7

200 8 0
                                    

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓

written by noor Eemaan
wattpad @noorEemaan

page 13-14

bayan ammi ta iddar ta sallan ko hijab bata cire ba ta nufi hanyar kofa " haba hajiyata ko dan tea din dana ajiye miki baza ki shi ba" ya fada yana marairaicewa kamar wani saurayi dan shekara 25 murmushi ammi tayi ta karbi shayin ta shanye tas take taji wani matsananci kasala hadi da jiri sun dirar mata lokaci daya baya baya tayi ta zauna akan gadon, can kuma sai ta kwanta babu jimawa bacci yasake daukar ta murmushi alhaji shettima yayi  ganin yasamu abunda yake so domin yana sane ya zuba tablet din da yawa acikin tea din...

shiryawa alhaji shettima yayi ya fita wurin harkokinsa batare yasake duba halin da abrar take ciki ba, bakinsa awashe kamar mai tallan toothpaste domin wani nishadi na musamman yake ji...

"TWO DAYS LATER"
abrar na kwance kamar mara rai, domin bata motsi sam, amma abun mamaki hawaye ne suke  zubowa  ta gefe da gefen idanunta izuwa kunnenta, bayan kamar 30minutes ta fara kokarin ware idanunta ahankali, saurin sake rufewa tayi domin wani dishi dishi take gani, sake bude su tayi tana bin dakinta da kallo, can kwakwalwarta ta hasko mata abunda har ta koma ga Allah bazata taba mantawa, wani ihu mai karfi tasaki hadi da durawa daga kan gadon wani radaddi ya ziyarci kwakwalwarta daya sake hargitsa tunaninta, kayan dake jere kan dressing mirror ta fara hargitsa su tana cilli dasu duk wani abu mai fashewa da hannunta ya taba sai ta fasa, su gaba daya ta yanke hannunta da kwalba turare kuka take har da majina, kuka take mai taba zuciyan mai sauraro, kuka take da sautinsa ke fitar da asalin abunda ke zuciyarta, dole atausaya mata komai rashin imanin mutum kuwa. Cikin fitar hayyaci take cewa "mena maka?  laifin me na aikata agareka daka nemi ka ruguza rayuwata? shin ni ba diyar matarka bace, ni ba tamkar yar jikinka bace? dan ba  kai ka haifeni ba shiyasa ka cutar dani? da yar cikinkace zaka iya mata haka?" kuka take mai matukar ciwo tana maganganun nan ita kadai. hawayenta ta share amma ina wani na koran wani ta dora da cewa" na tsaneka tsana mafi muni na tsaneka fiyeda yanda na tsaneka a baya sau dubu, ya Allah kasaka min, ya Allah ki mun hakkin na, akan wanna mara imanin bawan naka" ta karasa wasu hawaye masu zafi suka cigaba da zubo mata sai faman buga kanta take a bango amma sam bata jin zafin hakan kamar zafin da zuciyarta hadi kasanta ke mata, ta kai awannnin uku masu kyau tana kuka hadi da maganganu masu matukar tausayi hadi da taba zuciyar, daga kanta tayi ta kalli sama take idanunta suka sauka kan  agogan dakin mai hade da calender, tabass bata manta date din da abun ya faru, sai taga ashe kwananta uku akwance sai ta kuma rushewa da kuka "yanzu kwana uku ban yi sallah innalillahi, ammina ina kike?" tasake rushewa da wani sabon kuka...

toilet ta nufa yayinda take taka kwalaben turaren daya fashe, duk inda ta taka sai ka ga jini amma sam bata damu ba ta cigaba  da tafiya, domin tafi jin zafin abunda ya faru da ita fiyeda yakan  kwalaben dake shigarta ayanzu, wankan sarki tayi hadi dana sabulu tana yi tana kuka sannan ta dauro alwala ta fito, azaune ta fara rama sallolin dake kanta domin tsayuwar ya gagareta....

bayan ta iddar  ta daga hannunta sama "ya Allah ka yafeni, ya Allah ka yafeni, ya Allah na tuba, ya Allah kasaka min abunda mijin ammina yamin ya ubangiji....." sai ta sauke hannayenta ta fashe da wani kuka mai matukar taba zuciya tama rasa addu'ar daza tayi... takai kusan awa daya tana kuka har idanunta wani yaji yaji take jinsa, tana kuma mamakin rashin ganin ammi da bata yi ba, cikin dauriya ta mike domin gaba daya bata da  karfi ko daya ajikinta murda kofa tayi domin zuwa sanar da ammi, bata jin zata boye mata bata da kowa daya huce ammi aduniyar nan tana da kuma tabaccin ammi zata kwatar mata hakkinta gun alhaji shettima, shiyasa tun ganin data masa akaron farko taji tsanar ashe shine zai zama silan lalacewar rayuwarta gaba daya ta tsani gidan da duk wani abu daya dangaci alhaji shettima da wanna tunanin ta fita...

sallah ammi ta gama idarwa akurarren lokaci kamar yanda akwanakin nan take yawan yi, sosai hakan ke bata mamaki, burinta yanzu tasa tilon yarta a ido domin rabonta da ita kwana uku kenan, tana kuma mamaki rashin ganin abrar ko dai jikin ne ta aiyana aranta? ninke sallayan tayi kana ta bude kofar...

✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLETED)✨Where stories live. Discover now