The Ugly Duckling

16.8K 1.1K 40
                                    

A garin dutsen Jihar Jigawa, a unguwar da ake kira da takur-aduwa, anyi wani mutum magidanci mai suna Alhaji Zayyan. Alhaji Zayyan tsohon dan siyasa ne, dan a zamanin daya wuce har mukamin kantoma ya rike, amma kuma a halin yanzu bashi da wani mukami a siyasance, sai dai yana da manyan mutane wadanda suke jan ragamar gwamnatin ta jihar Jigawa. Wannan ya saka har yanzu yake da ɗan abin hannunsa, duk kuwa da cewa a matsayin malamin makarantar secondary ta gwamnati yake. Alhaji Zayyan bafulatani ne, wanda kallo daya zakayi masa kasan cewa tabbas shi 'din pure fulani ne.

Matarsa daya tun ta auren fari, Hajiya Rabi'a, wadda ita kuma bahaushiya ce usul, mutuniyar unguwar mandawari ta jihar kano. Yayin da Alhaji Zayyan ya zamanto mai zafin kai, ita kuma Hajiya Rabi'a sanyi ne da ita sosai. Macece mai tsananin biyayya ga maigidanta. Wannan yana daga cikin dalilin da har yau Alhaji Zayyan ya kasa yiwa matar tasa abokiyar zama, saboda shi kansa yasan ba lallai bane ya samu wacce zata iya hakuri dashi kamar yadda Rabi'a take yi.

Allah ya albarkaci aurensu da samun 'ya'ya guda biyu, Nana Aisha da Nana Khadija. Daga nan kuma shikenan, tun suna saka ran samun wadansu 'ya'yan har suka hakura. Aisha ce babba, shekara biyu ta bawa Khadija. Ranar da aka haifi Aisha, hatta mahaifanta sai da suka yi mamakin kamanninta, dan da ace ba'a gida aka haife ta ba da Alhaji Zayyan zai iya cewa ba 'yarsu bace ba chanji aka yi musu. Daga Alhaji Zayyan har matarsa Rabi'a duk ba baya bane wajan kyau da cikar halitta amma Aisha is far away from kyakykyawa. Bawai hancintane kato ba ko idonta ne kanana ba, a'a, kusan komai a fuskar Aisha babu kyakykyawa. Mutane suka yi ta zuwa barka, kuma Hajiya Rabi'a tana sane cewa rabin mutanen ba barka ce take kawo su ba tsegumi ne. A bangaren iyayen yarinyar kuwa, munin Aisha bai rage ko kadan daga cikin son da mahaifiyarta take yi mata ba, mahaifinta kuma babu yabo babu fallasa, kullum ya kalli yarinyar yana jinjina munin nata a ransa amma kuma ya san tabbas 'yarsa ce, dan haka yake iyakacin bakin kokarinsa gurin sauke mata hakkin daya rataya a kansa a matsayinsa na uba.

Shekara biyu bayan haihuwar Aisha aka haifi Khadija. Duk inda aka san jariri mai kyau to Khadija ta kai nan, dan duk wanda yazo barkanta ya dauke ta sai yaji kamar ya sace ta ya gudu saboda kyau. Ikon Allah.

A hankali yara suka fara girma a tare, kyawun Khadijah sai kara fitowa yake yi, wani irin kwarjini ne da ita da farin jini. Alhaji Zayyan kullum sai ya dauke ta ya fita majalissa da ita, wani lokacin har gurin aiki yake zuwa da ita, mutanen unguwa da abokan aikinsa kowa yasan ta kuma kowa yana sonta, kowa so yake ya ganshi tare da Khadija.

Aisha bata da girman jiki sam, gashi kuma bata da magana sosai, amma duk abinda yake faruwa ta sani, tana sane da cewa ko kayan sawa babansu ya sayo musu sai ya fara zabarwa Khadijah sannan za'a bata sauran. Ba wai yana kinta bane ba amma duk da kankantarta tasan yafi son Khadija a kanta. Bashi kadai ba, Aisha tasan cewa mutanen unguwa da 'yan'uwansu na barin uwa dana uba duk sunfi son Khadija a kanta. Amma lokacin tana yarinya bata san dalili ba.

Da lokacin shiga makarantar Aisha yayi sai Alhaji Zayyan yace "ita wannan da ko maganar kirki bata iya ba mai zata koya a makarantar? Barinta zamuyi kawai ta kara girma kafin nan Khadija ta isa zuwa makaranta sai a hada su tare" Hajiya Rabi'a bata ji dadin wannan hukuncin ba, amma kuma sai tayi tunanin maybe hakan is for the best, tunda Aisha is extremely shy, bata kula kowa dan haka in aka saka ta a makaranta ita kadai zata takura, gwara a bari a hada su da khadijan, maybe zata fi sakewa tayi karatun sosai.

Duk da haka dai sai aka hada su aka saka a islamiyyar unguwarsu. Kullum suna zuwa Aisha zata wuce karshen aji ta zauna ta rungume hannayenta tana kallon malam, yayinda ita kuma Khadijah manyan dalibai zasu yi ta daukanta ana yi mata kwalliya ana gyara mata daurin dankwali, babu wanda yake kulawa da Aisha, ta zama tamkar abinda hausawa suke kira da saniyar ware. Amma har lokacin Aisha bata san dalili ba.

A gida kuma Umma (hajiya Rabi'at) tana iya kacin kokarinta gurin daidaitawa tsakanin 'ya'yan nata dan haka Aisha tafi sakewa da ita akan kowa, itace babbar kawarta kuma ita kadai ce kawarta, in dai ba makaranta ba to kullum suna tare. Tun Aisha tana damuwa in Abba yazo ya fita da Khadijah har ta daina damuwa, tafi son ma su fita din su barta ita da ummanta suyi ta hirar su, dan da ita kadai take yin hira.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now