14

174 7 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓

written by noor Eemaan
wattpad:NoorEemaan

page27-28

cikin sauri ma'aikatan suna shiga duba ko wani lungu da tsakon gidan, shima alhaji shettima ba'a barshi abaya ba har da shi ake neman nata, bayan sun duba ko ina basu ganta ba suka sanar da alhaji cewa bafa ta cikin gidan, cikin wani tashin hankali yafara tunanin ina taje? can sai ya kalli mai gadi babu alamun wasa yace
"kodai ka bude mata gate ne?
murya na rawa mai gadi yace "wallahi tallahi alhaji ban bude mata gate ba" domin shi kam be shirya rasa aikinsa ba...
"Toh acikin ku waye yaji fitar ta?"
shiru duk sukayi sai daya daga ciki yace

"ni dai alhaji ina kwance adaki naji an diro kasa, amma ban leka ba"

Cikin takaici alhaji shettima yace kwada masa mari yace"shashashan banzan da wofi meyasa baka lekan ba?" domin alhaji shettima ya fahimci cewa lada ta hau ta dira kasa, tunda me gadi be bude mata ba domin babu wata hanyar agidan, adaran nan yasa dukkansu banda megadi baza nemanta, shima mota ya hau ya bar gidan...

Duk inda suke tunanin zasu ganta sun duba amma ko alamarta babu, har karfen bakwai din safe suke nemanta, dasuka gaji kawai ya kira su kwaro yace duk inda suka ga abrar su kawo masa ita tunda sun santa ya kuma yimusu alkwarin basu kyauta me tsako, domin shi be shirya  asirinsa ya tonu ba, domin ana ganin mutuncinsa agarin na abuja sosai,  da wanda ya nufi gida...

Bangaren ammi kuwa gaba daya ta fita a hayyacinta kuka take sosai, kukan nadama akurarren lokaci, "wani hali abrar take yanzu?" shine tambayar dake kai kawo aranta, gashi tana rufe balle tasamu ta fita ko Allah ze sa tayi dacen ganin yarta, tana cikin wanna tunanin taji an dan bude kofar hadi da tura mata plate din abinci kafin ta taso an rufe kofar...

"Waye nan? wanene dan Allah abude min inje neman yata"...

dariyar alhaji shettima taji yace "hajiyata ki kwantar da hankali, ana kan nema miki yarki, sai dai kisani idan an ganta wani gidan daban zan kaita in cigaba da lasar zumanta domin bazan iya barinta ba,  za kuma ki cigaba da zama anan dakin har a ga abrar, karki damu zan dinga turo miki abinci kullum"...

cikin kuka ammi tace "Allah ya isa tsakanina da kai, sai ka wulakanta aduniya, idan ka isa ka sake ni na bar maka gidan ka, domin gidanan tamkar kuzurmin daji haka nake ganinta"

"hhhh hajiyata kenan ina raga miki ne saboda son hadi da sha'awar da nake wa abrar daba haka ba... sai ya ja kwafa hadi da barin wurin.

da misalin karfe hudun yamma zaune suke a babban falon gidansu su duka ukun yayinda mummy ta kalli hanan dake faman danna waya rai abace tace "ke kam hanan me damuwarki ne"
"tambayeta mummy ta damu mutane da tsaki" amal ta fada tana harararta.
turo baki tayi tace "mummy ki raba  ni da anty amal"
"ke ni ba wanna na tambayeki ba, meke damunki?"
"number amminsu abrar nake ta kira baya shiga, gashi inason zuwa gidan".

mummy na shirin bata amsa suka ji wani razananan ihu da sautin sa ya karade duk ila'irin mainson din nasu, kallon kallo aka shiga yi tsakanin mummy, hanan, amal, yayinda suka mike atare suka nufi bangaren aaban domin tabass ta nan wanna ihun ke tashi, suna kokarin hawa matattakala sai suka ji dariyarta na tashi sosai can kuma sai kuka  gaba daya suka rugo aguje suka dawo falon har da mummy kuwa😅 kukan ne ya shi gaba da tashi yayinda suka zauna jugum cikin rashin sanin abunyi, dadinta daya yau aaban da wuri ze dawo, take ciwon abrar ya fadowa hanan, domin irin ciwon abrar ne wanna patient din ya aaban keyi amma nata be kai wanna ba, sun kai awa daya awanna halin kana suka ji tsayuwar motar aaban ajiyar zuciya suka sauke, yana sallama yabi su da kallon mamaki se dai be tambaya ba, be kuma nuna afuska ba, "yawwa son welcome home, ga patient dinka can tana kuka  hadi da dariya kaje ka duba awani hali take ciki"..

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Onde as histórias ganham vida. Descobre agora