33

168 5 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMI NA NE SILA🍓🍓
(A heart touching story)

written by Noor Eemaan
wattpad username @NoorEemaan

Juma'at Mubarak to you all my lovely fans, Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke.😘

Page 65-66

_________________📖 "tabbas wanna shine mutumin dana kai wa takardan sammaci ba jimawa gidan sa, toh meya fito yi dashi, ga yanayin sa ya nuna bashi da gaskiya"  matashin ya fada a ransa yana kallon alhaji Shettima da ke cikin halin azaba, sam baya fahimtar kowa da komai.

Babur din sa ya bawa wani mai shago  ajiya kan cewa zuwa dare zai zo ya dauka, kana ya tari mai adaidaita sahu, suka kama Alhaji Shettima aka sa shi ciki dan sahun kana suka nufi asibiti....

Direct emergency aka kai shi, suka yi treating ciwon nasa, kana suka kai shi dakin hutu, matashin nan mai suna Mansur kuwa direct gidan alkalin da case din ke hannun shi ya nufa domin sanar da shi halin da ya tsinci alhaji Shettima, kana ya bashi jakar takardun da tsinta a tare da shi....

Jinjina kai alkhali yayi domin a matsayin sa na alkhali ya fahimci wasu abubuwan...take ya bada umarni aka zuba yan sanda ciki da wajen asibitin domin gadin alhaji Shettima, haka alhaji Shettima ya kai kwana ki goma sha biyar cikin asibiti wanda zuwa lokacin ya fara taka kafar tasa.
police station aka kai shi sai da ya shafe kwanaki 5 Cikin cell wanda ba karamin azaba ya sha ba....

"RANAR SHARI'A"

Kotun cike yake da su, Abrar, Aaban, Hanan, Amal, Adam, Ammi, anty Raheenat, yaya Nadeem, mama, baba, (wanda yanzu ya ji sauki jikinsa) Mummy, Daddy.

Ta wata kofar a shigo da alhaji Shettima gaba daya ya sake fita hayyacinsa babu kyawun gani, tumbin sa yayi kasa alamun babu sauran jin dadi da Hutu, kansa na kasa kunya mai yawan gaske na saukar masa...

Nan mai gabatar wa ya karanto laifi Alhaji Shettima, domin su Aaban basu dauki lauya ba haka alhaji Shettima... Gyara zaman gilashin sa mai shari'a  yayi kana ya ce "alhaji Shettima ana tuhumar ka da yi wa Abrar diyar matar ka fyade, shin kana da ja ko ka aikata?"...

Shiru kotun ya dauka baka jin motsin komai sai sautin kukan Abrar dake tashi sosai, saboda tuno komai da ya faru, Aaban dake gefen ta ya kasa cewa komai saboda yanayi da yake ciki...

Sun dauki mintuna biyar kyakyyawan ba tare da alhaji Shettima ya ce komai ba, haka kawai yaji bakinsa ya kasa motsi, cire gilashin sa mai girma mai shari'a yayi, domin baro baro alamun rashin gaskiya ya bayyana a tattare da alhaji Shettima, kallon shi yayi na yan mintuna  kana Cikin hikima ga shiga gaya masa illar zinah hadi da azaba mai tsanani da rabbul samawwati ya tanadar wa duk wanda ya aikata zina kasancewar mai shari'a na da ilimin addini mai zurfin gaske....

Abun mamaki jikin alhaji Shettima yayi wani sanyi kalau, sai yanzu nadama hadi da matsanancin kunyar gamuwan shi da Allah ya saukar masa...

Dago kansa yayi yayin da muryan sa na rawa gwanin tausayi yace " ya mai girma mai shari'a duk abinda kace, nina aikata su, da kaina nayi wa Abrar fyade, yarinyar da zan iya haifa a cikina, hakika na cutar da Abrar da ma Rahilat... Ya karasa yana zubewa kasa yayinda wasu zafaffan hawaye suka zubo masa gwanin tausayi, shi kanshi bazai iya tuna when last da yayi kuka a duniya ba....

"Alhamdulillah! A bisa rashin wahalar da kotu da baka yi ba, kotu ya yanke maka hukunci kisa ta hanyar jifa, har Allah ya karbi ranka, haka Allah ya yanke hukunci wa duk wanda ya aikata zina, alhalin yana da aure, don haka hukunci ka kenan, Allah zai yafe maka wanda laifi daka aikata na zina matukar aka jefa ka ta hanyar jifa, ko da a ranar tashin alkiyama, ubangiji bazai tuhumeka kan wanna laifin na zinah ba Allah ya tsare imanin mu"

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ