alhaji Shettima yayi, bayan kammala karatun su da dawowarsu Nigeria, da shigo dakinta da yayi cikin dare, da yanda ta kubuta daga sharrinsa har ta fada hannun Aaban......
Bata boye musu komai ba ta gayamusu

kuka daya ci sunan shi kuka suke yi, har da Amal data dau karan tsana ta daurawa Abrar, Daddy ma duk girmansa kuka yake, mummy ma kuka take domin sosai sautin kukan ta ke tashi,  Aaban kuwa har yanzu idanun sa a lumshe suke yayinda idon sa ke zubar da hawaye, karo na uku kenan da yake kuka domin ita kadai bayan girmansa, jikinsa har wani mugun rawa yake wanda da ace zai  ga alhaji Shettima a yanzu babu abinda zai  hana shi rabi shi biyu saboda wani mashahurin tsanar sa dake ratsa jijiya da jinin jikinsa.

Mikewa Abrar tayi domin gani take dukanninsu banda Hanan di'nta sun tsaneta, ta ma kasa kallon Aaban domin bata son ganin yanayi ko kallon da take  tunanin zai mata, taku daya, biyu ta fadi wani jiri ya dauke ta, duhu ya gilma ta idanunta take ta fadi kasa summamiya....

Comment, vote, share please🙏

editing is not allowed❌❌

Jama'ata ku yi mun afuwa, kasancewar ana ta hidimomin bikin sallah yasa bana baku update da wuri, ga shi na ba ku ba yawa, amma in sha Allah gobe da wuri zan muku posting, ngd da kaunar da kuke nunawa books dina, son so nake muku.💞

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now