Not Again

7.8K 819 24
                                    

Komai ya tafi yadda ya kamata. Aisha tazo kano gurin auntynta ta kwana biyu sannan suka tafi Dutse tare. A dutse da kanta taje ta kaiwa Yakumbo da Maryam IV wanda hakan ba karamin faranta ran yakumbon yayi ba. Ranar thursday din kamu da safe sai ga mutanen Abuja sunzo, Mami da Amira, sai kuma Zainab da wadansu 'yan department dinsu su uku. Aisha ta tare su da murna sosai, tama rasa inda zata ajiye su taji dadi saboda yadda gidan yake karami gashi kuma mutane sun cika, tayi musu korafin rashin tahowa da basuyi da yara ba, Mami tace "rufa mana asiri Aisha, waye yake zuwa biki da yara, in na taho da Abdallah ai sam ba zai barni inyi enjoying bikin nan ba, ni kuma na shirya damarar kwaso shoki son raina" suka yi dariya gaba daya, Amira tace "kina so idan labari yaje kunnen Sultan ya harbo igwa tun daga abuja ta zo ta tarwatsa gidan bikin kenan gaba daya" Mami tace "dama kuwa da kyar aka barni tahowa ba, kin san halinsa, kuma na tabbatar dan yana ganin mutuncin Aisha ne sosai". Aisha ta kuma jin dadi a ranta, dan sam bata saka ran zuwan su har Dutse ba saboda tasan yadda Mami suke manne ita da mijinta basa rabuwa.

Gidan bikin ya cika sosai, musamman saboda wannan shine kadai event din da za'ayi a Dutse dan haka 'yan uwan Abba kowa yayi kokarin ganin ya halarta, duk wanda yazo kuwa in ya kalli Aisha sai kaga ya koma gefe yana kiran sauran 'yanuwansa suma suzo su gane wa idonsu yadda Aisha ta koma, wasu ma in suka shigo basa ganeta sai tayi musu magana ko kuma in an nuna musu ita. Aisha tana lura da yadda kowa yake kallonta inta juya ayi kus kus inta juyo ayi shiru, sai dai kawai tayi murmushi a zuciyarta tana kara godiya da tasbihi ga Allah almusawwiru daya juya rayuwarta gaba daya.

Gwoggo sai faman kaiwa da komowa take yi tana jagorantar mutane suzo suga amarya Aisha, in zata yiwa Aisha magana kuwa har sunkuyowa take yi kusa da ita kamar mai shirin durkusa mata, nan ma Aisha ta tuno irin kyara da hantarar da gwoggon take yi mata a da, babu irin zagi da ba'a da bata gani a gurin gwoggo ba, Khadija ce favorite dinta yanzu kuma ina Khadijan take?

Duk abinda yake faruwa sai Aisha take ganin kamar wani second bikinta ake sakewa, tunda dai an taba kama ta before, kuma ita ba bazawara ba balle tace aure na biyu take yi, wannan sai dai a kira shi da biki biyu. Da yamma duk aka dinguma aka tafi gurin event din, amarya da tawagarta sune na karshen tafiya. Kamar yadda tayi a wancan bikin wannan ma da kanta tayi wa kanta kwalliya kuma ta wannan karon sosai tafi ta wancan kyau saboda changin da ita Aishan ta samu, in ka ganta sai ga dauka professional make up artist ce tayi mata kwalliyar. Ta saka farar atamfa tas mai adon red flowers manya, sai kuma ta dauko katon red mayafi ta yafa har kanta ta lullube rabin fuskarta dashi, a hannunta kuma ta rike red purse mai fararen stones ta saka takalmin jakar, wuyanta, kunnenta da hannunta sunsha adon white pearl wadanda suka kara fito da kyawun jan lallen da aka yi mata a hannu da kafafunta. Hatta mami data kalle ta sai da tayi tasbihi ga ubangiji daga halicci Aisha, dan shi kadai ya san irin yawan baiwar da yayi mata.

Gurin taron ya cika fal da mutane, da wadanda aka gayyata da wadanda suka zo gulma, kowa sai fadar albarkacin bakinsa yakeyi, kowa kuma kokari yake yi yazo ya dauki hoto da amarya Aisha. Ana tsakiya da taro sai ga zugar kawayen su nan na secondary school, wadanda duk kawayen Khadija ne dan Aisha ko kallo bata ishe su ba a wancan lokacin, amma yau sai gashi sunzo bikinta suna ta washe mata baki wai lallai su kawayenta ne, cikin fara'a ta karbe su kuma ta saka aka kirawo mai hoto yayi musu hotuna sosai sannan tace da Zahra ta tabbatar sun samu soveniers. Yakumbo kuma tare suka zo da 'yan uwan Nura da suka zo kamun amarya, Maryam ma tana cikinsu amma daga baya sai ta dawo cikin kawayen Aisha. An kusa tashi kenan sai ga Nafisa babbar kawar Khadija, Aisha ta faki idon mutane ta jata gefe tace "Nafisa ina Khadija?" Da sauri Nafisa ta bude ido tace "Khadija kuma, ni bansan inda Khadija take ba, wai mai yasa har yanzu mutane suka ki yarda dani ne? Police sunyi min tambayar nan, Abba yayi min, Kamal ko last week dana je shagonsa kai dinki sai da ya biyo ni yana tambayata Khadija, ni bansan inda Khadija take ba" Aisha ta tsare ta da ido tace "ki rantse da Allah baki san inda take ba" Nafisa ta kalle ta cikin ido tace "wallahi tallahi billahillazi bansan inda Khadija take ba, Na rantse da Allah rabona da Khadija tunda ta bar garin nan" Aisha taji ta yarda har cikin ranta Nafisa gaskiya take gaya mata, taji babu dadi a ranta, Nafisa tace "to ke menene naki na nemanta ma? Inda akwai wanda zai nesanta kansa da Khadija ma ai ke ce, after all what she did to you?" Aisha tace "tabbas zan iya saka Khadija a layin makiyana, zan iya cewa ma tana daga farko a makiyana amma hakan bai goge cewa jininta ne yake gudana a cikin jijiyoyi na ba, 'yar uwata ce uwa daya uba daya, a yanzu bayan Abba duk duniya bani da kamarta".

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now