22

147 6 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓

Written by NoorEemaan

page 43-44

Murmushi daddy yayi domin ya fahimci tunanin daya darzu a ran Aaban, cikin zolaya yace  "angon Abrar ba abinda kake tunani bane, ina nufin tunda bikin kanwarka Amal saura sati daya ya kamata ka tsaya a daura auren da kai, Allah basshi washegarin daurin auren sai ku tafi, tunda ba'a san tsahon lokacin da zaku dauka a can ba"...

Ajiyar zuciya ya sauke, kana yace " Ok  Dad zanyi hakan " ya kara sa maganar yana Sosa kansa...da kallon kawai daddy ya bishi yana murmushi

"Assalama alaykum"
Sallamarsa ta karade dakin, amsa wa ammi ta yi tana murmushi tace "Adam har ka dawo daga zancen?" Ammi tace cikin tsokano domin zamanta a gidan, yasa shakuwa mai yawa shiga tsakaninsu domin sai kayi tunanin tayi shekaru masu yawa a gidan, kuma sosai yake debe mata kewa rashin yarta, duk da in ta kadai'ce takan yi kuka, kukan nadama, kukan rashin baiwa maganar yarta muhimmanci, babban abinda yafi damunta dare da rana shine a wani hannu yarta take? a hannun nagari ko akasin hakan? Duk yaya Alkasim mahaifi ga Adam da yaya Nadeem na matukar kokarin wurin bincike inda take...

"Eh antyna na dawo, ina anty raheenat take suka bar ki kedai?" 

"Suna part di'n mama wato (mahaifiyar Adam)" har ya budi baki ze tambayeta sai kuma yayi shiru gudun kada ya tayar mata da mikin da ke ranta.

"Antyna bara na je part din mama zan dawo"

"Toh Adam sai ka dawo" ammi ta amsa.

Yana shiga part din Mama ya gansu zaune ita da yaya raheenat suna hira, bayan gaishe'n su dayayi sai yace
"anty raheenat wai yar anty rahilat data bata suna kamasosai ne?"

Kallon juna mama da yaya raheenat sukayi kana anty raheenat tace "eh toh suna matukar kama a lokacin da take da kananun shekaru, amma yanzu ban saniba ko yanayin fuskarta ya sanja, amma meyasa ka tambaya Adam?"...

" Wato dana je gidansu Amal naga wata mai kama da anty Sak, babamcinsu kawaivyawan shekaru da anty ta fita"

"Adam kenan sau nawa ana samun masu kamanin da yawa kuma babu wata dangantaka dake tsakaninsu? kuma banda abinka meye zae kai yar Rahilat gidansu Amal? Kuma ina fatan baka fadi wanna maganar Rahilat taji ba ko? Domin kada hankalinta ya sake tashi"... Mama yafada tana kallon Adam

" eh ban gaya mata ba"

"Yawwa kada ka bari ko da wasa taji, kila wata yar'uwar su Amal din ce, kada kazo baka da tabbacin Abu ka tayar mata da hankali, muna kokarin kwantar da hankali ta"

"Toh mama" yace domin yasan baza su fahimce shi  ba, shi ya ganta da idanunsa tsananin kamarsu  ya wuce ace kawai kamanin ne ba wata karfaffan alaka a tsakaninsu, yana kuma fatan idan sun je kai lefe su ganta suma, hakan zai sa su gasgata maganarsa....

Yau ya kasance ranar dasu ammi zasu kai lefen gidansu Amal, motar har biyu ce ta debi kayan yayinda su yaya raheenat, ammi tare da wasu yan'uwan mama ke wata motar daban, motocin sun tashi uku kenan.

Horn driver's din gidansu Adam suka danna, babu bata lokaci aka wangala musu yalwataccen gate din kasancewar an san da zuwan su, bayan sun faka motocin, kana driver's suka shiga fito da akwatunan suna shigar da shi cikin gidan sai da suka shigar da akwatunan duka kana su ammi suka shiga ciki, yaya raheenat ce agaba yayinda ammi ke baya da ita, sai sauran matan da suka biyo baya...

Sosai su mummy da mutanenta suka tarbe su cikin mutunci, mummy tadan yi mamakin ganin tsananin kaman da ammi da Abrar ke dashi amma bata kawo komai a ranta ba, akwatunan ba karya sun hadu,  guda ashirin da hudu ne, hadi da kudi har million uku, bayan duk sunyi abinda ya dace suka mike domin tafiya,  mummy ta basu tukwuici million biyu, haka suka rabu cikin mutunta juna, bayan sun fito duk sun shige motar saura ammi dake kokarin shiga, kamar ance to waiwayo ta hango Abrar zaune ta bata baya, yayinda wani kyakyyawan matashin saurayi ke yi mata yankan farce, haka kawai ta ji tanason ganin wanna budurwa har ta fara takawa taji yaya raheenat tace
"Rahilat ina zaki? Ki shiga mu tafi mana".
Bata ce komai ba ta shiga motar, sai lokacin tunani yazo mata, ita yanzu data nufi wajen su mezata ce musu? Tunda bata san su ba, suma ba saninta suka yi ba...

Bayan kwana biyu aka fara bikin Amal wanda suka fara da bridal shower, kamu, dinner,  sai mother's eve, duk wani anko da akayi, sai da Hanan ta tabattar Abrar tayi domin har dinki iri daya ta musu, sedai Aaban yace bazata je ko wani event ba, dalilinsa kuwa shine bayaso ko da wasa awulakantata, ko wata ta gaya mata ba dadi, yasani cewa bata cikin hankalin ta amma matukar aka haiba tata har zuciyarsa yake jin ba dadi, Hanan tayi rokon duniyan nan ya ki, har alkawari cewa tare zaku zauna waje daya amma yaki amincewa. Saboda yasani ciwonta ze iya tashi a ko wani lokaci, hakan ze iya sawa wasu mutane su fadi wata kalma mara dadi akanta wanda shi bazai ji dadi ba, ba kuma zae jure ba, ya kuma san cewa da maza a wurin, shi bazae bari wani namiji ya kalle masa mata ba domin yana tsananin kishin'ta fiyeda zaton mutum, da wadanan hujojin ya ki bari Hanan ta kaita...

Washegari aka daura auren Amal da Adam wanda dubban jama'a suka shaida, da yamma aka kai Amal gidanta da babu wani nisa tsakanin sa da gidan su Adam, Amal tasha kukan rabuwa da su Mummy, Hanan ma tayi kukan rabuwa da yayarta sosai ....

Washegari kuwa babu bata lokaci Aaban yaje booking flight sae de be samu direct zuwa India ba, a Syria jirgin ze tsaya haka yayi booking domin bayaso ko dan ya sake daukan lokaci basu tafi neman lafiyarta ba...

Yana shiga part dinsa, ya ganta kwance tana bacci,  jikinta rabi a kasa rabi a gado, gyara mata kwanciyar yayi ya bata kyakyyawan Sumba a kumatun ta, kana ya bude wardrobe dinsa, take idanunsa suka sauka kan sadakinta wanda naira na gugan naira har million daya, "zan cigaba da ajiye miki su  har ki samu lafiya domin hakkin ki ne" ya fada yana waiwayonta hadi da sakin murmushi... Sai kuma ya Dan daki kansa yana cewa
"mekake yi haka ne Aaban? kai kadai kana magana". Sai kuma ya girgiza kansa yayinda fuskarsa ke dauke da murmushin still, kayan dayasan zasu bukata ya hada awani madaidaicin jaka domin a tsarensa bayasan tafiya da kaya masu yawa musamman in tafiyar ta kasance mai nisa ce....

Washegari karfe goma dai dai ya gama shirya ta, cikin abaya maroon color dayayi matukar karbanta, yayinda shi kuma ke sanye da kananun kaya masu kyau da tsari, saukowa kasa suka yi,  su Mummy na zaune suka jiran fitowarsu, tun daga nesa Mummy ke kallonsu, yayinda ta kasa gane yanayin da take ciki, duk inda ake neman ma'aurata da suka dace da junansa to indai an samu su Aaban an gama domin haduwarsu da dacewarsu na daban ne, bayan ya gaishe da mum and dad, Hanan ma ta gaishe shi, babu bata lokaci gaba daya suka mike domin yi masa rakiya...

Mummy tayi masa fatan sauka lafiya hadi da add'ua domin haka kawai ta ji jikinta yayi sanyi, daddy ma yayiwa Aaban fatan Alkhairi, da ameen duk ya amsa kana ya rungumi iyayansa cikin kaunarsu...

Hanan da idanunta suka ciko da kwalla ta rungume Abrar tace
"Allah yasa adace bestie Abrar, ki dawo mu cigaba da rayuwar mu yanda muka saba, nayi missing duk lokutan da muka kasance ciki a Cyprus" Hanan ta karasa maganar wasu hawaye na zubo mata.

Abrar kuwa shiru tayi kamar tana fahimtar abinda Hanan ke cewa, sai kuma tasa dariya mai tafe da kuka, tana kallon Hanan , bubbuga bayan Hanan Aaban yayi alamun rarrashi kana ya riko hannun Abrar suka shige motar driver ya ja suka bar gidan...

Bayan sun isa airport babu bata lokaci jirginsu ya daga zuwa sararin samaniya, kowa cikin jirgin harkan gabansa yake yayinda Hannun Abrar ke cikin na Aaban  duk da tana kusa dashi amma hakan be wadace su ba sai da ya rike hannun, sun dan yi tafiya mai nisa sai kawai yaji  ta fara dariya, sai kuma kuka ya biyo baya, hankalin jama'a ne ya fara yo Kansu, a karon farko ya hade bakinsu......

In Allah ya amince, gobe ma zan muku posting sae dai zaku ji ni ba da wuri ba.

Share✔
Vote✔
Comment✔
Edit❌
https://chat.whatsapp.com/FEfWeTiufpk96my8yNBeaM

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now