Baby

9.3K 799 42
                                    

Here is a long episode for you. Asha karatu lafiya.

Da assuba Humairah ta tashi kamar kullum, tunda ta farka take jinta babu dadi, zuciyarta tayi mata wani irin nauyi kuma tana tunanin yawan kukan da take yi kwana biyu shi ya jawo hakan. Wanka ta fara yi kamar yadda ta saba sannan tayo alwala tazo ta saka doguwar riga da hijab ta tayar da sallah. Tun tana cikin sallar ta ringa jin wani irin sanyi yana shigarta, sanyi mai shiga har cikin 'bargon mutum. Ta idar da sallar ta daga hannu sai taji ta kasa gabatar da addu'ah kamar kullum, ta kasa rokon Allah bukatunta kamar yadda takeyi kullum. Saboda yanzun duk ji take yi bata da wata bukatar da tafi ta ganin mahaifinta, duk duniya yanzu babu abinda take so irin taga babanta. Gani take yi ganin babanta shine tamkar warwarar sauran matsalolinta na rayuwa. Rashin uba ne ya saka ta rasa komai a rayuwa, kuma rashin uba ne zai saka ta rasa Al'ameen a yanzu. Ta shafa addu'ar ta ta jingina kanta jikin gado tare da lumshe idonta, ta bude su a hankali ta sauke su akan hoton da yake kan bedside din Basma. Family picture ne, kuma tsohon hoto ne dan mutanen ciki basu kai yadda suke yanzu shekaru ba. Daddy ne a tsakiya, yayi famous murmushinsa na gefen kumatu, Mami da Basma suna sides dinsa biyu kowacce ta kankame hannunsa. Bassam yana kusa da Basma, ya rage tsaho ya jera fuskarsa a jikin ta Basma. Little Abdallah a tsaye gaban Mami ta dora hannunta a gashin kansa. Sai Al'ameen, yana tsaye a kusa da Mami, hannayensa duk biyun a cikin aljihu, ya dan juyar da kansa gefe tamkar ba dashi za'ayi hoton ba, ya hade girar sama data kasa, dukkaninsu suna murmushi hatta Al'ameen daya bata rai murmushi ne kwance a lips dinsa. This is what is call a Family. Something bounded by blood, wanda babu ta yadda za'ayi a raba shi, komai rintsi komai wuya dole akwai wani dauri a tsakanin family members wanda baya kwancewa. Abinda Humairah bata dashi kenan. Ta kwanta akan sallayar ta lulluba da hijab dinta tana kara jin sanyi yana shigarta, ta fara tunanin yadda rayuwarta zata kasance idan da ace tana da family.

Misali ace tana da Mamanta da Babanta, da two sisters, no, three, sannan da little brother. Kullum zasu ke zuwa school tare, in an yi break su ci abinci tare, sannan in sun tashi babansu yazo ya dauke su kamar yadda take gani ana daukan yara tun tana yarinya. A hanya duk zata bawa babanta labarin duk abinda ya faru a school, da irin fad'an data tarewa kannenta, sai ya shafa fuskarta yace "am so proud of you Baby". In sunje gida zasu tarar da Mamansu, duk suje su rungume ta suna rige rigen kissing dinta, sannan sai maman ta rike hannunta tace "yau abinci specially dan ke na dafa Baby, tuwon shinkafa miyar danyar kubewa saboda nasan kina son shi. Because I love you so much Baby". Ta share hawayen da yake bin fuskarta yana kwanciya a kan pillow, tana wondering menene ainahin abinda ya raba iyayenta? Menene ya saka Mamanta ta zabi barin cikin danginta ta shiga duniya ba tare da tayi tunanin yadda karshen rayuwarsu zai kasance ba?

Ta fara wassafa different scenarios a ranta. Misali; Mamanta 'yar wani hamshakin maikudi ce a, babanta kuma talakane tikis bashi da komai sai teburin da yake siyar da irin su ashana da Maggi. They fall in love amma iyayen Mamanta sai suka ki amincewa da auren, wannan yasa suka gudu suka tafi can wani gari inda babu wanda yasansu suka yi aure suka haifeta, daga baya talauci ya ishe su shine Babanta ya shirya ya tafi Lagos neman kudi, tun daga nan babu wanda ya kuma jin labarinsa, wannan ne yayi forcing Mamanta ta shiga cikin sana'ar da tayi, wannan kuma shi yasa daga baya suka koma Lagos saboda Mamanta tana saka ran haduwa da Babanta a can. Har ta mutu kuma bata ganshi din ba. Sai kawai ta kama share hawayen tausayin Mamanta.

Another scenario, babanta Prince ne kyakykyawa just like Al'ameen. Rannan ya fita a mota sai ya kade wata 'yar talla ya dauke ta ya kaita asibiti yayi mata magani, daga nan ya kaita gida sai yaga marainiya ce bata da kowa sai tsohuwar kakarta, tausayinta ya saka ya aureta ba tare da amincewar iyayensa ba, sai daga baya iyayen suka san labarin auren suka sa aka kori mamanta daga garin akace in dai ta dawo sai an kasheta, duk basu san cewa mamanta tana dauke da cikinta ba. Wannan yasa mamanta ta shiga yawon duniya har ta mutu bata koma gida ba, babanta kuma har yau yana can yana ta nemansu kullum sai yayi kukan rashin samun labarin su. Itama sai ta kama kukan tausayin kanta da tausayin Babanta.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now