The Choices

9K 859 49
                                    


Gidan aunty ya sauke ta, da kyar ta lallaba shi ya shiga ta kawo masa drinks ya dan sha kadan sannan suka yi sallama ya tafi. Sai bayan ya tafi sannan ta samu shiga gida ta gaisa da Aunty sosai, ta tarar da ita tana ta faman lissafa atampopi ita da Zahra, ta zauna a gefen gado tace "aunty wannan kayan fa? Business kika fara?" Bata kalleta ba tace "wanne business kuma banda abinki, in business din zanyi sai in siyo set din akwati in zuba kayan a ciki?" Sai a lokacin Aisha ta lura da sabon set din akwati a jere a bango, gabanta ya fadi tayi shiru bata ce komai ba.

Aunty tace "kayan lefenki ne ake hadawa, yanzu so far dai kayan kwalliya suka rage. Dama jira nake yi kizo in zaki tafi dutse ku tafi tare dashi ya gabatar da kansa a gurin abbanki, in yaso daga baya kuma sai su Alhaji suje" Aisha ta sunkuyar da kai, Aunty taci gaba "dama gini ne bai gama ba shi yasa nayi shiru da maganar, tunda yanzu ya gama kuma kinga ai shikenan. Ni maganar karatun ki ce bansan yadda za'ayi da ita ba" Aisha taji hawaye ya fara taruwa a idonta tayi sauri ta mayar dan ko kadan bata son Aunty taga bacin ranta akan maganar nan, Aunty tayi mata komai a duniya, ta nuna mata soyayyar da mahaifiyarta ce kadai ta nuna mata irinta, kuma wannan auren ma da take kokarin hadawa shima duk cikin soyayyar ne, dan haka ita kuma zata yi iya kacin kokarinta ita ma dan ganin ta faranta mata ranta.

Suna nan kuwa sai ga dan halak din ya iso, ya shigo ya gaida Aunty ya dauki atampa daya yana gani yace "kayan sun iso kenan, yanzu saura dogayen riguna ko?" Tace "suma Alhaji zai taho dasu daga kasuwa anjima, yanzu kayan kwalliya ya rage, kuma duk kaine kake wannan delay din minti nawa ne zamaje ka siyo ka kawo?" Ya langwabe kai yace "Umma ba maganar mintina bane ba maganar kudi ne ai, Allah da gaske nake babu kudi a hannuna, kinga albashin wannan watan duk a tailing ya kare, gashi ba'a saka lokokin kitchen ba suma kuma tsada ne da su, kayan kwalliyar nan ki barsu tunda ba yanzu za'a kai kayan nan ba" tace "wanne irin ba yanzu za'a kai ba, bayan gata nan tazo hutu kuma so nake ayi sa rana kafin ta koma" sai a lokacin ya kalli Aisha shima ba tare da ya hada ido da ita ba ya ce "sati nawa ne hutun naku?" ta bude masa hannu alamar itama bata sani ba, yayi karamin tsaki yace "hutun semester ne ai ba zai wuce sati biyu ko uku ba, Umma lokacin yayi kadan wallahi, har su koma ba lallai in kuma yin wani albashin ba fa" ta danyi shiru sai kuma tace "to shikenan, ai ina ganin kafin nan na dauki dashi na sai a karasa siyayyar dashi, amma sai ka biya ni ehe, dan kayan kitchen zan siya mata dashi" ya mike tsaye yana cewa "naji nagode, ai nasan matsayina dama, kinfi son Aisha da kowa a gidan nan" sai daya kai bakin kofa sannan Aisha tace "Barka da yamma" ya juyo yana kallonta yace "bazan amsa ba, sai yanzu kika ganni?" Ya fice.

Zahra ta fara zungurar ta tana cewa "ki tashi kije ki bashi hakuri, kinga yayi fushi baki gaishe shiba, ki tashi kije" Aisha tayi banza da ita. Aunty tana cigaba da aikinta tace "ki je ki kai masa abincin sa, gashi can a kitchen, dan nasan da yunwa ya dawo kuma in dai ba'a kai masa ba ba zai nema ba" Aisha ta mike jiki babu kwari ta tafi kitchen, ita ta kasa gane kan wannan lamarin, ita sam babu feelings whatsoever na Hafeez a gurinta, kuma shima tasan haka, maybe ma haushin ta yake ji yanzu. Ta runtse idonta tace "ya Allah ka kawo min dauki".

Tayi knocking kofar sa taji yayi magana sannan ta tura da sallama ta shiga, yana tsakiyar gado ya baza takardu a gabansa ga calculator a gefe, ta ajiye abincin sannan ta zauna akan bedside drawer ta gaishe shi, bai amsa ba ya dago ya kalleta sai kuma yayi murmushi yace "Mai suke baki a abujan nan ne? Mai da tsohuwa yarinya? To mu dai munsan asalin balbela ballantana ta daga mana kai dan tayi fari" tayi murmushi kawai, yace "ya karatun?" Tace "Alhamdulillah" ya miko mata wasu takardu da calculator yace "tunda Allah ya kawo ki sai ki taya ni lissafi" ya zagayo gabanta ya nuna mata abinda yake so tayi a takardar sannan ya zauna a kasa ya zuba abinci ya fara ci, ta kalli rubutun, duk lissafin laces ne da atampopi da mayafai da takalma, daya takardar kuma lissafin siminti da yashi da tsakuwa da rodi, taga yawan kudin ta girgiza kanta kawai, yace "kinga abinda nake fama dashi ko? Amma wai sai ace aure yakin mata bayan ku babu abinda kukeyi komai yi muku akeyi, mu kuma komai mu zamu yi wa kanmu, yanzu kayan kwalliyar ma ance ba za'a sai min ba" Aisha bata yi magana ba yace "tunda kinzo ma kafin ki koma sai muje kiga gidan, in akwai abinda kike so sai kiyi magana tun yanzu" ta dago tana kokarin karantar fuskarsa, babu excitement kwata kwata a cikinta, ko makaho ya shafa yasan ba son auren nan yake yi ba.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now