19

159 9 0
                                    

🍇🍇 MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓
(A heart touching story)

written by Noor Eemaan✍😊

Page 37-38

Mummy bata damu da yanda taga Abrar na gudun ta ba, ta kamo hannun Aaban tace "son na yarje mana auren ta, amma akan dalili daya tak, matukar ta dawo hayyacinta yanayin nutsuwarta be mun ba toh dolenka ka kara aura, kasani cewa babu wata uwa a duniya komai lalacewarta dazata so dan cikinta ya auri macen da bata tare da mutuncinta, amma na yarda da kaddara ina muku fatan Alkhairi" tana fadin haka ta sa hannu ta share kwallar daya zubo mata...

Murmushin da har jerarrun fararen hakoransa suka bayyana yayi kana ya bawa mummy wani Sumba mai tsayi a goshinta kana cikin muryansa dake bayyana halin zallan farincikin dayake yace

"thank you so much mum na yarda da sharadin ki"

tsalle hadi da ihun murna Hannan ta daka ta rungumi mummy cikin farinciki, mummy ma rungumeta tayi batare da tace komai "mummy ina me tabattar miki sai kin yabi halin Abrar da bakin ki is just a matter of time, but mummy please ki bani dama na fada muku dalilin daya sa Abrar shiga wanna halin"...

"Zanso jin hakan ko hankalina ze kwanta da wanna auran, amma ba ke nakeson ki gayamin ba, ita Abrar din nakeson jin komai daga bakinta"...

"but Mummy... bazata iya yin wani bayani ba, domin bata a cikin hankalinta yanzu" Hanan tace cikin damuwa.

"Nasani, zan jira ta samu lafiya, kuma matukar naji dalilinta be gamsheni ba, ko kuma da amincewarta hakan ya faru toh dole dana ya rabu da ita, domin yanmmata na irin haka da amincewarsu za'a keta musu mutuncinsu daga baya su fake da cewa fyade aka musu ko kuma kaddara ce ta fada musu".... Mummy na gama fadin haka ta bar wajen cikin yanayin da suka kasa ganewa, Amal dake cike da jin haushin amincewar da mummy tayi da aura ta bar wajen...

Daddy murmushi yasaki, murmushin so hadi da alfahari da matarsa domin yasan fadan da yayi mata ya yi matuk'ar shigar ta...

Yayinda su Aaban suka bi Mummy da kallon suna kuma saka ran zata sauko gaba daya musamman idan ta fahimci wacece asalin Abrar...

Daf da kunne daddy Aaban yace "dad please ka aura min ita da wuri, domin in kula da ita, gashi inason fitar da ita India a sati nan" yana gama fadin haka ya ja hannun Abrar suka bar wajen fuskar nan ba alamun wasa kai baka ce shi yayi wanna maganar ba"...

Dariya daddy yayi kana girgiza kai, tabbas soyaayya ko yace mace kan sanja namiji, be taba tunanin cewa Aaban ze iya wanna rudewar kan mace ba, amma adalilin ta har magana me dan tsayi take yi sabanin da, ze fara sanar da yan'uwansa duk da abun yazo a kurarren lokaci, amma zesa abuga kati tunda yau talata sai su sa ranar daurin auran ya kasance ranar asabar da Wanda tunanin ya mike domin yana da appointment da wani abokin kasuwancin sa nan abujan....

Sai lokaci Hanan tace "daddy me ya Aaban ke rada maka akunne dazu"

"Je ki tambayeshi mana, ya baki amsa" Daddy yace yana mata hararan wasa...

Zaro ido tayi tace "ni Daddy! ya Aaban ya balla ni"

Dariya daddy yayi sai yace "wato ni kika raina ko?"

"A'a Daddy kayi haku'ri " ta fada itama cikin dariya...

Daddy na fita ta haura saman Aaban domin so take ta taya shi murna sosai...

Zaunen yake a gabanta ya k'ura mata idanunsa kamar ko yaushe, yayinda fuskar'sa ke fitar da wani murmushi da shin kanshi be San yana murmushin ba, imaging kawai yake gata ta samu lafiya suna shimfuda soyayyarsu, a yau jinsa yake a farinciki mara mitsaltuwa, burinsa ya cika mummy ta amince yanzu fatansa daya Allah ya bata lafiya ya nuna mata zazzafan kaunar dayake mata...
Abrar kuwa sai wasa take da wayarsa ta juya ta nan ta juya ta can bata ma San yanayi ba...

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now