9

185 4 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓

Written by noor Eemaan
wattpad@noorEemaan

free book

page17-18

take jikinsa ya fara rawa dan shi kanshi bai san dalilin buguwan zuciyar sa  ba ya dau kusan 20minutes a haka kana cikin dauriya ya cigaba da duba marasa lafiyan bayan ya gama ya kwantar da kansa a table, ya zuro hannunsa acikin locker ya ciro  rigar abrar  yayi matashi dashi tunaninta ne kawai ke kai kawo azuciyarsa yana fatan tana cikin kwanciyar hankali...

"WAYE DOCTOR AABAN"
Aaban abdur-rauf dane ga alhaji abdur-rauf    mai fata da hajiya aisha, auren soyaaya iyayensa sukayi alhaji abdur-rauf dan asalin garin adamawa ne, yayinda hajiya aisha ta kasance shuwa arab aaban shine dan su na fari sai kanwarsa mai bin sa amal sai yar autansu hanan, alhaji abdur-rauf babban dan kasuwa ne domin yana hannun jari a companies yawa masu anan gida da kasar waje haka kuma yana da company's daya mallaka na kansa  suna matukar son yayyansu, amma aaban shine mafi soyuwa agaresu, sun basu tarbiyya daidai gwargwado iyarsu. Aaban gaba daya karatun sa a india yayi ta idan ka cire primary school dayayi anan abuja bayan wasu shekaru yadawo da dinbin nasarori inda yadawo amatsayin babban doctor, domin har can a india sunso rikeshi domin ya musu aiki amma yaki acewarsa yafison yayi aiki akasar sa ta haihuwa wato nigeria   bayan ya dawo alhaji abdur-rauf ya gina masa katafaran hospital,  inda anan yake aiki yanzu ya kuma mallaka masa shi halak malak, amal kuwa tana serving ne yanzu a abia state ta kuma karanci banking and finances ne, sai hanan da take karantar law ayanzu, duk da kasancewar boko ta ratsa su amma sam basa wasa da addininsu, a kuma wanna turban suka dora yayansu a kai, aaban kyakyawa  kuma lafiyayyen namiji ne mai ji da kuruciya, bashida yawan magana ahaka kuma bayason hayaniya baya kuma shiga abunda bai shafe shi ba, bai taba yin soyaaya ba haka kuma bata burgeshi, bai taba nuna damuwarsa akan wata mace ba bayaga mummynsa, amal, da hanan sai yanzu da tunanin abrar ya hanashi sakat wanda ya alakanta hakan da tsananin tausayinta ne... (LABARIN AABAN ATAKAICE KENAN)

yanzu gaba daya abrar ta dawo so silent kwata kwata bata magana kullum daki take wuni daga ta sha su yoghurt sai lemuka suma sai taji yunwar ta isheta ne kuma yanzu koda wasa bata barin kofarta abude koda da rana ne kuwa, bata da aiki daya wuce kuka domin kullum idanunta basa rabuwa da kumburi, ada har tana cewa bazata koma school ba amma yanzu ta gwanmace ta kuma cyprus ko ta huta da wanna gidan data yiwa lakabi da "bakin gida"....

a yau abrar zata koma cyprus tun karfe shida ta shirya domin flight dinsu karfe takwas zai tashi, burinta kawai taji ta bar gidan duk da tasan zata yi matukar kewar amminta tana kuma fatan watarana ammi ta fahimci gaskiya, da gari ya dan yi haske domin har bakwai da kwata tayi abrar ta fito sanye da turkish abaya red color sai ta yana kanta da mayafin abayan sai black wage shoe dake sanye akafarta duk da tayi rama amma hakan bai hana sihirtaccen kyawunta fitowa ba, yan kayan dazata tafi dasu kuwa tuni daya daga cikin ma'aikatan su kai mota, tana tsaye awaje domin driver yace alhaji yace su dan tsaya can sai ga alhaji da ammi sun fito, kallon ammi take tun daga nesa, cikin tafiyar nutsuwarta ta taka zuwa wajenta dan nesa da ita ta tsaya tace
"amminaaaa" 
ammi kuwa jitayi wani abu ya taba zuciyarta, saurin dago kanta tayi taga abrar na sakar mata murmushi yayinda hawaye ke zuba a idanunta, itama ammi kwalla sun ciko idonta amma bata basu daman zubowa ba, ware hannunta tayi alamun abrar tazo cikin sauri ta karosa ta rungumi ammi hadi da fashewa da kuka sai tace "ammi zan tafi kisamun albarka" ta fada cikin sheshekan kuka, hawayen daya zubowa ammi tayi saurin sharewa kana tace"kina tare da albarkata akodayaushe Allah ya bada sa'a" tana fadin hakan ta koma cikin gida domin wani kuka ne ke kokarin kufce mata....

da kallon kauna ta bi amminta kana ta nufi   mota, sai ga alhaji shettima ya tari gabanta hadi da cewa"my sweet abrar, zanyi kewarki sosai, anya zan iya hakuri ki dawo kuwa? kinga ya kamata ki kwantar da hankalinki ki bani dama da hadin kai dan in cigaba da dandana zumarki, ina mai tabattar miki ko nawa kikeso, ko  mikike so aduniyar nan ni alhaji shettima zanyi miki shi, yakamata ki more rayuwarki domin har yanzun ke karamar yarinya ce kuma kada kiyi tunanin  amminki zata taba yarda cewa ni na kusance ki koda kin gaya mata dom......" saurin dakatar dashi abrar tayi cikin tsanarsa haushinsa hadi da kyamarsa tace "an dai ji kunya tsahon najadu kawai, mugu, kana tunanin kazamin hannunka zai sake taba jikina?  toh bazan kara barin hakan ta faru ba koda zan rasa raina kuwa kuma in sha Allah sai kaga yanda karshenka zai kasance" tafada cikin muryan kuka kana ta shige cikin mota driver yaja suka tafi....

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now