25

175 8 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓

Written by NoorEemaan

page-49_50

a hankali ya mirgina sai ya zama na tana kasan sa yayinda yayi mata rumfa da faffadar kafadar sa, ido cikin ido yake duban ta haka itama .....tsawon mintuna 15 suka dauka ba tare da sun ko kyafta idon su ba. ita tayi karfin halin janye idanunta yayinda yanayinta ya canza lokaci guda... mirginawa gefe yayi cikin Damuwa yace
"menene wiffy?"
"Ammina!" tace idanun ta na ciko da kwalla.

"ina take?" yace yana goge mata hawayen da ya fara sauka kan kyakyyawar fuskarta.

"Ta...tana gidan Shettima"
"waye Shettima?" ya tambayeta.

Wani abu mai daci ta hadiya tace "Mijin Ammina"

dan zaro ido yayi yace "shine kike kiran sunan shi"?

murmushi mai ciwo tayi kana tace "a haka nayi masa adalci dana kira asalin sunanshi"...

cikin daurewan kai yace "decent one ban fahimci abinda kike nufi ba, i thought mijin ammi ne, he deserve some respect from you"....

kuka mai matukar ciwo ta fashe da shi jikinta har wani rawa yake, take hankalinsa ya tashi domin sam kwakwalwarta baya bukatar damuwa da duk wani tashin hankali, cikin lallashi ya dora ta a kirjin sa yace "it's ok decent one, mu bar maganar nan yanzu, za mu yi ta wani lokacin"

luf tayi a kirjin sa tana sauke karfaffar ajiyar zuciya. "mu tafi gida dan Allah" yaji saukar muryar ta.

"zamu tafi cikin satin nan kinji" jinjina masa tayi tana kara zagaye shi da hannunta hadi da kara rungumar sa, domin haka kawai taji ya kwanta mata a rai, wanda bata san dalili ba, amma tana ji a jikin ta cewa shi din na daban ne.... bangaren Aaban kuwa ba haka yaso ba, yaso su dan kara kwanaki a garin shi da decent one din shi ko dan su kara samun fahimtar juna, amma tun da ta bukaci su tafi dolensa su tafi domin yafi bukatar farincikin ta fiye da komai......

*NIGERIA*
a hankali suke taka matattakalan benen jirgin, hannuwan su cikin na juna, sanye Abrar take da pakistan red color da mayafinsa, hannuwanta awarwaro ne masu kalar ja, kunnenta sanye da fashion din dan kunne mai dan tsayi baki masu stone, kafarta na sanye da black shoe mai dan tsini amma ba sosai ba,... duk da ita ba fara bace amma sosai tayi kyau domin kayan sun karbi jikin ta kwarai, Aaban kuwa sanye yake da pencil jeans baki da jan riga da aka rubuta "MY WOMAN" da manyan aruffa, kansa akwai P-cap yayinda fuskarsa ke rufe da glass da ya yi matukar karban fuskar sa, kafarsa kuwa sanye take da takalmi sau ciki baki, agogon zallan azurfa ne ke kwance kan lafiyayyan farar fatar sa, sun yi matuk'ar haduwa sun kuma dace kwarai da junan su...

kasancewar bai sanar da cewa gida cewa yau zasu dawo ba, ya sanya babu wanda ya zo tarban su, taxi ya tsayar suka nufi gida... Abrar kuwa jikinta ne ya yi sanyi sosai domin bata san ya halin yan gidan su yake ba, shine Mahaifiyarsa za ta karbeta amatsayin suruka? da kuma tunanin ammi da dai sauran tunani sune suka haifar mata da sanyi jiki....

Kura mata ido ya yi sonta mai zafin gaske da matsananci tausayin ta na ratsa shi, ko dai dai da second daya baya son ganin damuwa shimfud'e kan kyakyyawar fuskarta hakan yasa shi cewa janyota jikinsa "bana son ganin damuwar ki, please ki daina tunani kinji?" ya fada idanunsa kafe kanta...

"toh na daina" ta fada hawaye ya zubo kan fuskarta, kamo fuskarta yayi cikin lallausan tafin hannunsa ba tare da ya ko kalli driver ba ya fito da harshensa ya shiga lashe hawayen fuskarta... shiru tayi tana kallonsa yayinda take jin wani son sa na ratsa jininta, shi din na daban ne, haka komai nasa ma special ne, murmushi ta sakar masa tana kokarin daidaita yanayinta, duk dan ta kwantar masa da hankali domin ya cancanci fiyeda haka, hannun sa ta zame daga fuskar ta ta kwantar da kanta kan kafadar sa tana sauke ajiyar zuciya...

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now