32

170 10 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓
(A heart touching story)

Written by NoorEemaan

page 63-64

(not edited)

______________________📖 zaro ido Ammi ta yi cikin kaduwa hadi da mamakin ganin Ummi acikin wani matsanancin yanayin.

"Zulaihat me ya sa mu Ummi haka?" Ammi ta tambaya tana bin Ummi dake kwance da kallo cikin halin matsanancin ciwo....

"Hakkin ku" Zulaihat ta ce idanunta cike da kwalla

Cikin sauri Ammi ta durkusa gabanta tana cewa "Ummi!" Kura wa Ammi ido Ummi ta yi yayin da bakinta ya fara motsi alamun zata yi magana, amma ta gagara furta komai...

Cikin tausayawa halin da Ummi take ciki Ammi ta share kwalla, wai yau Ummi yar gayu, mai ji da dukiya ce kwance cikin wanna matsanancin halin?...

"Zulaihat Baku kai ta asibiti ba ne?"

"Anty Rahilat na gaya miki cewa hakkin ku  ke bibiyar Ummi domin babu irin asibiti da bamu je ba, babu kalan maganin da bata sha ba, amma babu wani sauki, ta kai kusan shekaru bakwai cikin wanna halin tun tana iya cewa a nemo mata ku ta nemi yafiyar ku har ta ma daina magana sai dai kawai ta bi mutum da kallo....

" innalillahi wa Inna ilaihi raju'un " Ammi ta ce tana kuka, domin duk mai imani dole ya tausayawa halin da Ummi ke cik, domin wani mugun rama tayi baka ganin komai sai  kashishuwa.

"Ku zauna bayin Allah" ki jin Zulaihat.

A sanyaye duk suka zauna, domin suma sun tausayawa halin da take ciki.

Ruwa hadi da drinks Zulaihat ta kawo wa mu sy, kana ta zauna, aka gai gaisa jiki a sanyaye...

"Jikin Ummi ne ya fara rawa yayinda bakin ta ya cigaba da motsi, cikin mamaki Zulaihat ta ce " ya rabb! Yau Ummi ke kokarin tashi bayan tsahon lokaci?" Ita kanta bata san maganar ya fito fili ba...

"Daman ta jima Bata motsa komai nata?" Ammi ta tambaya hankali tashi.

"Hmm anty Rahilat, ai Ummi ta kai wasu shekaru a haka bata ko motsa jikinta fa" inji Zulaihat.

Cikin sauri Aaban ya tashi ganin matar na ta kokarin tashi, tabbas a matsayin na doctor ya fahimci cewa matar na da karfin hali da karsashi, domin tana cikin ciwon sosai kuma take kokarin tashi...

A hankali ya daga ta zaune, ya dora mata pillow data kwanta a kai kan gadon bayan ta domin ta ji dadin zaman, kuma ikon Allah ta zauna yayinda idanun ta ke kafa kan mutane biyu "Ammi da Abrar"...

Wasu tagwayen numfashi ta shiga saukewa wanda kai tsaye mutum zai fahimci cewa na azaban ciwo ne...

" R...ra..hi...la...t  ki... ya...fe...fe...min Ha...ki...ka... Ban...ri...ke Ama...nar ...sa..jee..d... ba.." Ummi tace baki na rawa domin maganar ma da kyar ta fizgo shi...

Kukan mai sautin gaske Ammi ta sa, lallai bawa ba'a bakin komai yake ba, haka zalika duk wanda ya dauke tsananin son duniya ya dora a kanshi yana cikin matsala babba kuwa, ga misali nan kan Ummi .

"Ki...kin...ji...? I...ina ....ji...ka...ta? "

Cikin kuka Ammi ta riko hannun Abrar dake zubar da hawaye itama zuwa gaban Ummi, meya ribar ta idan taki yafewa Ummi? Ko iya haka, ai ta ga ishara tun a gidan duniya, duniyar ma nawa take da wasu mutanen ke daukan ta da zafi, har su sabawa Allah...

"Ni na yafe miki duniya da lahira" inji Ammi.

Sannan ta kalli Abrar tace "diyata ga kakar ki nan, shin zaki iya yafe mata?" Ammi ta tambayi Abrar cikin sigar tambaya.

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now