27

177 4 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓
(A heart touching story

Page 53-54
........salatin da su Mummy suka sanya ya sa shi saurin bude idanunsa, hankali tashe kana kuma a firgice ya nufi ta, cikin zafin nama ya manna ta da kirjinsa yayinda zuciyar sa ke wani mahaukacin bugu, hawaye ke zuba kan kyakyyawar fuskar sa, duk jarumtar sa ya kasa daurewa, saboda tsananin tausayinta, daga karshe ma fashewa yayi da kuka mai sauti, ya kara kamkame Abrar a kirjinsa, gaba daya ya rasa abinda zai yi domin kwakwalwar sa ta tushe.....

Cikin karfi hali Daddy yace "abokina me kake yi haka ne? Ka bata taimakon gaggawa mana"

Sai a lokacin yayi tunanin hakan, da mugun gudu yayi hanyar saman bene ya dauko box din treatment din sa, kwanatar da ita yayi kan kujera three seater yayin da ya shiga bata taimakon gaggawa hawayen fuskar sa ya gagara tsayuwa....

Amal kuwa matsanancin nadama ne ke cin zuciyarta, ta kasa tsayar da hawayen fuskar ta, haka zalika Mummy son Abrar, tausayinta, dama nadama, su suke yi wa zuciyar ta dabaibayi, tana ji kamar hannu agogo ya dawo baya ta goge tsanar da ta yi wa Abrar ta kuma nuna mata, dan ma bata cikin hankali ta a lokacin, da da wani ido zata kalleta? gaba daya mamakin tsantsar rashin irin imani da son zuciya irin  na alhaji Shettima suke yi....

ta kai kusan awanin 4 ba ta farfado ba, kana ta fara bude idanunta, hawaye ke bin gefe da gefen fuskarta..., a cikin awanin nan  sallah kadai ke ta da su Daddy daga falon, da zarar sun iddar zasu dawo su zauna domin ganin farkawar ta...

"sannu ya jikin?"  gaba daya suka hada baki wurin fadin haka, yayinda suke yi kanta, jinjina musu kai tayi, still hawaye na cigaba da zuba kan kyakyyawar fuskar ta  da yayi fayau tashi daya, sosai kuma kanta ke mata ciwo tamkar ana buga mata guduma...

gyaran murya daddy yace"hakika Abrar kin ga rayuwa, ta SILAN MIJIN AMMINKI, mun yi matukar tausaya miki, kuma kaddarar ki ce ta zo da haka, domin mutum baya kaucewa kaddarar sa, sai dai ina so ki sani cewa babu wanda ya kai uwa son danta ko yarta a duniya, duk da Amminki ta yi kuskuren rashin sauraren ki, wanda iyaye da dama na aikata hakan, idan yayansu sun kawo musu wata magana mai muhimmanci maimakon su tsaya su yi wa maganar duba na tsanaki, amma sai su yi watsi da maganar...(izinah garemu iyaye) da wanna nake cewa kada ki yi fushi da Amminki, nasan a yanzu tana cikin matsananci damuwa da kuma kewar ganin ki, sannan idan an kwana biyu zamu je can gidan inda Ammin taku take aure kin ji ko? ".... daga kai tayi alamun "toh" yayinda take take kokarin bude baki tayi magana, amma ta kasa, girgiza mata kai Daddy yayi alamun ba sai tayi maganan ba, wayar Amal ce ta fara ringing "sweet Adam" ta gani a rubuce, dagawa tayi ya sanar da ita cewa yana jiran ta a waje domin su tafi gida, a sanyaye ta mike ta yi salama da su Mummy tana waiwayon Abrar ta fito...

"Amma Daddyn'su bai kamata a bar dan iskan mutumin nan haka ba fa, domin irinsu a cikin al'ummah masifa ce" Mummy tace cikin tafarfasan zuciya, domin ji take kamar ta ga alhaji Shettima gabanta tayi ta kwada masa lafiyayyun maruka...

Murmushi irin nasu na manyan Daddy yayi a ransa yana fadin duk shekarun mace, toh ba shakka  namiji ya fita kaifin tunani "relax mana Mummyn'su komai a nutse ya kamata mu bi shi"...

Jinjina kai tayi kawai tayi,  ba dan haka ta so ba, kallonta ta kai ga Aaban da ke ta fama hargitsa sumar sa hadi da cije tattausan labbansa, cikin tausayinsu tace " son, ya kamata ku je daki ku kwanta haka, domin tara saura" ta fada tana duba tsadadden agogan dake makale a jikin bangon dakin...

Bai ce kala ba ya nufi sama cikin sassarfa ba tare da ya ko kalli inda Abrar take ba, da kallon Abrar ta bishi yayinda hawaye masu suka cigaba da gudana a fuskar ta, gani take kamar ya daina sonta ne...

cikin tausayin ta Mummy ta kamo ta hadi da mikar da ita tsaye, kana ta kaita har saman bangaren su kana ta sauko... a hankali ta dora hannunta kan handle din kofar, ta tura ta shiga a hankali, zaune ta gan shi kansa na kasa, dauke idanunta tayi ta nufi toilet, alwala ta dauro kana ta fito ta shimfuda sallaya ta shiga rama salollin da ke kanta....

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now