Malaysia

7.7K 791 20
                                    

A watannin da suka biyo bayan wannan, su Aisha suka chanza doctor din daya ke dubata, new doctor din ne ya dubata yace matsalar ɓarinta shine bakin mahaifarta ne bashi da kwari. A ka'ida idan mace ta samu ciki bakin mahaifarta yana rufewa ne kuma ba zai bude ba har sai ta fara labour, to amma a case din Aisha sai ya zamanto da zarar cikin nata ya dan yi girma kadan sai yayi wa bakin mahaifar nauyi hakan ne yake saka wa ya bude, ya zarar ya bude kuma dole duk abinda yake cikin mahaifar ya fito waje. Dan haka yayi suggesting da zarar ta samu wani cikin to suyi gaggawar zuwa sai a daure bakin mahaifar yadda ba zata bude ba har sai cikin ya isa haihuwa. Sannan ya basu magunguna da zasuyi boosting fertility dinsu duk su biyun.

A watan kuwa sai ga Aisha da ciki, dan haka direct gurin doctor suka je aka daure mahaifa. Wannan ciki kam yaga gata dan duk son da Nura yake yiwa girkin Aisha cewa yayi ya hakura, gwara yake siyo musu abinci ko shi yake yi musu girkin akan Aisha tayi wahalar girki, ko kasa bata saukowa tana sama kullum dan Nura yace stairs din zasu iya bude mahaifar. Sex ma cewa yayi ya hakura har sai cikin yayi kwari. Allah yasa lokacin sun sami hutu mai dan tsaho dan haka Aisha ta mike kafafuwanta tana mulki a sama, sai dai taci tayi sallah ta kwanta dan wanka ma Nura ne yake yi mata kar ta wahala. Cikin yana wata daya suka je first scan. Aisha tana kwance Nura yana gefenta ya rike hannunta bakunansu kamar gonar auduga suna kallon screen din gaban doctor, doctor ya kallesu shima da fara'a a fuskarsa yace "congratulations, you are having twins" Aisha bata san sanda kuka ya kwace mata ba, kukan dadi take yi Nura kam sai dariya, ji yake yi kamar doctor din ya bar masa machine din ya tafi dashi gida kullum yake kallon yaransa. Tun daga ranar suka fara siyayyar haihuwa, duk abinda suka gani na twins sai sun siya sun ajiye, kayan sawa, kayan wasa, car seats, trolleys kullum in Nura ya fita da abinda zai dawo dashi a hannunsa. A haka har cikin Aisha yayi wata hudu, wannan shine highest da cikinta ya taba kaiwa. Sun koma makaranta amma ba sosai take zuwa ba ita dai.

Ranar nan ta tashi cikin dare zata yi fitsari tana zama akan toilet kawai taji abu mai kauri da dumi yana fitowa, kusan mutuwar zaune Aisha tayi, da sauri ta mike amma taga toilet din jawur da jini. Numfashinta taji kamar zai dauke, ta fara kokarin kiran sunan Nura amma wani azababben ciwon mara ya hana muryar tata fitowa, haka ta kwanta a kasan toilet tana ta murkususu tana hawaye a haka har 'ya'yan duk biyun suka fito, ta dauke su duk ta dora a cinyarta tana wani irin kuka mai cin zuciya, sautin kukan tane ta tashi Nura ya shigo toilet din da sauri, abinda ya gani ya saka shi durkushewa a bakin kofa, ya kasa ma karasowa ballantana yayi wa Aisha magana, sai da yaga tana neman shidewa sannan ya karaso ya jawo ta tare da babies din jikinsa ya rungume su yana dan bubbuga bayanta hawaye yana bin tasa fuskar shima.

A haka suka kasance har assuba ta karasa yi. Nan kuma aka kama rigima dan Aisha kin barin Nura ya dauke 'yan tayin nan ya binne su tayi, rigima sosai tana kuka tana cewa "my babies, my babies" dole ya rabu da ita ya kirawo Mami a waya, itama da tazo sai da lallami da dabara sannan ta fito da Aisha daga toilet din nan aka dauke babies din.

Tun daga ranar rayuwa ta kara yiwa Aisha kunci, dole Nura ya kwashe duk kayan babies din da suka siyo ya saka su a store din gidan ya rufe saboda irin yadda hankalin Aisha yake tashi in ta gan su. A hankali kuma sai ta fara dangana, ta cigaba da karatunta wanda yanzu tana final year sai dai ko maganar haihuwa yanzu bata son ayi mata.

A shekarar da Aisha ta gama makaranta a shekarar Nura ya nemi komawa Malaysia dan gabatar da degree dinsa na uku, dan haka tare ya shirya musu tafiyar shida Aisha inda ita kuma zata gabatar da degree na biyu. Komai ya kammala na tafiya dan har yaje ya gama musu registration ya samar musu gida da komai sannan ya dawo zasu tafi tare. Sunje dutse, kano, yola duk sunyi sallama da kowa, a dutse ne suka samu labarin aikin da a kayiwa Kamal na ciwon koda da yake ta fama dashi har sai da ta kai an cire masa kodar guda daya, da kyar Aisha ta lallaba Nura ya yarda suka je suka duba Kamal. Suka tarar dashi a kwance da Maryam a zaune a gefensa, daga Kamal har Maryam sunyi mamakin chanzawar both Aisha da Nura. Kamal ya tashi zaune da kyar ya mika wa Nura hannu suka gaisa, sai kuma Nura yaji babu dadi a ransa, tsakaninsa da Kamal bai kamata ace wai har sunyi batawar da sai an lallameshi sannan zai zo ya duba shi ba.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now